, Everton 0-0 Manchester City
Matheus Nunes ya kasa tare ƙwallo, amma Iliman Ndiaye ya samu bayan da ya ruga a guje.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga 4 zuwa 8 ga watan Mayun 2026.
Mohammed Abdu
Matheus Nunes ya kasa tare ƙwallo, amma Iliman Ndiaye ya samu bayan da ya ruga a guje.
Tuni ta ɗauki Carabao Cup
Ta kai zagayen karshe a FA Cup
Tana sa ran lashe Premier League
Erling Haaland ya ci kwallaye 24 a Premier League, kuma Jérémy Doku ne ya taimaka masa da huɗu daga ciki.
Wannan makon ya kasance mai cike da abinda ba za a manta ba a Manchester City.
Kwanan nan kyaftin Bernardo Silva ya sanar da cewa zai bar Etihad a karshen kakar nan, hak kuma mai tsaron baya, John Stones ya biyo baya da cewa shi ma zai tafi a ƙarshen kakar.
Wannan na iya shafar yanayin ƙungiyar — musamman ganin cewa duka biyun manyan ƴan wasa ne masu tasiri a tsarin Pep Guardiola.
Wannan shi ne karo na 16 da David Moyes zai kara da Pep Guardiola a Premier League, amma har yanzu bai taba cin nasara ba (canjaras biyu aka doke shi 13). Wannan yana daga cikin mafi munin tarihin koci a kan wani koci.
A ƴan shekarun baya, Everton tana yawan kasancewa kusa da faduwa daga Premier League fiye da fafutukar zuwa gasar zakarun turai.
Yanzu haka tana matsayi na 11 da maki 47, kuma har yanzu tana da damar shiga gasar Turai — ko da yake samun gurbin Champions League yana da wahala a wajenta.
Europa League ko Europa Conference League na iya zama abin da za iya samun tikiti da zarar ta sa kwazo a sauran wasannin da suka rage mata.
Abin da koci David Moyes ya ce:
“’Ƴan wasan ba su saba da wannan yanayi ba. Amma ya fi kyau fiye da kokarin kauce wa faduwa. Muna fatan mu ci gaba da inganta wasannin mu kuma mu kalubalanci manyan ƙungiyoyi.”
Wannan yana nuna yadda Everton take inganta fafatawar da take yi a wannan kakar — daga fafutukar tsira zuwa mafarkin gasar zakarun Turai.
Manchester City ba ta yi rashin nasara ba a wasa 11 a gasar (Ta ci takwas da canjaras uku), kuma su ne suka fi tara maki (24) kuma suka fi rage kwallaye (takwas) a wannan lokaci.
Karon farko da Manchester City za ta buga wasa a sabon filin Everton, Hilldickinson Park.
Everton ta yi rashin nasara a wasanni biyu na baya bayan nan; ba ta taɓa yin rashin nasara uku a jere ba tun Janairu na kakar da ta gabata.
Wannan shi ne karo na uku da Manchester City da Arsenal ke fafatawa kai tsaye kan kalubalantar kofin Premier League.
A lokutan biyu baya, Arsenal ta kusa lashe gasar daga baya ta kasa ɗaukar kofin da Pep Guardiola da City suka ci nasara.
Haka kuma, Arsenal ta rasa kambun bara (2023–24) ga Liverpool da tazarar maki 10.
Sakamakon baya:
2022–23: Arsenal ta sha kashi da tazarar maki 5 a hannun Manchester City.
2023–24: Arsenal ta yi rashin kofin da tazarar maki 2 a hannun Manchester City.
2025–26: ???
Tambayar da ke tafe yanzu ita ce: wannan karon wa zai yi nasara a fafatawar karshe?
Manchester City ba ta yi rashin nasara ba a wasa 17 a Premier League da Everton (Ta ci 14 da canjaras uku), tun bayan shan kashi 4–0 a 2017.
A halin yanzu Manchester City tana biye da Arsenal da tazarar maki shida, amma City ta yi wasa kasa da yawan na Arsenal.
Idan City ta ci wasan daren nan, za ta rage tazarar zuwa maki uku, tare da wasan da suke da shi a kwantai.
Everton tana matsayi na 11. Idan ta ci, za ta haura zuwa na tara; idan ta tashi canjaras, za ta koma ta 10.
Samun tikitin zuwa gasar Turai har yanzu yana yiwuwa ga Everton, amma zai zama babban ƙalubale gare ta a wannan matakin na kakar.
Everton za ta karɓi bakuncin Manchester City a gasar Premier League da za su kara ranar Ltinin.
A wasan farko da suka buga a bana a cikin watan Oktoba, City ce ta yi nasara 2-0
Everton ta sha kashi a wasannin gida takwas a jere a gasar Premier League da Manchester City — wannan shi ne mafi tsawo a tarihinta da wata ƙungiya guda.
Cole Palmer ya bugo ƙwallo, amma Levi Colwill ya kasa samu .
Ƙwallon ya yi waje.