Arsenal na shirin ɗaukar Eze, an sanar da Man U farashin Mbuemo

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal na shirin bayar da wani ɗan wasa a cinikin da ta ke yi kan ɗan wasan Crystal Palace Eberechi Eze, mai shekara 27, kuma da alama za ta iya doke Tottenham Hotspur wurin ɗaukar ɗan wasan na Ingila. (Sun)
Akwai yiyuwar Brentford za ta buƙaci a biya fam miliyan 65 kan ɗan wasanta Bryan Mbeumo, mai shekara 25, bayan ta yi watsi da tayin fam miliyan 55 da kuma fam miliyan 62.5 daga Manchester United kan ɗan wasan na Kamaru. (Mirror)
Ɗan wasan gaba na Sporting da Sweden Viktor Gyokeres, mai shekara 27, ya shirya jira har zuwa ƙarshen bazara don cimma yarjejeniyar aro zuwa wata ƙungiya ta Turai idan har bai cimma burinsa na komawa Arsenal ba. (Sun)
Ɗan wasan Ingila Jadon Sancho, mai shekara 25, ya shirya rage albashinsa domin ya koma Juventus daga Manchester United, amma har yanzu kulob ɗin na Seria A bai shirya cika sharuɗɗan da za su tabbatar da ƙulla yarjejeniya ba. (Il Corriere dello Sport)
Nottingham Forest na zawarcin ɗan wasan PSV Eindhoven da Belgium Johan Bakayoko, mai shekara 22, yayin da ta ke shirin maye gurbin Anthony Elanga, mai shekara 23, wanda ake ganin zai koma Newcastle United. (Telegraph)
Manchester United na shirin karɓar fam miliyan 8 a matsayin wani ɓangare yarjejeniyar da ta ƙulla a lokacin da ta sayar wa Forest da Elanga a 2023. (Talksport).
Har ila yau, Forest na nazari kan abokin wasan Bakayoko na Belgium Malick Fofana, mai shekara 20, yayin da ake alaƙanta ɗan wasan na Lyon da komawa Chelsea ko Bayern Munich a wannan bazarar. (Sky Sports)
Unai Emery yana sha'awar ɗaukar ɗan wasan gaban Barcelona Ferran Torres, mai shekara 25, zuwa Aston Villa kuma a shirye ya ke ya biya fam miliyan 43 kan ɗan wasan na Sifaniya. (Fichajes)
Yunƙurin Arsenal na ɗaukar ɗan wasan bayan Valencia Cristian Mosquera, mai shekara 21, ya ci tura yayin da kulob ɗin na La Liga ke neman sama da fam miliyan 20 kan ɗan wasan na Sifaniya. (Mirror)
Bayern Munich ta tattauna da wakilan Christopher Nkunku yayin da ta ke nazarin ɗaukar ɗan wasan gaban Chelsea da Faransa mai shekara 27. (Bild).
Napoli ta miƙa tayin fam miliyan 42 kan ɗan wasan gaban Liverpool Darwin Nunez, mai shekara 26. (Gianluca di Marzo)
Sunderland na dab da kammala cinikin ɗan wasan gaban Morocco Chemsdine Talbi mai shekara 20 daga Club Brugge na Belgium. (Fabrizio Romano)
Atalanta ta yi watsi da tayin fam miliyan 45.7 da ƙungiyar Al-Qadsiah ta Saudiyya ta yi kan ɗan wasan gaba na Italiya Mateo Retegui, a yayinda ƙungiyar ta Serie A ta buƙaci fam miliyan 51.8 kan ɗan wasan mai shekara 26. (Football Italia)











