Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni 17-23, 2025

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku sharhi da bayanai kan labarain wasanni a faɗin duniya daga ranar Asabar 17 zuwa 23 ga watan Mayun 2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Everton ta yi ban kwana da Goodison Park, Premier League

    Magoya bayan Everton sun yi ban kwana da filin Goodison Park, bayan shekara 133 suna taka leda a ciki.

    Ƙungiyar ta Mersyside za ta koma buga tamaula a Bramley-Moore Dock a kaka mai zuwa.

    To amma Everton za ta bai wa matan ƙungiyar filin Goodison Park, domin ci gaba da wasanni a ciki, amma za ta rage yawan kujerun zaman ƴan kallo.

  2. Wasannin da aka buga a Premier League a karshen mako, Premier League

    Ranar Juma'a, 16 ga watan Mayu

    • Aston Villa 2-0 Tottenham
    • Chelsea 1-0 Manchester United

    Ranar Lahadi, 18 ga watan Mayu

    • Everton 2-0 Southampton
    • West Ham 1-2 Nottingham Forest
    • Brentford 2-3Fulham
    • Leicester 2-0 Ipswich
    • Arsenal 1-0 Newcastle United
  3. Howe na fatan Newcastle za ta samu gurbin Champions League, Newcatle United

    Kociyan Newcastle United, Eddie Howe ya ce yana sa ran zai samu gurbin Champions League.

    Ranar Lahadi Arsenal ta ci Newcastle 1-0 a wasan mako na 37 a Premier League a Emirates.

    Hakan ya sa Gunners ta ci gaba da zama ta biyu a teburin babbar gasar tamaula ta Ingila da maki 71, sannan za ta wakilci Ingila a gasar zakarun Turai a baɗi.

    Kenan Liverpool, wadda ta lashe kofin Premier League na bana na 20 jimilla da Arsenal, sune suka samu tikitin shiga Champions League daga Ingila, kenan saura gurbi uku ake nema nan gaba.

    Kawo yanzu Newcastle tana ta uku da maki 66, iri ɗaya da na Chelsea ta huɗu da Aston Villa ta biyar, Manchester City mai ƙwantan wasa tana da maki 65 a mataki na shida da kuma Nottingham Forest ta bakwai da maki iri ɗaya da na City.

    Ranar Lahadi za a karkare wasannin kakar bana.

  4. Messi ya bukaci ƴan wasan Inter Miami su kara sa ƙwazo, Inter Miami

    Lionel Messi ya bukaci ƴan wasan Inter Miami su kara sa ƙwazo, saboda rashin kokarin da suke a kakar nan, bayan da Orlando City ta je ta doke ta da ci 3-0 a gasar MLS.

    Rashin nasara ta uku kenan a wasa bakwai a dukkan fafatawa, hakan ya sa ƙungiyar ta yi kasa zuwa ta shida a teburin Eastern Conference.

    Messi, ƙyaftin ɗin Argentina, mai shekara 37, wanda ya lashe Ballon d'Or takwas bai yi kokari ba sosai, wanda ƙwallo biyu kacal ya buga da ya nufi raga a gabaki ɗayan wasan.

  5. Nan muka kawo karshen shirin

    Da fatan kun ji dadin kasancewa da shirin na sharhi da bayanai kan labarain wasanni, kuma nan zan yi ban kwana da ku, zan ɗora ranar Litinin.

    Sunana Mohammed Abdu nake cewa mu kwana lafiya.

  6. Jamie Vardy ya yi ban kwana da Leicester City, Premier League

    Jarmie Vardy ya yi ban kwana da Leicester City, bayan kaka 13 da buga mata wasa 500 da cin ƙwallo 200.

  7. Wasannin mako na 38 a Premier League ranar 25 ga watan Mayu

    • Bournemouth da Leicester City
    • Fulham da Manchester City
    • Ipswich Town da West Ham United
    • Liverpool da Crystal Palace
    • Manchester United da Aston Villa
    • Newcastle United da Everton
    • Nottingham Forest da Chelsea
    • Southampton da Arsenal
    • Tottenham da Brighton & Hove Albion
    • Wolverhampton Wanderers da Brentford
  8. Alcaraz ya lashe Italian Open a karon farko a tarihi, Ƙwallon tennis

    Carlos Alcaraz ya lashe Italian Open, bayan caskara Jannik Sinner da 7-6 6-1 ranar Lahadi.

    An kuma kawo karshen lashe wasa 26 a jere da Sinner yake lashewa

    Sai dai Sinner ya yi fatan ɗaukar Italian Open na ban, domin ya zama na farko daga Italiya da ya lashe kofin tun bayan Adriano Panatta a 1976.

    Sinner, wanda ya koma buga tennis bayan wata uku da aka dakatar da shi, sakamakon samunsa da laifin shan abubuwan kara kuzari, ya sha kashi a hannun ɗan Sifaniya cikin minti 33.

  9. Bayern Munich za ta mamaye kakar baɗi - Kane, Bundesliga

    Ƙyaftin ɗin tawagar Ingila, Harry Kane ya ce yanzu Bayern Munich ta fara ganin ƙwazonsa sai ma kakar baɗi.

    Kane ya lashe Bundesliga a bana, kofin farko da ya ci a tarihin rayuwarsa ta tamaula.

    Mai shekara 31, yana da ƙunshin yarjejeniya da Bayern Munich zuwa karshen kakar 2027, wanda ya koma Jamus da taka leda kan £86.4million daga Tottenham a Agustan 2023.

    Kane ya ci ƙwallo 38 a kakar nan, yayin da Bayern Munich ta caskara Hoffenheim 4-0 ranar Asabar a wasan karshe a Bundesliga.

  10. Matakin da Arteta ya kare a teburin Premier a kaka shida a Arsenal, Arsenal 1-0 Newcastle

    Shin Arsenal na ci gaba ne karkashin Mikel Arteta ko kuma koma baya take yi?

    Ga jerin sakamakon kaka shida da Arteta ya ja ragamar Arsenal

    2019-20 - Mataki na takwas

    2020-21 - Mataki na takwas

    2021-22 - Mataki na biyar

    2022-23 - Mataki na biyu

    2023-24 - Mataki na biyu

    2024-25 - Mataki na biyu

  11. Yadda teburin Premier League yake, Arsenal 1-0 Newcastle

    Yanzu dai yaƙi ya rage tsakanin Newcastle da Chelsea da Aston Villa da Manchester City da Nottingham Forest a neman sauran gurbin shiga gasar zakarun Turai a baɗi.

    Uku ne daga biyar daga cikinsu za su wakilci Ingila a Champions League a kaka mai zuwa.

    A wasan karshe ranar Lahadi, Newcastle za ta kara da Everton a St James Park, Nottingham Forest da Chelsea za su kece raini a tsakaninsu a ranar.

  12. An tashi wasan, Arsenal 1-0 Newcastle

    Wasa ya kare

    Arsenal ta samu gurbin Champions League da za a buga a baɗi.

  13. YELLOW CARD - Katin gargaɗi ga ɗan wasan Newcastle, Arsenal 1-0 Newcastle

    Alkalin wasa ya bayar da katin gargaɗi, watakila ga Jakub Kiwior.

  14. Arsenal 1-0 Newcastle

    Mai tsaron raga David Raya na Arsenal ya kama ƙwallo.

  15. , Arsenal 1 - 0 Newcastle United

    Yanzu haka Declan Rice ya ci ƙwallo da yawa a Arsenal 16 a wasa 102, fiye da 15 a karawa 245 a West Ham United.

  16. A karon farko Kane ya lashe kofi na Bundesliga

  17. Gauff na fatan lashe French Open karo na uku

    Wadda take ta uku a ƙwallon tennis a duniya, Coco Gauff na fatan lashe French Open karo na uku.

    Ƴar wasan ta ci karo da koma baya karo biyu a jere da aka doke ta a wasan karshe - na farko Italian Open a hannun Jasmine Paolini ranar Asabar da kuma a Madrid Open a hannun Aryna Sabalenka.

    Za a fara French Open daga 25 ga watan Mayu.

  18. , Arsenal 0-0 Newcastle

    Wannan shi ne karon farko da Arsenal ke wasan Premier League tun Oktoba ba tare da ko dai Gabriel Magalhaes ko kuma William Saliba ba a cikin fili.

  19. GOAL - GOAL - Arsenal 1-0 Newcastle, Declan Rice

    Ƙwallo mai ƙyau da Declan Rice ya ci daga yadi na 20, bayan da ya samu tamaula daga Martin Odegaard.

  20. Arsenal ko Newcastle wa zai kare a mataki na biyu a Premier?, Premier League

    Arsenal za ta kece raini da Newcastle United a wasan mako na 37 a Premier League a Emirates ranar Lahadi.

    Arsenal tana ta biyu a teburin Premier League da tazarar maki biyu tsakani da Newcastle United ta ukun teburu.

    Wannan shi ne karo na huɗu da za su kece raini a tsakaninsu a bana, inda Newcastle ta yi wa Gunners gida da waje a League Cup, sannan ta doke ta a Premier League.

    Newcastle ta ɗauki Carabao Cup a kakar nan.

    Wasa uku da aka buga tsakanin Arsenal da Newcastle United a 2024/2025

    English League Cup ranar Laraba 5 ga watan Fabrairun 2025

    • Newcastle 2 - 0 Arsenal

    English League Cup ranar Talata 7 ga watan Janairun 2025

    • Arsenal 0 - 2 Newcastle

    Premier League ranar Asabar 2 ga watan Nuwambar 2024

    • Newcastle 1 - 0 Arsenal