Abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Asabar 05 zuwa Juma'a 11 ga watan Yulin 2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu da Abdulrazzaq Kumo

  1. Arsenal ta sake ɗaukar ɗan wasan tsakiya

    Christian Norgaard

    Asalin hoton, Getty Images

    Arsenal za ta biya fam miliyan 10 kai tsaye sannan sai samu ƙarin fam miliyan biyar idan ɗan wasan ya taka rawar gani.

    Norgaard mai shekara 31 ya sanya hannu ne kan yarjejeniyar shekara biyu a Emirates.

    A shekarar 2019 ne ɗan wasan ya koma Brentford daga Fiorentina, inda ya zama gwarzo a ƙungiyar har ya zama kyaftin a ƙungiyar, ya kum buga mata wasanni 196.

    Norgaard ya bayyana farin cikinsa na komawa Arsenal inda ya ce " Yanzu zan riƙa jin sautin gasar Champions League kuma zan buga gasar.

    Abu ne da nake buri tun ina yaro kuma ban taɓa tunanin zai faru ba. Don haka ina farin ciki".

    Norgaard ne ɗan wasa na uku da Arsenal ta saya a bana bayan Martin Zubimendi da Kepa Arrizabalaga, kuma har yanzu tana cinikin Noni Madueke da Viktor Gyokeres.

  2. Rodrygo Goes

    Asalin hoton, Getty Images

    Liverpool za ta iya bin sahun Arsenal wajen fafutukar ɗaukar ɗan wasan gaban Real Madrid da Brazil Rodrygo, mai shekara 24, idan har ta rasa ɗan wasan Colombia Luis Diaz, mai shekara 28, wanda ake alaƙantawa da komawa Barcelona. (Sacha Tavoleri).

    Napoli ta sake karkata akalarta kan ɗan wasan Manchester United da Argentina Alejandro Garnacho, mai shekara 21, kuma ta na fatan za ta iya samun ɗan wasan kan farashin fam miliyan 45. (Mirror)

    Manchester United na tunanin sayar da ɗan wasan Ingila Jadon Sancho, mai shekara 25, kan farashi mai rahusa. (Givemesport)

    United na ci gaba da sa ran cewa za ta iya kammala cinikin ɗan wasan Brentford da Kamaru Bryan Mbeumo, mai shekara 25, ta na kuma fatan ɗan wasan zai kasance a cikin tawagarta kafin ta fara rangadin wasannin share fage a Amurka. (Sky Sports)

    Tattaunawar da Arsenal ke yi kan ɗan wasan gaba na Sporting da Sweden Viktor Gyokeres, mai shekara 27, ya tsaya cak sakamakon rashin cimma matsaya kan farashi da kuma sharuɗɗan yarjejeniyar cinikin ɗan wasan. (Independent).

  3. Arsenal ta tuntuɓi Chelsea kan Madueke

    Madueke

    Asalin hoton, Getty Images

    Arsenal ta tuntuɓi Chelsea kan ko za ta sayar mata da Noni Madueke.

    Tun a makon jiya BBC ta sanar da cewar Arsenal ta cimma yarjejeniya da Madueke, amma ba a samu tunruɓa tsakanin ƙungiyoyin biyu.

    Chelsea na bukatar £50m domin sayar da ɗan wasan mai shekara 23 ɗan wasan tawagar Ingila.

    Ya buga wa Chelsea karawa 92 da cin ƙwallo 20 tun bayan da ya koma Stamford Bridge da taka leda daga PSV Eindhoven a Janairun 2023.

    Arsenal na shirin kara karfin gurbin masu cin ƙwallaye, wadda ke fatan daukar ɗan wasan Real Madrid, Rodrygo da Eberechi Eze na Crystal Palace.

    Haka kuma Gunners tana zawarcin Viktor Gyokeres daga Sporting, bayan da ta kammala sayen Zubimendi da Kefa Arizabalaga.

  4. Tottenham ta amince da farashin £55m ga Kudus daga West Ham

    Kudus

    Asalin hoton, Getty Images

    Tottenham ta amince da farashin £55m domin sayen ɗan wasan West Ham, Mohammed Kudus.

    Ɗan wasan tawagar Ghana zai je a auna koshin lafiyarsa, daga nan ya rattaba hannu kan ƙwantiragi.

    Ranar Asabar BBC ce ta bayar da rahoton cewar West Ham ta yi watsi da tayin £50m, amma yanzu ta kai ga cimma matsaya.

    Kudus, wanda yake da yarjejeniyar £85m ga duk wadda za ta saye shi ba tare da kwantiraginsa ya kare ba, ya koma West Ham daga Ajax a 2023.

    Ya buga wasa 65 a Premier League da cin ƙwallo 13 da bayar da tara aka zura a raga.

    A ƙalla ƙungiya shida ke fatan ɗaukar Kudus, sai dai yanzu ya zaɓi Tottenham, saboda za ta buga Champions League a kakar da za mu shiga.

    Haka kuma Tottenham na shirin zawarcin ɗan wasan Brentford, Yoane Wissa.

  5. Everton ta kammala sayen Barry daga Villareal

    Barry

    Asalin hoton, Getty Images

    Everton ta sanar da kammala sayen Thierno Barry kan yarjejeniyar kaka huɗu.

    Kamar yadda aka sanar ƙungiyar da ke Mersyside ta sayi ɗan wasan kan £27million.

    Barry ya ci ƙwallo 11 a wasa 35 a La Liga a kakar da ta wuce, ya taka rawar gani da Villareal ta kare a mataki na biyar a teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya, za ta buga Champions League a kaka mai zuwa.

    Ya fara taka leda a Toulon ta Faransa daga nan ya koma Beveren ta Belgium.

    Barry koma Basel a 2023 da cin ƙwallo 10 a wasa 36 daga nan ya koma Villareal a 2024.

  6. Musiala ya ce baya zargin kowa saboda karayar da ya yi

    Musiala

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɗan wasan Bayern Munich, Jamal Musiala ya ce baya zargin kowa kan karyewar da ya yi a Club World Cup a wasan da Paris St Germain ta kai zagayen daf da karshe a Amurka.

    Mai shekara 22, ya ci karo da cikas lokacin da mai tsaron ragar PSG, Gianluigi Donnarumma ya je kama ƙwallo tun kan hutu.

    Daga nan aka ɗauki ɗan wasan tawagar Jamus a kan gadon daukar marasa lafiya daga Atlanta zuwa birnin Munich inda aka yi masa tiyata, ba za a fara wasannin kakar bana da da za a buɗe labule a watan Agusta.

    Musiala ya kammala kakar da ta wuce da cin ƙwallo 21 da bayar da takwas aka zura a raga a Bayern Munich, wadda ta lashe Bundesliga a kakar da ta wuce.

  7. Man City

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayern Munich ta tattauna da wakilan Christopher Nkunku yayin da ta ke nazarin ɗaukar ɗan wasan gaban Chelsea da Faransa mai shekara 27. (Bild).

    Napoli ta miƙa tayin fam miliyan 42 kan ɗan wasan gaban Liverpool Darwin Nunez, mai shekara 26. (Gianluca di Marzo)

    Sunderland na dab da kammala cinikin ɗan wasan gaban Morocco Chemsdine Talbi mai shekara 20 daga Club Brugge na Belgium. (Fabrizio Romano)

    Atalanta ta yi watsi da tayin fam miliyan 45.7 da ƙungiyar Al-Qadsiah ta Saudiyya ta yi kan ɗan wasan gaba na Italiya Mateo Retegui, a yayinda ƙungiyar ta Serie A ta buƙaci fam miliyan 51.8 kan ɗan wasan mai shekara 26. (Football Italia)

  8. Jordan Henderson ya bar Ajax bayan wata 18 a ƙungiyar

    Hendersen

    Asalin hoton, Getty Images

    Dan wasan tawagar Ingila, Jordan Henderson ya bar Ajax, bayan wata 18 a ƙungiyar.

    Mai shekara 35 ya koma Netherlands da taka leda daga Al-Ettifaq ta Saudiyya a Janairun 2024, ya taka rawar gani a kakar da ta wuce da Ajax ta zama ta biyu a teburi da samun gurbin shiga Champions League a kaka mai zuwa.

    Henderson wanda ya yi ƙyaftin din Ajax, yana da sauran kwantiragin kaka ɗaya, sai dai Ajax ba ta sanar da tafiyar Henderson ba, wanda ya buga mata wasa 57 da cin ƙwallo ɗaya.

    An yi mamaki da Thomas Tuchel ya gayyaci Henderson a cikin tawagar Ingila a watan Maris, bayan da bai buga wa kasar Euro 2024 ba, kawo yanzu ya buga wa kasar wasa 84 da yin karawa uku a neman shiga gasar kofin duniya da Albania da Latvia da kuma Andorra.

  9. An yanke hukuncin ɗaurin shekara ɗaya ga Ancelotti kan zambar haraji a Sifaniya

    Ancelotti

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata kotu a Sifaniya ta yanke hukuncin zaman gidan yari shekara ɗaya ga kociyan tawagar Brazil, Carlo Ancelotti, saboda gaza biyan haraji kan kudaden shiga na hakkin hotonsa a cikin 2014 a lokacin da yake horar da Real Madrid, in ji wani rahoton da aka fitar ranar Laraba.

    Ancelotti, wanda ya horar da Real Madrid daga 2013 zuwa 2015 da kuma tsakanin 2021 zuwa 2025, an taɓa wanke shi a irin wannan zargin a 2015.

    Ya koma Landan a Mayun 2015, bayan da Real Madrid ta kore shi.

    To sai dai a karkashin dokar Sifaniya duk wani hukunci da ke kasa da shekaru biyu idan bai shafi tashin hankali ba, yana da wuya a bukaci wanda ake tuhuma ba tare da an taɓa yanke masa hukunci a baya ba ya yi zaman gidan yari.

    Mai shekara 66, tsohon wanda ya horar da Bayern Munich da Chelsea, shi ne na kusa-kusan nan da hukumar Sifaniya suka bincika da yanke hukunci kan zambar biyan haraji.

  10. Semenyo

    Asalin hoton, Getty Images

    Arsenal na shirin bayar da wani ɗan wasa a cinikin da ta ke yi kan ɗan wasan Crystal Palace Eberechi Eze, mai shekara 27, kuma da alama za ta iya doke Tottenham Hotspur wurin ɗaukar ɗan wasan na Ingila. (Sun)

    Akwai yiyuwar Brentford za ta buƙaci a biya fam miliyan 65 kan ɗan wasanta Bryan Mbeumo, mai shekara 25, bayan ta yi watsi da tayin fam miliyan 55 da kuma fam miliyan 62.5 daga Manchester United kan ɗan wasan na Kamaru. (Mirror)

    Ɗan wasan gaba na Sporting da Sweden Viktor Gyokeres, mai shekara 27, ya shirya jira har zuwa ƙarshen bazara don cimma yarjejeniyar aro zuwa wata ƙungiya ta Turai idan har bai cimma burinsa na komawa Arsenal ba. (Sun)

    Ɗan wasan Ingila Jadon Sancho, mai shekara 25, ya shirya rage albashinsa domin ya koma Juventus daga Manchester United, amma har yanzu kulob ɗin na Seria A bai shirya cika sharuɗɗan da za su tabbatar da ƙulla yarjejeniya ba. (Il Corriere dello Sport)

  11. Ƙudin da ƙungiyoyi suke ƙarɓa a Club World Cup

    Club world Cup

    Asalin hoton, Getty Images

    Tsabar ƙudin da ake bai wa ƙungiyoyin da ke buga Club World Cup, shi ne ke jan hankalin masu bibiyar tamaula a faɗin duniya.

    Fifa ta sanar tun kan fara wasannin cewar za ta raba £775m tsakanin kungiya 32, inda duk wadda ta lashe kofin za ta samu £97m.

    Yadda Fifa za ta raba ƙuɗi a Club World Cup

    • Wasan cikin rukuni - £1.5m idan aka ci wasa/£800k idan aka yi canjaras
    • Zagayen ƴan 16 - £5.8m
    • Kwata fainall - £10.1m
    • Daf da karshe - £16.2m
    • Wasan karshe - £23.2m
    • Wadda za ta lashe kofin - £30m
  12. Tottenham ta ɗauki mai tsaron baya Kota Takai

    Kota Takai

    Asalin hoton, Getty Images

    Tottenham ta kammala daukar mai tsaron bayan tawagar Japan, Kota Takai kan yarjejeniyar kaka biyar daga Kawasaki Frontale, kamar yadda kungiyar ta sanar ranar Talata.

    Ba a fayyace kudin cinikin mai shekara 20 ba, amma wasu rahotannin na cewar kungiyar da ta lashe Europa League ta biya sama da fam miliyan shida, kwatankwacin sama da naira biliyan biliyan 12.

    Takai shi ne mai tsaron baya na uku da kungiyar Arewacin Landan ta dauka kawo yanzu, bayan Luka Vuskovic da Kevin Danso, wanda ta saya bayan wasannin aro da ya yi mata daga RC Lens.

  13. Gittens

    Asalin hoton, Getty Images

    Manchester United na shirin karɓar fam miliyan 8 a matsayin wani ɓangare yarjejeniyar da ta ƙulla a lokacin da ta sayar wa Forest da Elanga a 2023. (Talksport).

    Har ila yau, Forest na nazari kan abokin wasan Bakayoko na Belgium Malick Fofana, mai shekara 20, yayin da ake alaƙanta ɗan wasan na Lyon da komawa Chelsea ko Bayern Munich a wannan bazarar. (Sky Sports)

    Unai Emery yana sha'awar ɗaukar ɗan wasan gaban Barcelona Ferran Torres, mai shekara 25, zuwa Aston Villa kuma a shirye ya ke ya biya fam miliyan 43 kan ɗan wasan na Sifaniya. (Fichajes)

    Yunƙurin Arsenal na ɗaukar ɗan wasan bayan Valencia Cristian Mosquera, mai shekara 21, ya ci tura yayin da kulob ɗin na La Liga ke neman sama da fam miliyan 20 kan ɗan wasan na Sifaniya. (Mirror)

  14. Leeds United ta sayi Gudmundson daga Lille

    Gud

    Asalin hoton, Getty Images

    Sabuwar kungiyar Leeds United, wadda za ta buga Premier League a kakar da za a fara a cikin watan gobe, ta dauki mai tsaron baya, Gabriel Gudmundsson daga Lille.

    Dan wasan tawagar Sweden, mai shekara 26, ya rattaba hannu kan kwantiragin kaka hudu kan fam miliyan 10.

    Gudmundsson ya buga wasa 45 a Lille a kakar da ta wuce, kungiyar da ta kare a mataki na biyar a teburin babbar gasar Faransa, wadda ba za ta buga Champions League a kaka mai zuwa ba.

    Haka kuma Lille ita ce ta biyu da kwallaye da yawa ba su shiga ragarta ba, mai 36, biye da Paris St Germain mai 35.

  15. Gossip

    Asalin hoton, Getty Images

    Manchester United na zawarcin ɗan wasan tsakiya na Najeriya Wilfred Ndidi, mai shekara 28, wanda rahotanni ke cewa ya na ɗauke da farashin fam miliyan 9 a kwantiraginsa da Leicester City, yayin da Fulham da Everton da kuma Crystal Palace su ka nuna sha'awarsu kan ɗan wasan . (Tuttosport)

    Tottenham da Newcastle da Napoli duk suna bibiyar ɗan wasan tsakiya na Ingila Jack Grealish bayan da Manchester City ta sanya farashin fam miliyan 40 kan ɗan wasan mai shekara 29. (Sun)

    Newcastle United na ci gaba da fatan cimma nasara a zawarcin da ta ke yi wa Marc Guehi, mai shekara 24, inda ƙungiyar ke neman ƙarfafa tawagar ƴan wasanta da ɗan wasan bayan na Ingila da Crystal Palace. (GiveMeSport)

    Crystal Palace na tattaunawa da Sporting kan tayin fam miliyan 45 da za ta gabatar kan ɗan wasan bayan Ivory Coast Ousmane Diomande, mai shekara 21. (Guardian)

  16. Gabriel Heinze ya koma mataimakin Arteta a Arsenal

    Heinz

    Asalin hoton, Getty Images

    Kungiyar Arsenal ta nada tsohon dan wasan tawagar Argentina, Gabriel Heinze a matakin mataimakin Mikel Arteta.

    Heinze mai shekara 47 ya taka leda tare da Arteta a Paris St Germain daga nan ya koma Manchester United, wanda ya lashe Premier League a 2007, ya buga kaka biyu a Real Madrid.

    Bayan da ya yi ritaya a 2014, Heinze ya horar da tamaula a cikin Argentina daga nan ya yi kocin Atlanta mai buga babbar gasar tamaula ta Amurka.

    Heinze ya koma Gunners, bayan da tsohon mataimakin Arteta, Carlos Cuesta ya bar Emirates, domin karbar aikin jan ragamar Parma.

    Tuni Arsenal ta dauki Martin Zubimendi da Kepa Arrizabalaga

  17. Madueke ya amince da ƙunshin kwantiragin da Arsenal ta gabatar masa

    Madueke

    Asalin hoton, Getty Images

    Tun a farkon makon nan BBC ta sanar cewar Arsenal ta cimma yarjejeniya tsakaninta da ɗan wasan Chelsea, Noni Madueke.

    Mai shekara 23 yana fatan komawa Gunners da taka leda, sai dai ba a tuntuɓi juna ba tsakanin Arsenal da Chelsea.

    Ɗan wasan tawagar Ingila, ya koma Stamford Bridge daga PSV Eindhoven a 2023, ya ci ƙwallo bakwai da bayar da huɗu aka zura a raga a wasa 32 a Premier League kaka da ta wauce.

  18. Gossip

    Asalin hoton, Getty Images

    Newcastle ta fara tattaunawa da Dominic Calvert-Lewin, mai shekara 28, bayan koci Eddie Howe ya bayyana cewa ya daɗe yana sha'awar ɗan wasan na Ingila wanda ya bar Everton bayan kwantiraginsa ya ƙare a watan da ya gabata. (Talksport)

    Sunderland da Leeds United da kuma Wolves suna zawarcin ɗan wasan Lens da Morocco Neil El Aynaoui na kasa da shekaru 23, amma suna fuskantar hamayya daga AS Roma da Juventus da AC Milan kan ɗan wasan mai shekara 24 (Footmercato).

    Kocin Slavia Prague Jindrich Tripisovsky ya tabbatar da cewa El Hadji Malick Diouf na shirin barin ƙungiyar a daidai lokacin da West Ham da Leeds ke zawarcin ɗan wasan bayan na Senegal mai shekara 20. (Standard)

    Ɗan wasan bayan West Ham da Morocco Nayef Aguerd, mai shekara 29, ya kasance kan gaba a jerin ƴan wasan da ƙungiyar Marseille ta Faransa ke zawarci a bana. (L'Equipe)

  19. Everton ta kusan kammala daukar Barry daga Villareal

    Barry

    Asalin hoton, Getty Images

    Everton ta kusan kammala daukar dan wasan Villareal, Thierno Barry kan £27million.

    Ana ci gaba da tattaunawa, sannan ana sa ran Barry zai je ƙungiyar Merseyside, domin a auna koshin lafiyarsu.

    Dan wasan mai shekara 22 yana da kunshin yarjejeniyar £34.5m a Villareal, sai dai Everton na sa ran sayen dan kwallon kasa da hakan.

    Barry ya ci kwallo 11 a wasa 35 a La Liga a gasar da ta wuce, inda Villareal ta samu tikitin shiga Champions League a kakar da zamu shiga, bayan da ta kare a mataki na biyar a teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya.

    Ya fara tamaula a matakin matashi a Toulon daga nan ya koma Sochaux, ya fara nuna kansa a Beveren ta Belgium daga nan ya koma Basel ta Switzerland a 2023.

    Barry ya ci kwallo 10 a wasa 36 a Basel daga nan Villareal ta dauke shi a 2024.

    Kociyan Everton, David Moyes na fatan kara karfin gurbin masu cin kwallaye, bayan da Dominic Calvert-Lewin ya bar kungiyar, sannan Armando Broja ya koma Chelsea, bayan kammala wasannin aro.

  20. Kudus

    Asalin hoton, Getty Images

    West Ham ta ƙi amincewa da tayin £50m da Tottenham ta yi wa Mohammed Kudus.

    Ɗan wasan tawagar Ghana na fatan samun ƙungiyar da za ta buga gasar zakarun Turai.

    Tottenham za ta buga Champions League a kaka mai zuwa, bayan da ta lashe Europa League a kakar da ta wuce.

    .