Kociyan Sifaniya, Luis de la Fuente ya gayyaci Gavi da Isco ranar Litinin, domin buga wa kasar karawar daf da karshe a Nations League da za ta fafata da Faransa.
Rabon da Gavi, mai shekara 20 ya buga wa Sifaniya tamaula tun Nuwambar 2023, sakamakon raunin da ya yi jinya, wanda ya yi wa Sifaniya karawa 27..
Gavi, wanda ya lashe La Liga da Copa del Rey da Spanish Super Cup a Barcelona, ya buga wasa 42 a kakar nan.
Wannan shi ne karon farko da Isco zai koma buga wa Sifaniya tamaula tun bayan kaka shida.
Mai shekara 33, ya samu goron gayyatar sakamakon rawar da ya taka a bana Real Betis da cin ƙwallo12 da bayar da 10 aka zura a raga a wasa 32 da ya buga da ta kai Betis ta samu gurbin Conference League.
Sifaniya za ta kara da Faransa a Stuttgard ranar 5 ga watan Yuni.
Ƴan wasan tawagar Sifaniya da aka gayyata Nations League:
Masu tsaron raga: Unai Simon, David Raya, Alex Remiro
Masu tsare baya: Pedro Porro, Oscar Mingueza, Robin Le Normand, Pau Cubarsi, Dean Huijsen, Alejandro Grimaldo, Marc Cucurella, Dani Vivian
Masu buga tsakiya: Martin Zubimendi, Fabian Ruiz, Mikel Merino, Alex Baena, Pedri, Fermin Lopez, Gavi, Isco
Masu cin ƙwallye: Alvaro Morata, Lamine Yamal, Nico Williams, Yeremy Pino, Dani Olmo, Samu Aghehowa, Mikel Oyarzabal. (Reporting by Pearl Josephine Nazare in Bengaluru, editing by Ed Osmond)