Nottingham Forest na fatan samun gurbin Champions League, Premier League
Nottingham Forest ta samu damar kammala kakar bana cikin ƴan biyar ɗin farko a Premier League, sakamakon da ta je ta doke West Ham United 2-1 a wasan mako na 37 ranar Lahadi.
Da wannan sakamakon Forest tana mataki na bakwai da maki 65, iri ɗaya da na Manchester City ta shida, mai ƙwantan wasa, wadda Crystal Palace ta ci 1-0 ta lashe FA Cup ranar Asabar a Wembley.
Forest za ta karɓi bakuncin Chelsea a wasan karshe ranar Lahadi, wadda za ta yi kokarin cin wasan daga nan ta yi fatan wasu sakamakon wasannin su ba ta damar shiga ƴan biyar ɗin farko a Premier League a bana.
Chelsea tana mataki na huɗu da maki 66, iri ɗaya da na Aston Villa ta biyar.