Yau za a kammala Bundesliga a Jamus, Bundesliga
Za a kammala wasannin mako na 34 a Bundesliga ranar Asabar, inda za a yi fafata tara a kuma lokaci ɗaya.
Tuni Bayern Munich ta lashe kofin bana, kuma na 33 jimilla.
Yanzu ana neman huɗun da za su wakilci kasar a Champions League a baɗi da wadda za ta Europa da kuma wadda za ta buga Conference League da waɗanda za su yi ban ƙwana da kakar bana.
Tun a mako na 27 Bayern Munich ta samu gurbin shiga gasar zakarun Turai ta baɗi, yayin da Bayern Leverkusen ta samu nata tikitin a mako na 29.
Waɗan da suka yi ban kwana da Bundesliga a kakar nan sun haɗa da Holstein da Bochum tun a karawar mako na 33.
Wasannin makon karshe a Bundesliga ranar Asabar:
- Augsburg da Union Berlin
- Borussia Dortmund da Holstein Kiel
- Borussia M'gladbach versus Wolfsburg
- Freiburg da Eintracht Frankfurt
- Heidenheim da Werder Bremen
- Hoffenheim da Bayern Munich
- Mainz 05 da Bayer Leverkusen
- RB Leipzig da Stuttgart
- St. Pauli da Bochum