Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni 17-23, 2025

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku sharhi da bayanai kan labarain wasanni a faɗin duniya daga ranar Asabar 17 zuwa 23 ga watan Mayun 2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Babu batun ƴan shidan farko a yanzu a Premier League

    Kociyan Arsenal, Mikel Arteta ya ce yanzu ba batun manyan ƙungiya shida a Premier League.

    Gunners za ta karɓi bakuncin Newcastle a wasanta na karshe a bana a Emirates ranar Lahadi, kuma dukkansu suna neman gurbin Champions League, Arsenal tana ta biyu da tazarar maki biyu tsakani da ƙungiyar St James Park.

    Ƙungiya biyar ake sa ran za ta wakilci Ingila a baɗi a Champions League, sai dai ana sa ran su zama shida, bayan kammala wasan karshe a Europa League tsakanin Tottenham da Manchester United a makon gobe.

    Chelsea da Aston Villa da Manchester City, kowacce na neman gurbin gasar zakarun Turai.

    Arteta ya ce gasar Premier ta kara tsauri, kuma yadda suka ga sauye-sauye a kakar nan, lallai za a yi tata ɓurza a baɗi sai mai rabo.

  2. Bradley ya tsawaita yarjejeniyarsa a Liverpool

    Ɗan ƙwallon Liverpool, Conor Bradley ya saka hannu kan ƙwantiragin kaka huɗu da zai ci gaba da taka leda a Anfield zuwa karshen kakar 2029.

    Ɗan wasan tawagar Ireland ta Arewa, mai shekara 21 na taka rawar gani karkashin Arne Slot, musamman a Premier League da kuma rawar da ya taka a Champions League da Liverpool ta ci Real Madrid a cikin watan Nuwamba.

    Bradley ya buga wasa 27 a bana a Liverpool a dukkan fafatawa, koda yake jinya ta hana shi buga karawa da yawa.

    Amma ana sa ran zai buga wasanni da yawa a baɗi, wanda ake sa ran zai maye gurbin Trent Alexander-Arnold,

  3. Bai kamata Liverpool su yi wa Arnond ihu ba

    Dan wasan Liverpool, Mohamed Salah ya ce bai kamata magoya bayan ƙungiyar su yi wa Trent Alexander-Arnold ihu ba, wanda ya zabi gwada sa'a a wani wajen bayan shekara 20 a Anfield.

    Magoya bayan Liverpool sun yi wa matashin ihu a gasar Premier League da aka tashi 2-2 da Arsenal.

    Salah, wanda shi ne kan gaba a yawan cin ƙwallaye a Premier League mai 28 a raga ya ce Arnold ya cancanci bikin girmamawa, bayan rawar da ya taka a ƙungiyar.

    Alexander-Arnold, wanda aka haifa a Liverpool ya fara daga makarantar ƙungiyar har ta kai ya kai matakin buga wa babbar ƙungiya, wanda ya lashe Premier League biyu da Champions League da kuma Club World Cup da sauran kofuna a Liverpool.

    Ana cewa Arnorl zai koma taka leda a Real Madrid a kakar baɗi.

  4. An bai wa Crystal Palace FA Cup na bana, Crystal Palace 1-0 Man City

  5. , Crystal Palace 1-0 Man City

    Ƴan wasan Crystal Palace sun je karbar kofin FA - an bai wa Joel Ward da kuma Marc Guehi tare da yan wasa sun ɗaga kofin a filin Wembley.

  6. , Crystal Palace 1-0 Man City

    Ƴan wasan Manchester City sun je wajen zaman manyan baƙi, domin su karɓi ƙyautar zama na biyu a FA Cup na kakar nan.

    Kusan magoya bayan City sun bar filin wasa na Wembley. Wannan shi ne karon farko da City ta kare kakar tamaula ba tare da lshe kofi ba tun bayan 2016/17.

    Yanzu abin ji shi ne ko City za ta samu gurbin Champions League? saura wasa bibiyu a kare gasar Premier League.

  7. , Crystal Palace 1-0 Man City

    Oliver Glasner bai yi gudu cikin fili ba wai don sun lashe FA Cup a karon farko, abin da ya yi shi ne ya je wajen zaman Manchester City ya gaisa da jami'ai da ƴan wasa, sannan ya shiga fili, domin ya gaisa da Pep Guardiola.

  8. Manchester City ta kare kakar bana ba tare da lashe kofi ba, Crystal Palace 1-0 Man City

    Manchester City ta kare kakar bana ba tare da lashe kofi ba.

    City wadda ita take rike da Premier League ta yi rashin kokarin da ta kai Liverpool ce ta lashe na bana.

    Haka kuma ƙungiyar Etihad ta fice daga gasar Champions League a hannun Real Madrid a wasan cike gurbi, sannan a Carabao Cup Tottenham ta yi waje da ita.

    Yanzu kuma Palace ta yi nasara ɗaukar FA Cup a karon farko a tarhinta.

  9. Palace ta lashe FA Cup a karon farko a tarihi, Crystal Palace 1-0 Man City

    A karon farko Crystal Palace ta lashe FA Cup, bayan cin Manchester City 1-0 ranar Asabar a Wembley.

    Eberechi Eze ne ya ci ƙwallon da ya bai wa Palace damar lashe FA Cup a karon farko a tarihi.

  10. Napoli na fatan lashe Serie A na bana, bayan samun gurbin Champions League, Serie A

    Tuni dai Napoli ta samu gurbin wakiltar Italiya a gasar Champions League a baɗi, amma tana fatan lashe Seie A na kakar nan.

    Ranar Lahadi Napoli za ta je gidan Parma a karawar mako na 37, kuma maki ɗaya ya rage tsakanin Napoli da mai jan ragam da Inter Milan ta biyun teburi.

    A makon jiya Napoli ta tashi 2-2 a gidan Genoa, wadda take ta 13 teburi, hakan ya bai wa Inter damar rage tazarar makin da yake tsakaninsu.

    Watakila a buga karawar neman zakaran bana tsakanin Napoli da Inter idan sunj kammala kakar bana da maki irri ɗaya da juna.

    To sai dai damar cinye Serie A na kakar nan yana hannun Napoli da zarar ta yi nasara a sauran wasa biyun da ya rage mata, wadda za ta je gidan Parma, sannan ta karkare a gida da Cagliari.

  11. Har yanzu da jan aiki a gaban Newcastle - Howe, Newcastle United

    Eddie Howe ya ce Newcastle United tana jan aiki a gabanta, idan har tana son ake saka ta cikin manyan ƙungiyoyin Ingila.

    Ƙungiyar ta lashe Carabao Cup a kakar nan - karon farko da ta ɗauki kofin gasar Ingila tun bayan shekara 70, kuma tana cikin waɗan da ake takarar gurbin Champions League da ita, wadda ke fatan karewa a mataki na biyu a teburi

    Newcastle ta yi nasara a kan Arsenal karo uku a bana, za kuma su fuskanci juna ranar Lahadi a gasar Premier League, Arsenal ce ta biyun teburi da maki 68, sai Newcastle ta uku da maki 66.

    Newcastle ta lashe Carabao Cup a kan Liverpool sannan ta yi nasara gida da waje a kan Manchester United, hakan ke nuna irin ƙwazon da take yi a bana.

  12. Slot na fatan Liverpool za ta lashe wasa biyun da suka rage

    Kociyan Liverpool, Arne Slot na fatan za su lashen Premier League da ya rage musu, domin su farfaɗo daga koma bayan da suka ci karo a gasar.

    Liverpool, wadda ta lashe Premier League na bana na 20 jimilla ta ziyarci Dubai a makon nan - shi kuwa Slot ya je Ibiza domin yin kwanaki daga cikin bikin cin kofin babbar gasar tamaula ta Ingila ta bana.

    Tun bayan da aka tabbatar da Liverpool ta lashe kofin kakar nan, ta yi rashin nasara a hannun Chelsea, sanna ta tashi 22-2 da Arsenal, wadda ita ce ta fara zura biyu a raga daga baya aka farke su.

    Wasannin da suka rage a gaban Liverpool a bana:

    • Premier League Litinin 19 ga watan Mayu, Brighton da Liverpool
    • Premier League Lahadi 25 ga watan Mayu Liverpool da Crystal Palace
  13. Leverkusen ta yi wasanni a waje ba tare da an doke ta ba a Bundesliga a bana

    Bayer Leverkusen ta je ta tashi 2-2 a gidan Mainz 05 a wasan karshe a gasar Bundesliga ranar Asabar.

    Kenan kociya, Xabi Alonso ya ja ragamar ƙungiyar wasa biyu a jere ba tare da rashin nasara ba a karawar waje a Bundesliga- wanda a bara ba a ci Leverkusen ba a dukkan fafatawa a karawar gida.

    Alonso zai bar Bundesliga kenan tunda an kammala kakar bana, ana cewa Real Madrid zai koma domin maye gurbin Carlo Ancelotti, wanda ya amince da aikin jan ragamar tawagar Brazil.

  14. Emery zai duba makomar Martinez a Aston Villa

    Kociyan Aston Villa, Unai Emery ya ce zai duba makomar mai tsaron raga, Emiliano Martinez, bayan da golan ya fashe da kuka, bayan cin Tottenham.

    Mai shekara 32 ya sha kuka a kokarin da ƙungiyar ke yi na neman gurbin Champions League, bayan nasara a kan Tottenham da ci 2-0 ranar Juma'a a gasar Premier League.

    Martinez ya buga wa Villa wasa 211 tun bayan da ya koma ƙungiyar daga Arsenal a 2020.

    Aston Villa ta koma cikin ƴan biyar ɗin farko a teburin Premier League, sakamakon doke Tottenham, sai dai Manchester City tana da ƙwantai, kenan Villa na fatan doke Manchester United a wasan karshe, sannan ta yi fatan wasu sakamakon ya ba ta damar buga Champions League a baɗi.

  15. MISSED PENALTY - Omar Marmoush ya ɓarar da fenariti, Crystal Palace 1-0 Man City

    Omar Marmoush ya zubar da fenariti, bayan da mai tsaron raga, Dean Henderson ya tare ƙwallon da aka buga masa.

    City ta samu bugun daga kai sai mai tsare raga, bayan da Tyrick Mitchell ya yi wa Bernardo Silva keta.

  16. GOAL Crystal Palace 1-0 Man City, Eberechi Eze

  17. Ƴan Palace da na City da za su fara FA Cup, FA Cup

    Kociyan Crystal Palace, Oliver Glasner ya yi canji biyu daga ƴan wasan da suka doke Tottenham a Premier League.

    Palace ta yi murna da ɗan wasan tawagar Ingila, Adam Wharton, ya koma taka leda, wanda ya maye gurbin Will Hughes.

    Haka shima Daichi Kamada zai fara wasa a madadin Jefferson Lerma.

    Crystal Palace 11: Henderson, Munoz, Richards, Lacroix, Guehi, Mitchell, Kamada, Wharton, Sarr, Eze, Mateta.

    Mai horar da Manchester City zai fara karawar da karfinsa, domin kofin da ya rage masa ya ɗauka kenan a kakar nan.

    Ya yi canji biyar, inda mai tsaron raga, Stefan Ortega zai buga wasan karshe karo na uku FA Cup, yayin da za a fara karawar da Nico O'Reilly, Jeremy Doku, Savinho da kuma Omar Marmoush.

    An ajiye Ederson da Phil Foden a benci, yayin da Rico Lewis, Mateo Kovacic da James McAtee ba za su yi wasan ba.

    Man City 11: Ortega, Akanji, Gvardiol, Dias, O'Reilly, Silva, De Bruyne, Savinho, Doku, Marmoush, Haaland.

  18. Labaran da jaridu ke wallafawa kan cinikin ƴan wasa

    Aston Villa ka iya sayo dan wasan Sifaniya Ferran Torres mai shekara 25, da ke taka leda a Barcelona, zuwa kulub din Premier League kan kudi fam miliyan 4, idan an bude kasuwar saye da saida 'yan wasa a kaka mai zuwa. (Birmingham Mail)

    Southampton na son dan wasan baya na Sturm Graz Max Johnston, 21, kan kudi fam miliyan 3. (Sky Sports)

    Wrexham na duba yiwuwar dauko dan wasan tsakiya na Nottingham Forest, Lewis O'Brien mai shekara 26- wanda a yanzu ya ke zaman aro a Swansea City - bayan likkafarsu ta daga a Championship. (Football League World)

  19. Alcaraz da Sinner za su buga wasan karshe a Italian Open

    Jannik Sinner ya doke Tommy Paul, zai kuma fuskanci Carlos Alcaraz a wasan karshe a Italian Open.

    A makon nan Sinner ya koma buga ƙwallon tennis tun bayan Australian Open, wanda aka dakatar wata uku kan zargin shan abubuwan kara kuzarain wasanni.

    Sinner ya kai zagayen karshe ne da cin 1-6 6-0 6-3 kuma wasa na 26 da ya yi nasara a jere kenan.

    Kenan Sinner zai fuskanci Alcaraz a karon farko a bana. Rabon da su fafata a tsakaninsu tun cikin Oktoban bara a China Open, inda ɗan kasar Spaniya ya zama zakara.

    Sinner ya yi rashin nasara a dukkan fafatawa ukun da ya yi da Alcaraz a kaka biyu baya.