Abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Asabar 05 zuwa Juma'a 11 ga watan Yulin 2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu da Abdulrazzaq Kumo

  1. Chelsea ta kafa tarihi a Ingila

    'Yan Chelsea na murna da kambin da suka ci na duniya

    Asalin hoton, Getty Images

    Chelsea ta zama ƙungiya ta biyar kuma ta farko a Ingila da ta ci kofuna fiye da ɗaya na hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya , bayan da ta doke Zakarun Turai a gasar World Club Cup na Fifa da ci 3-0 a New Jersy, Amurka ranar Lahadi.

    Real Madrid ita ce ta farko a wannan bajinta da kofi shida, sai Barcelona mai uku, sai Bayern Munich mai kofi biyu kamar yadda ita ma ƙungiyar Corinthians take da biyu.

    Cole Palmer na Ingila ne ya jagoranci caccakar da Chelsean ta yi wa PSG da ƙwallo biyu sai kuma ya sa sabon cefane Joao Pedro ɗan Brazil a hanya shi ma ya zura ta uku.

    da wannan nasara yanzu wasu magoya bayan Chelsea na ganin sai an yi da gaske a kansu a gasar Premier ta kaka mai kamawa.

  2. An girmama Jota da Silva a wasan sada zumunta na Liverpool

    Magoya bayan Liverpool

    Asalin hoton, Getty Images

    An girmama Diogo Jota da ƙaninsa Andre Silva a wasan farko na sada zumunta na Liverpool tun bayan rasuwar 'yanwasan biyu.

    Tun kafin a take leda a wasan na shirin tunkarar kaka mai kamawa a Preston North End, an riƙa rera waƙar Elvis Presley ta 'Can't Help Falling in Love' wadda waƙa ce mai ratsa zuciya, da kuma waƙar taken Liverpool ta - You'll Never Walk Alone'.

    Ɓanagren magoya bayan Liverpool ya cika da tutoci da kyallaye na tunawa da tsohon ɗanwasan na Porto da Wolves, inda suka riƙa rera waƙar Jota, yayin da su kuma 'yanwasan suka yi shiru na minti ɗaya domin tunawa da shi.

    Liverpool ta yi nasara a wasan da ci 3-1, inda Conor Bradley ya fara ɗaga raga, sai Darwin Nunez ya ci ta biyu tare yin irin murnar da Jota ke yi idan ya ci ƙwallo har sau biyu, sai kuma Cody Gakpo, ya zura ta uku, tare da murna da yin alamu na lamba 20 - wato lambar Jota a ƙungiyar

  3. Cristhian Mosquera ya cimma matsaya da Arsenal

    Cristhian Mosquera

    Asalin hoton, Getty Images

    Babban ɗanbayan Valencia Cristhian Mosquera ya cimma yarjejeniya da Arsenal, a ƙoƙarin da ƙungiyar ke yi na sayenshi.

    Tun a baya daman BBC ta ruwaito cewa Arsenal na tattaunawa da ɗanwasan mai shekara 21 - yanzu kuma sun yi nasarar ƙara cimma wata matsaya tsakaninsu.

    Gunners na ƙoƙarin ganin sun ƙara wani matashin ɗanbaya a tawagar domin gogayya da William Saliba da Gabriel Magalhaes.

    Mosquera wanda ɗan tawagar Sifaniya ne ta 'yan ƙasa da shekara 21, wanda kuma ɗan Colombia ne, zai iya wasa a tsakiyar baya da kuma gefen dama kuma zai cike gurbin da Takehiro Tomiyasu, ya bari.

    Ya yi wa Valencia wasa 90, kuma a kakar da ta wuce kusan a kodayaushe yana wasa inda ya buga wasa 37 daga cikin 38 da ƙungiyar ta yi a La Liga.

  4. Tsohon ɗanbayan Man Utd Tuanzebe ya kai ƙarar ƙungiyar

    Axel Tuanzebe

    Asalin hoton, Getty Images

    Tsohon ɗan wasan baya na Manchester United Axel Tuanzebe ya kai ƙarar ƙungiyar bisa zargin ba shi shawarar da ba ta dace ba a kan lafiyarsa.

    A makon da ya wuce ne ɗanwasan mai shekara 27, wanda ya koma Burnley daga Ipswich a bazaran nan, ya shigar da ƙara ne a kan United.

    Ƙarar da danganci wani lokaci ne daga watan Yuli na shekara ta 2022, wanda ya danganci wani rauni da ba a sani ba - wanda kuma ake ganin zai iya cin har sama da fam miliyan 1.

    A shekararsa ta ƙarshe a United Tuanzebe, ya tafi jinya tsawon kwana 195, kafin ƙungiyar ta bayar da aronsa ga Stoke a watan Janairun 2023, inda ya yi wasa biyar kawai.

    Ya bar Old Trafford a 2023, inda ya koma Ipswich a watan Satumba na wannan shekara inda ya yi wasa 45 har ma ya taimaka wa ƙungioyar ta tsallaka zuwa gasar Premier a 2024.

    A lokacin da BBC ta yi ƙoƙarin jin ta bakin lauyan ɗanwasan da kuma Manchester United dukkanninsu sun ƙi cewa komai a kan lamarin.

  5. Forest na barazanar kai ƙarar Tottenham a kan Gibbs-White

    Morgan Gibbs-White

    Asalin hoton, Getty Images

    Nottingham Forest na duba yuwuwar ɗaukar matakin shari'a a kan Tottenham saboda sha'awar da Spurs ɗin ta nuna a kan ɗanwasan tsakiya na Forst ɗin Morgan Gibbs-White, ba bisa ƙa'ida ba.

    A ƙa'ida ƙungiya ba za ta yi wa duk wani ɗanwasa da yake da kwantiragi da wata ƙungiya ba, har sai ta samu izinin yin hakan daga ƙungiyar ɗanwasan.

    Ana ganin Forest na dubawa ta ga ko akwai wata ƙa'ida ta sirrin yarjejeniyar da ke tsakani a kan siɗirar damar sayar da ɗanwasan ta fam miliyan 60 a kwantiraginsa da aka saɓa.

    BBC ta fahimci cewa Forest ta kafe lalle cewa Tottenham ba ta nemi izininta ba ta je ta yi magana da Gibbs-White, saboda haka za ta ɗauki duk matakin da za ta iya na ganin ta hana tafiyarsa.

    Tottenham dai ta san da duka wannan halin da ake ciki amma har yanzu tana da ƙwarin gwiwa cewa za a yi cinikin.

    A ranar Alhamis BBC ta bayar da rahoton cewa ɗanwasan zai je a gwada lafiyarsa a Tottenhma kafin a kammala cinikinsa a kan fam miliyan 60.

    To amma kuma kwatsam washegari sai wasu majiyoyi suka sheda wa BBC cewa Nottingham Forest na tunanin kai ƙarar Tottenham saboda sha'awar da ta nuna a kan ɗanwasan na tawagar Ingila.

    Yanzu dai makomar Morgan Gibbs-White a Nottingham Forest na nan zaman ƙila-wa-ƙala.

    Kasancewar akwai damar ɗanwasan ya bar ƙungiyar idan an saye shi fam miliyan 60 a yarjejeniyarsa, kuma yanzu an saye shi hakan amma Forest na neman yin ƙafar-ungulu - wasu na ganin Forest ɗin ce za ta iya kwana a ciki idan ɗanwasan ya kai ƙara.

    Kuma ana ganin hakan zai iya sa nan gaba 'yanwasa su yi shayin zuwa ƙungiyar saboda saɓa wannan yarjejeniyar.

  6. Kun san kuɗin da aka bai wa ƙungiyoyin da suka shiga gasar Club World Cup?

    Kambin da aka ci na gasar Clup World Cup

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɗaya daga cikin manyan batutuwan da aka riƙa yi a tsawon gasar cin kofin duniya ta ƙungiyoyi - wato Clup World Cup, shi ne kuɗin da za a bayar ga waɗanda suka yi nasara a gasar.

    An ware dala miliyan 1000 kwatankwacin fam miliyan 726 da za a bai wa ƙungiyoyi 32 da suka shiga sabuwar gasar, inda za a raba dala miliyan 525 a tsakanin dukkanin ƙungiyoyin da suka fafata, sannan za a bayar da dala miliyan 475 da za a bayar daidai da ƙoƙarin da ƙungiya ta yi.

    An bai wa ƙungiyoyin Turai tsakanin dala miliyan 12.81 da miliyan 38.19 saboda zuwa gasar kawai, yayin ƙungiyoyin da suka je daga Latin Amurka aka ba su dala miliyan 15.21, su kuwa ƙungiyoyin nahiyar Amurka ta Arewa da ta tsakiya da Asia da kuma Afirka - miliyan 9.55, su kuwa ƙungiyoyin Oceania aka ba su dala miliyan 3.58.

    Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya Fifa ba ta tabbatar da ainahin kuɗin da ta bai wa ɗaiɗaikun ƙungiyoyin Turai ba na shiga gasar, illa an yi amfanbi da ƙididdigar shafin intanet da ke bayar da bayanan kuɗaɗe na wasan ƙwallon ƙafa- The Swiss Ramble aka fitar da alƙaluman.

    Ƙungiyar gasar Premier ta Ingila Chelsea ce ta yi nasara a wasan ƙarshe na gasar inda ta doke PSG da ci 3-0.

    Ladan kuɗin da ƙungiyoyin suka samu ya taimaka musu sosai musamman ma Chelsea da Manchester City.

    Chelsea ta kashe fam miliyan 198 wajen sayen 'yanwasa zuwa yanzu a wannan bazarar, wajen sayen irin su Joao Pedro da Liam Delap, kuma ta mayar da fam miliyan 84 daga cikin wannan kuɗin a sakamakon kuɗin da aka ba ta a gasar.

    Haka ita ma Manchester City duk da ƙungiyar Al-Hilal ta Saudiyya ta yi waje da ita daga gasar tun da farko-farko, to amma ta samu kuɗin da ta mayar da kusan kashi 35 cikin ɗari na kuɗin da ta kashe a bazara - wato ta mayar da fam miliyan 31 da ta kashe wajen sayen Rayan Ait-Nouri daga Wolves.

  7. Luis Enrique zai iya fuskantar hukunci kan marin Pedro

    Kociyan PSG na hatsaniya da Pedro

    Asalin hoton, Getty Images

    Bisa ga dukkan alamu kociyan PSG Luis Enrique zai iya fuskantar hukunci saboda 'yar hatsaniyar da ta barke tsakanin 'yan wasa bayan da Chelsea ta casa kungiyarsa ta PSG da ci 3-0 a wasan karshe na gasar cin kofin duniya na kungiyoyi - Club World Cup a jiya Lahadi.

    Bayan tashi daga wasan da aka yi a New Jersey, an samu hatsaniya a tsakanin 'yan wasan inda aka ga kociyan na PSG dan Sifaniya ya mari Joao Pedro, wanda ya ci kwallo ta uku a wasan, a minti na 43, bayan da Palmer ya zura biyu a minti na 20 da kuma 30.

    To amma kuma tsohon kociyan na Barcelona ya ce yana kokarin raba 'yan wasan ne da suke hatsaniya kawai.

    Ya ce :"Ba ni da wata matsala kan bayyana yadda na ji a karshen wasan a yadda ya kasance. Abin takaici ne ga dukkaninmu, saboda haka abu ne mawuyaci a iya kauce wa irin wannan abu."

    Ya kara da cewa, ''kowa yana da hanu. Ba abu ne da ya dace ba da kuma yadda sakamakon wasan ya haifar da haka.

    "Na ga yadda Maresca, yake ture sauran 'yanwasan to kuma dole ne mu raba su, na san abin da ya sa ransu ya baci,'' in ji kociyan na PSG.

    Ya ce: ''Kowa yana son ya yi nasara a wasa, kuma a karshe ransu ya baci saboda yadda ya kasance.''

    Bayan 'yanwasan PSg sun janye kociyan nasu, an ga Pedro ya hakura shi ma.

    An ji danwasan na Brazil na cewa 'yan kungiyar ta Faransa sun harzuka ne. Ba na bukatar in yi wata magana a kansu.''

  8. Arsenal na dab da kammala cinikin Gyokeres

    Viktor Gyokeres

    Asalin hoton, Getty Images

    Ana sa ran nan da 'yan wasu sa'o'i Arsenal za ta kammala cinikin Viktor Gyokeres na Sporting a kan kudi yuro miliyan 73.5 kwatankwacin fam miliyan 63.5m.

    Wasu majiyoyi sun tabbatar wa da BBC cewa cinikin danwasan gaban na Sweden ya kusa kammala in banda wasu 'yan bayanai da suka rage a cimma matsaya a kansu.

    Dukkanin bangarorin da ke cikin maganar na so a kammala komai ta yadda Gyokeres zai tafi da Arsenal wasannin shirin tunkarar kaka mai kamawa a Asia a karshen makon da muke ciki.

    Da farko dai Arsdenal ta taya danwasan ne a kan yuro miliyan 70 amma daga baya ta kara da 'yan wasu tsarabe-tsarabe.

    Tuni danwasan mai shekara 27 ya amince da yarjejeniya zama a Gunners din ta tsawon shekara biyar.

    A farkon watan nan BBC ta ruwaito cewa Arsenal ta karkata ga Gyokeres ne bayan da ta kasa cimma matsaya a cinikin Benjamin Sesko na RB Leipzig.

  9. Sinner ya yi raga-raga da Djokovic a Wimbledon

    Jannik Sinner

    Asalin hoton, Getty Images

    Jannik Sinner ya fitar da Novaj Djokovic daga gasar Wimbledon bayan lallasa shi da ci 6-3, 6-3 6-4 a fafatawarsu ta yau Juma'a.

    Wannan ne karo na shida da Sinner ke doke ɗan wasan na Serbia a jere.

    Sakamakon na nufin cewa Sinner zai kara da Carlos Alcaraz mai kare kambinsa a wasan ƙarshe na gasar Wimbledon ranar Lahadi mai zuwa.

    Sinner shi ne na ɗaya a jerin ƴan wasan Tennis a duniya yayin da Alcaraz ne na biyu.

    A cikin dukkanin manyan gasannin Tenis shida da suka gabata, ɗaya daga cikin ƴan wasan biyu ya kai wasan ƙarshe.

  10. Har yanzu Betis na sa ran sayen Antony

    Antony

    Asalin hoton, Getty Images

    Real Betis za ta dawo yin atisaye ranar Laraba - amma har yanzu ba a samu nasara a cinikin sayen Antony daga Manchester United ba.

    Antony yana Brazil har yanzu bayan da United ta sanar da shi cewa ba zai yi atisaye da tawagarta ba.

    Man United ta ce Antony ya faɗa mata zai bar ƙungiyar kuma ya yanke hukuncin zama a gida (Brazil) har sai ya samu ƙungiya.

    Betis na son Antony - wanda shi ne ɗan wasa na biyu mafi tsada a tarihin United ( fam miliyan 81.3) - amma ba ta da kuɗin kashewa mai yawa. Sai dai tana neman United ta yi ragi kuma ana ci gaba da ciniki.

    Antony ya zura ƙwallo tara a Betis inda ya taka leda a kakar da aka kammala a matsayin aro, kuma ya taimaka wa ƙungiyar zuwa wasan ƙarshe na gasar Uefa Conference League.

  11. UEFA ta hana Crystal Palace damar buga Europa duk da ta cancanta

    Crystal Palace

    Asalin hoton, Getty Images

    UEFA ta yanke hukunci cewa Crysal Palace ba za ta buga gasar Europa League ba a kakar wasa mai zuwa, a maimakon haka za ta buga gasar Europa Conference League.

    Hukuncin ya faru ne a dalilin dokar hukumar kula da ƙwallon ƙafa ta Nahiyar Turai wadda ta haramta wa ƙungiyi biyu mallakin mutum ɗaya buga wata gasar Turai a lokaci guda.

    John Textor shi ne mutum mafi yawan hannun jari a ƙungiyar Crystal Palace da ke Ingila da kuma Lyon ta Faransa.

    Crystal Palace ta yi ƙoƙarin kare kanta da cewa John Textor ba shi da wani ƙarfin faɗa a ji a ƙungiyar amma UEFA ba ta amince da wannan batun ba.

    A farkon makon nan ne aka soke hukuncin da aka yanke wa Lyon na komawa gasar Ligue 2 saboda ƙarancin kuɗi da take fuskanta - in da ba soke ba, Palace za ta samu damar buga Europa League.

    Akwai yiwuwar za a maye gurbin Palace a Europa League da Notthingham Forest wadda ta kammala kakar 2024/2-25 a matsayin ta bakwai a teburin Premier.

  12. Nottingham Forest za ta maka Tottenham a kotu

    Morgan Gibbs-White

    Asalin hoton, Getty Images

    BBC ta samu bayanin cewa Nottingham Forest na shirin maka kungiyar Tottenham a kotu saboda sha'awar ɗan wasanta Morgan Gibbs-White.

    Ana ganin cewa Tottenham ta karya dokar Premier League da ta haramta wa ƙungiyoyi tattaunawa da ɗan wasa ba tare da da amincewar ƙungiyarsa ba, muddin yana da yarjejeniya da ƙungiyar.

    Ita Forest ta ce ba ta taɓa bai wa Tottenham damar tattaunawa da Gibbs-White ba kuma za ta yi duk ƙoƙarinta domin ganin cewa ɗan wasan bai koma Spurs ba.

    A baya BBC ta ruwaito cewa Gibbs-White na shirin yin gwajin lafiya a yau Juma'a gabanin sauya sheƙa zuwa Spurs.

  13. Arsenal za ta sayi ƴar wasa mafi tsada a tarihi

    Olivia Smith

    Asalin hoton, Getty Images

    Arsenal - wadda ta lashe kofin Champions League na mata - ta amince ta biya fam miliyan ɗaya domin ɗaukar ƴar wasan gaba ta Liverpool, Olivia Smith mai shekara 20.

    A halin yanzu, ƴar wasan da ta fi tsada a tarihi ita ce ƴar Amurka NaomI Girma wadda Chelsea ta ɗauka kan fam 900,000.

    Sayen ƴar wasan ta Canada da Arsenal ke shirin yi na nuna ci gaba a ƙwallon ƙafar mata kuma ya nuna cewa akwai buƙatar kashe kuɗaɗe da yawa domin cimma nasara.

    Ana dai ganin cewa ba lallai Olivia ta iya samun wajen bugawa a Arsenal ba a halin yanzu, sai dai ta fara daga benci.

    A shekaru biyar da suka gabata, ƴar wasan da ta fi tsada ita ce Pernille Harder da Chelsea ta saya kan fam 250,000.

  14. Henderson zai koma Brentford

    Jordan Henderson

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɗan wasan Ingila, Jordan Henderson zai koma Brentford bayan barin Ajax ta Netherlands a cikin makon nan.

    Ƙungiyoyi da dama sun nuna sha'awarsu ta ɗaukar ɗan wasan mai shekara 35 amma Henderson ya amince da tayin da Brentford ta yi masa.

    Taka leda a gasar Premier League ta Ingila na iya ba shi damar sake buga wa Ingila gasar kofin duniya ta 2026.

    Henderson zai maye gurbin Christian Norgaard ne a Brentford bayan da ɗan wasan na Denmark ya koma Arsenal.

    Henderson - wanda ya buga wa Ingila wasanni 84 - ya koma Ajax ne a 2024 daga Al-Ettifaq ta Saudiyya, amma bai lashe kowane kofi a Netherlands ba.

    Ana sa ran a ƴan kwanakin nan Brentford za ta kammala cinikin kuma Henderson zai fara taka ma ta leda.

  15. Super Falcons ta kai zagaye na gaba a gasar Wafcon

    Super Falcons

    Asalin hoton, CAF

    Najeriya ta doke Botswana a wasansu na gasar cin kofin nahiyar Afirka ta mata da suka buga a yau Alhamis.

    Chinwendu Ihezuo ce ta zura ƙwallo a minti na 89 ana daf da tashi wasan.

    Sakamakon na nufin cewa Super Falcons ce ke saman teburin rukunnin B inda ta haɗa maki shida, kuma ta samu damar zuwa zagayen ƴan 16.

    Ita kuwa Botswana ita ce ta ƙarshe a teburin yayin da ta gaza cin kowane wasa.

    Idan har tana son ta samu damar zuwa matakin gaba, dole ne ta doke Tunisia a wasansu na ƙarshe a rukunnin.

  16. Wafcon 2024: Abin da ya kamata ku sani kan wasan Najeriya da Botswana

    Super Falcons

    Asalin hoton, Super Falcons/X

    Najeriya na karawa da Botswana a wasa na biyu da ƙungiyoyin rukunin B a gasar cin kofin mata ta nahiyar Afirka da ke gudana a Morocco.

    Najeriya ce ta farko a rukunnin bayan ta doke Tunisia da ci 3-0 a wasanta na farko a gasar.

    Idan har Botswana - wadda ta yi rashin nasara a wasanta na farko da Ageria - na son ta kai matakin gaba, dole ne ta nemi dawowa kan ganiyarta ta hanyar doke Najeriya.

    A fafatawa tsakanin ƙasashen biyu a baya, Najeriya ce ta yi nasarar doke Botswana a gasar Wafcon ta 2022 da ci 2-0.

    Botswana za ta dogara da ƴar wasan gabanta Refilwe Tholakele wadda ta taɓa lashe kyautar takalmin zinare a gasar zakarun Afirka ta kulob-kulob a 2023.

    Najeriya kuwa za ta so ƴar wasanta Rinsola Babajide ta maimaita rawar da ta taka a wasan farko inda ta zura ƙwallo kuma ta bayar aka ci.

  17. Edin Dzeko ya koma Fiorentina

    Edin Dzeko

    Asalin hoton, Getty Images

    Edin Dzeko mai shekara 39 ya sanya hannu kan yarjejeniya da Fiorentina, hakan na nufin zai ci gaba da taka leda har ya cika shekara 40 a duniya.

    Tsohon ɗan wasan na Man City Dzeko ya sanya hannu ne kan yarjejeniyar shekara ɗaya kuma idan ya kammala zai iya ƙara tsawaitawa.

    Dzeko ya koma Fiorentina ne bayan ya bar Fernabache inda ya zura ƙwallo 21 cikin wasa 53 a kakar wasan da ta gabata.

  18. Jordan Henderson ya bar Ajax

    Jordan Henderson

    Asalin hoton, Getty Images

    Ajax ta katse yarjejeniyar Jordan Henderson da ƙungiyar duk da cewa yana da sauran shekara ɗaya da ta rage masa.

    Hakan na nufin kowace ƙungiya na iya ɗaukar ɗan wasan kyauta yayin da wasu daga Turai da sauran nahiyoyi ke nuna sha'awarsu.

    Ɗan wasan mai shekara 35 ya koma Ajax ne a 2024 bayan shafe wata shida a Al Ittifaq da ke Saudiyya.

    Bayan zuwansa Ajax, ya kasance kyaftin ɗin ta inda ya buga wasa 50 amma bai lashe Kofi ko daya ba.

    "Ina so na gode wa kowa a Ajax. Buga wa wannan ƙungiyar abin alfahari ne" in ji Henderson.

    Akwai raɗe-raɗin cewa Henderson zai iya komawa Sunderland ta Ingila, kasancewar ƙungiyar yake goyon baya tun yana yaro kuma a nan ya fara taka leda.

  19. Tottenham na tattaunawa da Nottingham Forest kan Gibbs-White

    Gibbs-White

    Asalin hoton, Getty Images

    Tottenham ta fara tattaunawa da Nottingham forest domin ɗaukar ɗan wasan tsakiya morgan Gibbs White kan kuɗi fam miliyan 60.

    BBC ta samu bayanai daga wata majiya cewa ɗan wasan na da darajar fam miliyan 60 wanda idan wata ƙungiya ta biya, ɗan wasan zai iya zuwa idan ya ga dama.

    Man City ta nuna sha'awar Gibbs-White a baya-bayan nan amma daga baya ta fasa.

    Ɗan wasan ya zura ƙwallo bakwai a gasar Premier a kakar wasa da aka kammala, lamarin da ya sa ƙungiyoyi da dama ke sha'awarsa, amma yanzu Tottenham ta dage kan ɗaukarsa.

    Idan abubuwa suka tafi daidai Gibbs-White mai shekara 25 zai iya komawa Spurs nan da ƴan kwanaki.

    Tottenham mai sabon koci Thomas Frank na shirin kammala ɗaukar Mohammed Kudus daga West Ham kan fam miliyan 55 kuma tana sha'awar ɗan Brentford Yoane Wissa.

  20. Barau FC ta samu gurbi a gasar Premier ta Najeriya

    Barau FC

    Asalin hoton, Barau FC/FB

    A yau Alhamis ne Barau FC ta samu gurbin zuwa gasar Premier League ta Najeriya bayan ta doke Doma United 2-0, inda Usman Maidubji da Shammasu Muhammad suka zura ƙwallo a wasan.

    Wannan ne karon farko da ƙungiyar ke samun damar buga gasar a tarihinta.

    Hakan na nufin za a buga wasan hammaya ta jihar Kano a kaka mai zuwa tsakanin Barau FC da Kano Pillars karon farko a tarihi.

    Barau FC ƙungiya ce da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Sanata Barau Jibrin ke mallaka.

    Haka zalika Wikki Tourists ta jihar Bauchi ta samu gurbin dawowa gasar a bana bayan faɗuwarta a 2023.