Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Fernandes ne gwarzon marubuta labarin tamaula na 2026

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga 4 zuwa 8 ga watan Mayun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Chelsea na fatan karwa a mataki na shida watakila ta buga Champions League

    Chelsea tana tazarar maki huɗu kacal daga matsayi na shida a gasar Premier League — wanda zai iya zama gurbin shiga gasar Champions League a baɗi.

    Matsayi na shida zai ba da damar shiga Europa League aƙalla, amma akwai yiwuwar abubuwa biyu su faru da za su sa wannan matsayi ya koma gurbin Champions League.

    Aston Villa na matsayi na biyar, wanda a yanzu haka tana cikin gurbin Champions League, sannan idan ta lashe lashe gasar Europa League. Koda yake ta yi rashin nasara 1-0 a hannun Nottingham Forest a wasan farko na zagayen kusa da ƙarshe (semi-final), amma za ta karɓi baƙuncin wasa na biyu ranar ranar Alhamis - kenan idan ta lashe kofin akwai dama ga Chelsea.

  2. Yadda teburin Premier League yake bayan mako na 35, Premier League

  3. Barkanmu da shiga fagen labarin wasanni

    Jama'a barkanmu da kasancewa a cikin shirin labarin wasanni da za mu ke sanar da ku wainar da ake toyawa daga wannan ranar zuwa Asabar 18 ga watan Afirilu.

    Sunana Mohammed Abdu za ku iya tafka muhawara a BBC Hausa Facebook ko kuma ku bibiyi labaran da muke wallafawa a BBC Hausa WhatsApp.