Canji daga PSG, Bayern Munich 0-1 Paris St-Germain
PSG ta saka Senny Mayulu ya maye gurbin Nuno Mendes.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga 4 zuwa 8 ga watan Mayun 2026.
Mohammed Abdu
PSG ta saka Senny Mayulu ya maye gurbin Nuno Mendes.
Bayern ta saka matashi mai cin kwallaye, Lennart Karl ya maye gurbin mai tsaron baya, Dayot Upamecano.
Wata damar rufewa karawar daga PSG. Dayot Upamecano ya ba da ƙwallo kyauta ga Khvicha Kvaratskhelia, wanda ya kuma aika ta ga Nuno Mendes.
Mendes ya buga kai tsaye daga nesa sosai (mita 35), amma Manuel Neuer bai yi nisa da layinsa ba, kuma ƙwallon ta fita waje ba tare da ta shiga raga ba.
Bradley Barcola ya yi wa Alphonso Davies keta a wajen akwatin bugun fanareti, kuma Bayern ta samu bugun tazara a wuri mai kyau.
Bayern Munich ta tsira da kyar! Khvicha Kvaratskhelia bai bugi ƙwallon da kyau ba duk da yana kusa da raga sosai.
Da ya zura wannan, da kusan an gama wasan gaba ɗaya kenan.
Ko Nicolas Jackson zai ceto Bayern a fatan kai wa zagayen karshe a Champions League? Ya shiga fili ya maye gurbin Jamal Musiala.
Bayern ta saka Alphonso Davies da Kim Min-jae, wadanda suka maye gurbin Josip Stanisic da kuma Jonathan Tah. Canjin masu tsaron baya guda biyu a take.
Masu tsaron bayan PSG sun hana Luis Diaz saka, shima harry Kane kamar baya wasan.
PSG ta saka Bradley Barcola ya maye gurbin wanda ya ci kwallon, Ousmane Dembele.
Wataƙila wannan ya taƙaita yadda Bayern ke taka rawa: An yi wata doguwar sa kai, amma a ƙarshe ƙwallon ta bugi alkalin wasa João Pedro Silva Pinheiro.
A taƙaice: ya kamata su buga kai kai tsaye maimakon yawan wasa da ƙwallo.
Kyakykyawan wasa daga Nuno Mendes na PSG, inda ya fito da ƙwallo daga bayan gida mai kyau, amma daga baya ya rasa ta.
Manuel Neuer ya tare kwallaye da yawa cikin daƙiƙu 35 fiye da duk abin da Matvey Safonov ya yi a duk tsawon wasan nan.
Wannan shi ne karo na biyu da mai tsaron ragar PSG, amma cikin sauri ya tare kwallon — irin wanda kowa zai iya yi.
Josip Stanišić bai buga ƙwallon da karfi ba daga waje da akwatin bugun fanareti, kuma ƙwallon ta rarrafa a hankali zuwa ga mai tsaron raga ba tare da wata barazana ba.
Idan har Bayern Munich tana son kai wa zagayen karshe sai ta kara sa kwazo, bayan da ta kasa fasa bayan PSG, kuma lokaci na ja.
If Bayern are really going to have a go, they'd better get on with it.
Aleksandar Pavlović na Bayern ya buga kwallo daga gefen akwatin bugun fanareti, amma ta fita ta yi fadi, har ta nufi kusan tutar kusurwa.
Harry Kane baya samun dama sosai a karawar yau. Har yanzu ana takura masa cikin akwatin bugun fanareti, inda aka ta tare kwallayen da yake bugawa.
Bayern ta buga kwallo zuwa raga sau 10, amma guda ɗaya kacal ne ya kai ga mai tsaron raga.
Kuma hakan yana nuna cewa ba su samu manyan damar zura ƙwallaye masu kyau ba a wannan wasan.