Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Labaran abubuwan da ke faruwa dangane da wasanni

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku sharhi da bayanai kan labarin wasannin da zai gudana daga ranar Asabar 24 zuwa 30 ga watan Mayun 2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu da Ahmad Bawage

  1. Salah ya lashe ƙyautar gwarzon ɗan wasan Premier League, Liverpool

    Ɗan wasan Liverpool, Liverpool, Mohamed Salah ya lashe ƙyautar gwarzon ɗan wasan Premier League na bana.

    Wannan shi ne karo na biyu da mai shekara 32 ɗan ƙwallon tawagar Masar ya ƙarbi ƙyautar, bayan 2017/18.

    Salah, wanda ya ja ragamar Liverpool ta lashe Premier League a kakar nan da cin ƙwallo 28, ya yi takara tare da Virgil van Dijk da Ryan Gravenberch da ɗan wasan Arsenal, Morgan Gibbs-White da Declan Rice da na Newcastle, Alexander Isak da na Brentford, Bryan Mbeumo da kuma Chris Wood na Nottingham Forest.

    Wannan shi ne karon farko tun bayan 2018-19 da ba ɗan ƙwallon Manchester City ne ya lashe ƙyautar ba.

    Ranar Lahadi za a kammala gasar Premier League, inda za a yi wasa 10 daga ciki Liverpool za ta kara da Crystal Palace, kuma Salah mai ƙwallo 28 ya bayar da 18 aka zura a raga.

  2. Burn ya tsawaita yarjeniyarsa da Newcastle, Newcastle United

    Ɗan wasan tawagar Ingila mai taka leda a Newcastle United mai tsare baya, Dan Burn ya saka hannu kan yarjejeniyar da zai ci gaba da taka leda a St James Park zuwa karshen kakar 2027

    Mai shekara 33 ya koma ƙungiyar daga Brighton a Janairun 2022, wanda yake kakar karshe da ta rage masa a sauran ƙunshin ƙwantiraginsa.

    Shi ne ya fara cin ƙwallo, sannan ya lashe ƙyautar ɗan wasan da ya fi taka rawar gani a watan Maris da Newcastle ta doke Liverpool ta kuma ɗauki Carabao Cup a Wembley, babban kofin da ta ci a karon farko tun bayan shekara 70.

    Burn ya buga wasa 45 a dukkan karawa a kakar nan.

  3. Jama'a barkanmu da wannan lokacin

    Sunana Mohammed Abdu zan gabatar muku da sharhi da bayanai kan labaran wasanni a ranar Asabar.

    Za ku iya bayar da gudunmuwa a shirin kai tsaye a BBCHausa Facebook ko kuma a X.