An ɗaure mutum biyar da suka yi wa Vinicius Jr kalaman wariya, Real Madrid
An yanke hukuncin ɗauri ga mutum biyar da aka samu da laifin yi wa Vinicius Jr kalaman wariya lokacin gasar La Liga ta Sifaniya.
A cikin watan Disambar 2022 aka ci zarafin ɗan wasan tawagar Brazil a wasan da Real Madrid ta doke Real Valladolid 2-0 a lokacin da aka sauya ɗan wasan a filin wasa na Jose Zorilla.
Kotun da take Valladolid ta yanke hukuncin shekara ɗaya ga kowanne mutum da cin tara da ta kai Yuro 1,080 zuwa 1,620.
To sai dai an jingine hukuncin ɗaurin da cewr har idan ba a sake samunsu da laifi irin wanda suka aikata, kuma ba za su sake shiga kallon tamaula a sitadiya shekara ukun.