Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Labaran abubuwan da ke faruwa dangane da wasanni
Wannan shafi ne da zai ke kawo muku sharhi da bayanai kan labarin wasannin da zai gudana daga ranar Asabar 24 zuwa 30 ga watan Mayun 2025.
Taƙaitattu
- Chelsea ta lashe Conference League bayan cin Real Betis 4-1 ranar Laraba a Poland
- Liverpool da Madrid na gogayya kan Wirtz, Rashford ya gana da shugabannin Barca
- Chelsea ta zama ta farko da ta lashe dukkan kofin Uefa da ya haɗa da Champions League biyu da Europa biyu da Cup winn ers Cup biyu da Super Cup biyu da kuma na Conference League
- Za ku iya muhawara a BBCHausa Facebook
- Mourinho shima ya lashe dukkan kofunan Uefa
- Chelsea tana sawun gaba a zawarcin Delap na Ipswich Town
- Fitattun ƴan wasan da suka yi ban kwana da ƙungiyoyinsu a bana
Rahoto kai-tsaye
Mohammed Abdu da Ahmad Bawage
Bayern Munich ta ɗauki Tah daga Bayern Leverkusen, Bundesliga
Bayern Munich ta sanar da ɗaukar mai tsaron baya, Jonathan Tah daga Bayer Leverkusen, bayan da ƙwantiraginsa ya kare a ƙungiyar.
Ɗan wasan tawagar Jamus, mai shekara 29 ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka huɗu da ƙungiyar da ta lashe Bundesliga na kakar da aka kammala.
Tah ya yi kaka 10 a Leverkusen da lashe Bundesliga da German Cup a 2023 karkashin Xabi Alonso, wanda ya koma aikin horar da Real Madrid ranar Lahadi.
Tun farko an yi ta alakanta ɗan wasan da ƙungiyoyin Premier League da suka haɗa da Liverpool da Manchester United da Tottenham da na La Liga da suka haɗa da Barcelona da kuma Real Madrid.
Amma ya zaɓi ya koma Bayern Munich,bayan da mai tsaron bayanta, Eric Dier ya koma Monaco mai buga Ligue 1.
Tah ya buga wa tawagar Jamus wasa 35, bayan da ta fara gayyatarsa a 2016.
Bayern ta lashe Bundesliga na 2024/25 da tazarar maki 13 tsakani da Leverkusen, wadda ta yi ta biyu a teburin.
Jackson zai buga wa Chelsea wasa da Betis, Real Betis da Chelsea
Kociyan Chelsea, Enzo Maresca zai yi amfani da Nicolas Jackson ɗaya daga canje-canjen da ya yi a wasan da ta doke Nottingham Forest ranar Lahadi a Premier League.
Mai tsaron raga, Filip Jorgensen da Malo Gusto da Trevoh Chalobah da kuma Benoit Badiashile za su fara karawar, yayin da Reece James da Levi Colwill da kuma Jadon Sancho suna benci.
Chelsea XI: Jorgensen, Gusto, Chalobah, Badiashile, Cucurella, Caicedo, Fernandez, Madueke, Palmer, Neto, Jackson.
Masu cin benci: Sanchez, Bergstron, Tosin, Colwill, Acheampong, James, Amougou, Dewsbury-Hall, George, Sancho, Nkunku, Guiu
Tsohon ɗan wasan Tottenham, Giovani Lo Celso yana benci
Manuel Pellegrini ya fitar da waɗanda za su buga masa wasan har da ɗan ƙwallon Manchester United, mai buga wa Betis wasannin aro, Antony da wasu fitattun yan wasan
Real Betis XI: Adrian, Gabaly, Natan, Bartra, Rodriguez, Cardoso, Fornals, Antony, Isco, Ezzalzouli, Bakambu.
Masu zaman benci: Vieites, Gonzalez, Perraud, Altimira, Lo Celso, Ruibal, Mendy, Rodriguez, Ortiz, Flores, Garcia
Ƴan wasan Chelsea da za su kara da Real Betis, Real Betis da Chelsea
Ko Chelsea za ta lashe kofi a Poland?, Real Betis da Chelsea
Saura wasa ɗaya Enzo Maresca ya lashe kofi a bana, bayan da Chelsea ta kai wasan karshe da za ta yi da Real Betis a Poland.
Ƙungiyar Sifaniya ce ke gabanta, wadda Manuel Pellegrini ke horarwa - wanda ya ɗauki kofin Premier League a Manchester City a 2013-14.
Ko Chelsea za ta lashe kofi karkashin Enzo Maresca a karon farko tun bayan since 2021.
Ko Chelsea za ta ɗauki kofi a bana?, Real Betis da Chelsea
Chelsea ta samu gurbin Shiga Champions League, bayan kammala kakar nan a mataki na huɗu a teburin Premier League.
Ko ƙungiyar Stamford Bridge za ta lashe kofi a kakar nan.
An yi wa United ihu bayan rashin nasara a Malaysia, Manchester United
Manchester United ta yi rashin nasara 1-0 a wasan sada zumunta a hannun fitattun Asia 11 da suka kara a Kuala Lumpur a Malaysia ranar Laraba a gaban yan kallo sama da dubu 72 da rabi.
Ranar Juma'a United za ta kece raini da tawagar Hong Kong a daya wasan na sada zumunta.
United ta kare a mataki na 15 a kasan teburin Premier ta bana ba tare da lashe kofi koda na shayi ba a daya daga kaka mafi muni da ta yi.
Zan so Newcastle kada ta sayar da ƴan wasanta - Cabaye
Tsohon ɗan wasan Newcastle United, Yohan Cabaye ya ce zai so ƙungiyar St James Park ta riƙe ƴan ƙwallonta, domin ta samu damar lashe manyan kofuna, bayan da za ta buga Champions League a baɗi.
Newcastle United ta samu gurbin shiga babbar gasar tamaula ta zakarun Turai ranar Lahadi, bayan da ta kare a mataki na biyar a teburin Premier League.
Samun gurbin shiga Champions League babban lamari ne ga koci, Eddie Howe in ji Cabaye ''Yana da ƙyau kada ya sayar da ƴan wasa kamar su Alexander Isak da Bruno Guimaraes da Sandro Tonali da Tino Livramento, waɗanda wasu ƙungiyoyi da dama ke son zawarci.
Cabaye, ya taka rawar gani a Newcastle United a kaka uku tsakanin 2011 zuwa 2014.
Man United ta amince za ta biya ƙunshin yarjejeniyar Cunha, Manchester United
Manchester United ta cimma yarjejeniyar biyan kunshin kwantiragin, Matheus Cunha, tuni kuma Wolverhampton ta bai wa dan wasan tawagar Brazil izinin tattaunawa da kungiyar Old Trafford.
Tun farko Wolves ta ki amincewa da tayin da United ta yi na biyan kudin Cunha cikin kaka biyar.
Rio Ferdinand zai bar sharhi da bayanan tamaula a TNT Sports, Sharhi da bayanan wasannin tamaula
Rio Ferdinand ya sanar cewar zai bar aikin sharhi da bayanan tamaula a TNT Sports a karshen kakar nan, zai koma wata sabgar da yake sha'awa.
Tsohon ɗan wasan tawagar Ingila mai taka leda a Manchester United yana sharhi da bayanan tamaula kusan kaka 10, yanzu zai daina aikin da zarar an kammala wasan karshe a Champions League da za a yi ranar Asabar tsakanin Paris St Germain da Inter Milan a Allianz Arena.
Labaran da jaridu ke wallafawa kan cinikin ƴan wasa, Daga jaridu
Ƙungiyar Al-Hilal ta Saudiyya ta gabatar da tayinta kan Kyeftin ɗin Manchester United, Bruno Fernandes na Portugal mai shekara 30, sannan ta faɗa ma sa yana da wa'adin sa'o'i 72 ya yanke hukunci kan amincewa da yarjejniyar ko akasin haka. (Mail, external)
Manchester City ta bi sahun masu fafutukar ɗan wasan Lyon mai shekara 21 daga Faransa, Ratan Cherki da ke buga tsakiya. Ana dai alakanta ɗan wasan da Liverpool da Chelsea. (Telegraph - subscription required, external)
Everton ta bi sahun Leeds United a farautar ɗan wasan nan mai shekara 33 daga Newcastle United da Ingila, Callum Wilson, wanda ba shi da kwantiragi a hannu. (The Sun, external)
Tottenham ta bada kofar iya sayen ɗan wasan Bayern Munich da Jamus, Leroy Sane mai shekara 29, wanda kwantiraginsa ke karewa a watan gobe.(Sky Sports, external)
Mataimakan Guardiola Lillo da Dominguez da Vicens za su bar Etihad
Manchester City ta sanar cewar mataimakan Pep Guardiola, Juanma Lillo da Inigo Dominguez da kuma Carlos Vicens za su bar ƙungiyar.
Lillo da kuma Dominguez za su bar Etihad lokacin da yarjejeniyarsu za ta kare a karshen kakar nan.
Shi kuwa Vicens ya karɓi aikin horar da Braga ta Portugal.
Lillo, ya zama na biyu a jerin mataimakin Pep Guardiola a 2020 daga baya ya bar Etihad a 2022 ya koma horar da Al-Sadd, sai ya sake komawa City a 2023,
City ta ɗauki Dominguez a lokacin da Lillo ya sake komawa Etihad a karo na biyu, yayin da Vicens ya koma ƙungiyar a 2017, wanda ya ja ragamar matasa ƴan kasa da shekara 18 ta lashe FA Cup a 2020, sanna ya yi aiki tare da Guardiola kaka huɗu.
Alcaraz ya kai zagaye na uku a French Open, French Open
Reigning French Open champion Carlos Alcaraz booked his spot in the third round at Roland Garros on Wednesday with a 6-1, 4-6, 6-1, 6-2 win over Fabian Marozsan.
Ɗan kasar Sifaniya, wanda ya taka rawar gani a gasar kan taɓo a Monte Carlo da Rum, shi ne ke rike da kofin bara a gasar ta Roland Garros.
Alcaraz zai buga wasan gaba da ko dai Giovanni Mpetshi Perricard ko kuma Damir Dzumhur a zagayen ƴan 32.
Yamal ya saka hannu kan yarjeniyar kaka shida a Barcelona, Barcelona
Lamine Yamal ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da taka leda a Barcelona, wanda ya taka rawar gani a kakar nan da ƙungiyar ta lashe kofi uku na Sifaniya a bana.
Tun farko yarjejeniyar matashin mai shekara 17 za ta kare a karshen kakar 2025-26, sai dai yanzu zai ci gaba da taka leda a Barcelona zuwa karshen kakar 2031.
Yamal, wanda ya fara yi wa Barca wasa yana da shekara 15 a 2023, ya ci ƙwallo 18 da bayar da 25 aka zura a raga a wasa 55 a bana da ƙungiyar ta ɗauki La Liga da Copa del Rey da kuma Spanish Super Cup a kakar farko karkashin koci, Hansi Flick.
Yamal ya ci ƙwallo 25 a wasa 115 a Barcelona, shi ne matashin da ya kafa tarihin cin ƙwallo a La Liga da Copa del Rey da kuma Spanish Super Cup.
Haka kuma Yamal, wanda zai cika shekara 18 cikin watan Yuli, shi ne kuma matashin da ya buga wa Barcelona wasa 100.
Ya kuma buga wa tawagar Sifaniya wasa 19, yana cikin waɗanda suka lashe Euro 2024, bayan cin Ingila 2-1 a wasan karshe a Berlin.
Tuni dai Barcelona ta tsawaita yarjejeniyar kociyanta, Hansi Flick da ɗan wasa Raphinha.
Jasmine Paolini ta kai zagaye na uku a French Open, French Open
Wadda ta yi ta biyu a bara a French Open, Jasmine Paolini ta kai zagaye na uku a French Open, bayan caskara Ajla Tomljanovic ta Australia ranar Laraba da cin 6-3, 6-3.
Paolini ta yi nasara ta takwas a ƙwallon tennis tun bayan lashe Italian Open.
Ƴar kasar Italiya za ta fafata da ko dai ƴar kasar Rasha, Anastasia Potapova ko kuma ta Ukraine, Yuliia Starodubtseva.
Brentford ta ɗauki Kayode bayan kammala wasannin aro, Premier League
Brentford ta kammala ɗaukar mai tsaron baya, Michael Kayode bayan da ya kammala buga wasannin aro a 2024-25.
Kayode, mai shekara 20, ya koma buga Premier League daga Fiorentina a watan Janairu, ya amince da ƙunshin yarjejeniyar kaka biyar da cewar za a iya tsawaita masa ita wata 12.
Ɗan wasan tawagar Italiya ta ƴan kasa da shekara 21, ya yi wasa 12 a Premier League a Brentford.
Zheng Qinwen ta kai zagaye na uku a French Open, French Open
Wadda ta lashe lambar yabo ta zinare a Olympic a ƙwallon tennis, Zheng Qinwen ta kai zagaye na uku a French Open ranar Laraba bayan doke Emiliana Arango da cin 6-2, 6-3..
Ƴar kasar China ta ci wasa takwas a jere a Roland Garros tun bayan da ta yi fice a Olympic gold a bara.
Zheng za ta fuskanci Victoria Mboko ta Canada a zagaye na huɗu a French Open.
Inter za ta sa riga mai ruwan ɗorawa a wasa da PSG a Champions League, Paris St Germain da Inter Milan
Inter Milan za ta sa riga mai ruwan ɗorawa ranar Asabar a wasan karshe a Champions League da za ta yi da Paris St Germain da za su kara a Allianz Arena.
Zuwa yanzu Inter ta buga wasan karshe karo shida a Champions League ko kuma European Cup tun daga 1964, kuma ba ta taɓa sa rigar ba a karawar karshe.
Hakan ya biyo bayan da PSG, wadda ita ce kamar wadda take gida za ta sa farar riga da ratsin ja, kenan ba dama Inter ta saka farar riga da ratsin bakaƙen ratsi ba kamar yadda ta saba.
Inter Milan tana da sa'a a riga mai launin ruwan ɗorawa, bayan da ta yi nasara a kan Sparta Prague 2-0 a gasar ta zakarun Turai a cikin watan Maris a zagayen ƴan 16.
Wasa ɗaya aka ci Inter a Champions League a kakar nan, shi ne a Bayern Leverkusen a karawar da ta sa farar riga mai ratsin bakaƙen layuka a Disamba.
Labaran da jaridu ke wallafawa kan cinikin ƴan ƙwallo, Daga jaridu
Arsenal ta tattauna da wakilin ɗan wasan Sporting, Viktor Gyokeres a Lisbon tare da gabatar da tayin fam miliyan 58.7 ga ɗan wasan na Sweden. (Correio da Manha - in Portuguese, external)
Manchester United ta amince da sharudan cimma yarjejeniya da ɗan wasan Ipswich, Liam Delap inda take jiran hukunci daga ɗan wasan na gaba. (ESPN, external)
Ɗan wasan Portugal Cristiano Ronaldo mai shekara 40, na shirin barin ƙungiyarsa ta Al-Nassr da ke Saudiyya, domin cimma sabuwar kwantiragi da wata ƙungiyar gabanin soma wasannin ƙungiyoyin duniya da za a soma a ranar 15 ga watan Yuni a Amurka.(Telegraph - subscription required, external)
An maye gurbin Raul Gonzalez da Arbeloa a matasan Real Madrid, Real Madrid
Tsohon ɗan wasan tawagar Sifaniya, Alvaro Arbeloa ya maye gurbin Raul Gonzalez a matakin kociyan karamar ƙungiyar Real Madrid Castilla, kamar yadda aka sanar ranar Laraba.
Arbeloa ya lashe kofin duniya a 2010 da European Championship biyu a wasa 56 da ya yi wa Sifaniya da ɗaukar kofuna da yawa a Real Madrid daga ciki har da LaLiga da kuma Champions League biyu.
Mai shekara 42, ya yi ritaya daga taka leda a 2017, sai dai ya karɓi aikin horar da Real Madrid ta matasa ƴan kasa da shekara 14 a watan Satumbar 2020 daga nan ya koma horar da matasan ƙungiyar ƴan kasa da shekara 19 a 2022.
Castilla tana buga Primera Federacion, gasa mai daraja ta uku a Sifaniya, wadda ta kare a mataki na shida teburi da kasa samun gurbin kai wa matakin gaba.