Mbappe ya lashe ƙyautar takalmin zinare a matakin mafi cin ƙwallaye a Turai, Europe golden shoe
Kylian Mbappe ne ya lashe ƙyautar takalmin zinare a matakin wanda ya fi cin ƙwallaye a dukkan gasar Turai, bayan da ya ci Real Sociedad 2-0 ranar Asabar a gasar La Liga.
Kenan din tawagar Faransa ya ci ƙwallo 31 a lik jimilla a kakarsa ta farko a babbar gasar tamaula ta Sifaniya, kuma shi ne kan gaba a cin ƙwallye a La Liga a kakar nan.
Kenan yana gaban ɗan wasan Sporting, Victor Gyokeres mai ƙwallo 39 da na Liverpool, Mohamed Salah mai 29 a raga.
Idan ɗan wasa ya ci ƙwallo a manyan gasar Turai biyar da ta haɗa da Premier League da La Liga da Bundesliga da Serie A da kuma Ligue 1 - ana bayar da maki biyu duk ƙwallo ɗaya.
Idan aka zura ƙwallo tun daga gasa mai daraja ta shida zuwa 22 a ma'unin ƙwazon ƙungiyoyin daga Uefa har da ta Portugal, ana bayar da maki 1.5 ga duk ƙwallon da aka ci.
Mbappe shi ne na uku a Real Madrid da ya lashe ƙyautar, bayan Hugo Sanchez a 1989-90 da kuma Cristiano Ronaldo a 2010-11 da 2013-14 da kuma 2014-15.
A jerin jadawalin Mbappe, wanda yake matakin farko yana da maki (62 points), sai Gyokeres mai maki (58.5), da Salah mai maki (58), da Robert Lewandowski da maki (54), da kuma Harry Kane mai maki (52).