, Chelsea 0-2 Nottingham Forest
Derry, wanda ke buga wasansa na farko a Premier League, an maye gurbinsa da Liam Delap.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga 4 zuwa 8 ga watan Mayun 2026.
Mohammed Abdu
Derry, wanda ke buga wasansa na farko a Premier League, an maye gurbinsa da Liam Delap.
Zach Abbott ba zai iya ci gaba da fafatawar ba, an kuma canja shi da eco Williams.
Magoya bayan Chelsea sun korafin sun samu fenariti. Wannan karon lallai kamar sun samu bugun daga kai sai mai tsaron raga. Ɗan wasan Nottingham Forest, Dilane Bakwa ne ya yi sakaci inda ya yiwa Malo Gusto keta, har ya jawo faɗuwar ɗan wasan Chelsea.
Amma Anthony Taylor tare da VAR sun yanke shawarar cewa kawai haɗuwa ce ta wasa, ba fenariti ba.
Joao Pedro yana da karancin taɓa ƙwallo a karawar, shi ne mai mafi karaci a fafatawar tsakanin ƴan wasa mai bakwai kacal.
Hakan na nuna maka yadda Chelsea ke cin karo da koma baya na rashin kwazo daga wasu ƴan wasan da ake sa ran za su fitar da ita kunya.
Nottingham Forest tana taka rawa sosai. Tsarinsu yadda suke taka leda a filin wasan yana da kyau, ba ta yawan kuskure tana buga karawar da kwarin gwiwa, kuma tan yin abin da ake bukata, kamar ta shiryawa wasan nan da kyau.
Chelsea kuwa ba ta yin abin da zai kai ta farke ƙwallayen da aka zura mata. Duk lokacin da take kokrin kai kora, sai kaga Forest na cikin shiri sosai. Har yanzu ba abin da za ka ce ya firgita Forest daga Chelsea.
Nottingham Forest na kara nuna tsantsar azama fiye da abokiyar hamayya mai masaukin baki, Chelsea. Duk lokacin da ta samu ƙwallo, tana kai hari kai tsaye kuma masu zafi.
A wannan karon, Igor Jesus ya buga ƙwallo daga cros ɗin da aka yi mosa, amma kai tsaye ta je wajen hanun mai tsaron ragan, Chelsea, Robert Sánchez.
Jesse Derry ya fadi a wajen da'ira ta 18 da ake zargin fenariti, bayan wani lamari da ya faru ba tare da ƙwallo ba da Ryan Yates.
Da alama Yates ya bugi ɗan wasan da hannunsa ba da gangan ba a fuska.
An duba ta hanyar VAR, kuma daga baya aka warware lamarin ba wani abinda ya faru.
Nottingham Forest kan yi nasara a dukkan wasanninta 25 a bayan nan a gasar Premier League duk lokacin da ta fara cin ƙwallaye biyu ko fiye da haka, tun bayan wasan da ta yi 2–2 da Luton Town a watan Oktoba 2023 a gasar ta Premier League.
Haka kuma, akwai tsohon ɗan wasan Chelsea, Thiago Silva, wanda kwanan nan aka naɗa shi gwarzon liga tare da ƙungiyar Portugal, FC Porto.
Haka nan Khabib Nurmagomedov, tsohon ɗan wasan MMA, ya bar gefen filin wasa kafin a fara wasan ya koma cikin kujerun kallo.”
Gaskiya babu wani motsi sosai mai amfani daga Chelsea idan tana da ƙwallo. Kowa dai yana tsaye yana kallo, babu gudu ko motsi ba tare da ƙwallo ba.
Ya zuwa yanzu, al’amura sun yi sauƙi sosai ga Nottingham Forest ba ta fuskantar wata babbar barazana.”
Anga kociyan Tottenham, Roberto De Zerbi cikin an kallo a Stamford Bridge.
Tottenham za ta fafata da Chelsea a mako biyu masu zuwa a Premier League.
Wannan bugun fenariti Igor Jesus ne ya buga , yayin da Robert Sánchez ya yi tsalle zuwa gefen damansa, kuma hakan ya bai wa Nottingham Forest zura na biyu a raga, yanzu ana cin Chelsea 2-0.”
“Bayan da ya ɗan kalli allo cikin sauri, Anthony Taylor ya bayar da bugun fanareti. Malo Gusto kuma ya samu katin gargadi (rawaya) saboda jan riga.”
“Dukkan hayaniyar da ake ta yi a Stamford Bridge tana fitowa ne daga magoya bayan Nottingham Forest. Chelsea FC na ƙoƙarin kai hari ta hannun Enzo Fernández, amma har yanzu ba su samu gagarumar dama ba.
“Wannan ƙwallon ta zo ne bayan daƙiƙa 97 kacal. Ita ce mafi saurin da wata ƙungiyar daga waje ta ci Chelsea a gasar Premier League tun daga watan Disamba 2013 — lokacin da Jay Rodriguez ya ci wa Southampton FC bayan daƙiƙa 13.”
“Kwallon da David Okereke Bakwa ya buga cikin gidan Chelsea ta yi kyau matuƙa, kuma dama ce mai sauƙi ga Taiwo Awoniyi ya zura ƙwallo a raga da kai, Robert Sánchez ba shi da wata dama. Gaskiya dai ta zo ne ba zato ba tsammani.”
Wace irin dama ce haka! A wasansa na 100 da ya fara bugawa Nottingham Forest, Taiwo Awoniyi ya ci wa ƙungiyarsa ƙwallon farko.
Dilane Bakwa ya samu ɗan sarari a gefen dama, ya aika da ƙwallon mai kyau, inda Awoniyi — wanda babu mai makinsa shi kaɗai ya zura ƙwallon a raga.