Sadio Mane ba zai buga wa Senegal wasan sada zumunta biyu da za ta yi nan gaba ba, wanda ya nemi izinin a barshi ya huta.
Mane ne daga fitattun da suka saba bugawa Senegal tamuala da ba zai yi karawar ba da aka gayyaci ƴan wasa 26 da koci, Pape Thiaw ya sanar ranar Talata.
Thiaw ya sanar da manema labarai cewar Mane, mai shekara 33, wanda ya buga wa Senegal karawa 111 ya sha suka da cewar bai yi kokari ba a fafatawa da suka tashi canjaras da Sudan, amma suka doke Togo a karawar neman shiga gasar kofin duniya a cikin watan Maris.
Koci, Thiaw ya gayyaci Mamadou Lamine Camara a karon farko cikin tawagar, wanda ya taka rawar gani a ƙungiyarsa, Renaissance Berkane ta Morocco, wadda ta lashe African Confederation Cup ranar Lahadi.
Ɗan wasan Chelsea, Nicolas Jackson da Iliman Ndiaye daga Everton, waɗanda ba su buga wasan cikin watan Maris ba, za su yi wa Senegal wasan biyu na sada zumunta.
Senegal za ta fara wasa da tawagar Ireland a Dublin ranar 6 ga watan Yuni, sannan ta kece raini da Ingila a Nottingham ranar 10 ga watan Yuni.
Tawagar Senegal da za ta buga wasan sada zumunta biyu:
Masu tsare raga: Mory Diaw (Rodez), Yevhann Diouf (Stade Reims), Edouard Mendy (Al Ahli)
Masu tsare baya: Abdou Diallo (Al Arabi), El Hadj Malick Diouf (Slavia Prague), Ismail Jakobs (Galatasaray), Kalidou Koulibaly (Al Hilal), Antoine Mendy (Nice), Moussa Niakhate (Olympique Lyonnais), Abdoulaye Seck (Maccabi Haifa)
Masu wasa daga tsakiya: Lamine Camara (Monaco), Mamadou Lamine Camara (Renaissance Berkane), Pathe Ciss (Rayo Vallecano), Habib Diarra (Racing Strasbourg), Krepin Diatta (Monaco), Idrissa Gana Gueye (Everton), Pape Gueye (Villarreal), Pape Matar Sarr (Tottenham Hotspur)
Masu cin ƙwallye: Boulaye Dia (Lazio), Idrissa Gueye (Metz), Nicolas Jackson (Chelsea), Cherif Ndiaye (Red Star Belgrade), Iliman Ndiaye (Everton), Cheikh Sabaly (Metz), Ismaila Sarr (Crystal Palace), Abdallah Sima (Stade Brest).