Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Arbeloa zai bar aikin kociyan Real Madrid a karshen kakar bana

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga 17 zuwa 24 ga watan Mayun 2026.

Taƙaitattu

  • Ingila za ta buga gasar kofin duniya ba tare da Foden da Palmer da Arnold
  • Burin Ronaldo ya ci ya lashe babban kofin Saudiyya a bana
  • Manchester United ta tabbatarwa da Carrick mukamin kociyanta
  • Guardiolazai bar Manchester City bayan sama da shekara 10 a Etihad
  • Mourinho na son Rashford a Madrid, Everton na harin Osula
  • Arbeloa zai bar Real Madrid a karshen kakar nan
  • Brazil ta saka Neymar cikin ƴan wasan da za su buga mata kofin duniya
  • Ku shiga zaurenmu na BBC Hausa WhatsApp
  • Za ku iya tafka muhara a shafnmu na sada zumunta a BBC Hausa Facebook

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Masu biyan haraji za su biya karin kuɗi idan West Ham ta faɗi daga Premier League, West Ham

    Masu biyan haraji a London na iya biyan ƙarin fam miliyan 2.5 idan West Ham United ta faɗi daga Premier League a wannan kakar, saboda yarjejeniyar hayan da ƙungiyar ta kulla kan London Stadium.

    Hammers tana matsayi na 18 a teburin gasar bana kuma wasa ɗaya ya rage a kammala kakar bana, kuma za ta koma buga Championship da zarar Tottenham ta doke Chelsea a Stamford Bridge ranar Talata.

    A karkashin yarjejeniyar haya ta shekaru 99, West Ham za ta biya Greater London Authority kusan rabin kuɗin hayar shekara-shekara, wanda a yanzu ya kai fam miliyan 4.4 idan ta fice daga gasar.

    Masu biyan haraji a London, waɗanda a yanzu suke taimakawa wajen biyan kuɗaɗen gudanar da filin wasa kamar tsaro da masu kula da tsaro, sune kuma za su cike giɓin kuɗin.

    Ana kuma sa ran kuɗin shiga daga harkokin kasuwanci a London Stadium za su ragu idan West Ham ta koma Championship, yayin da kuɗin kula da tsaro a wasannin gida guda 23 zai fi yawa idan aka kwatanta da wasannin gida 19 a gasar Premier League.

  2. Carvajal zai bar Real Madrid bayan shekara 23 a ƙungiyar, Real Madrid

    Ƙyaftin ɗin Real Madrid, Dani Carvajal, zai bar ƙungiyar a ƙarshen wannan kakar, bayan da ya shafe shekara 23 a matakai biyu daban-daban a filin wasa na Santiago Bernabéu Stadium.

    Carvajal mai shekara 34, wanda ya buga wa Real Madrid wasa 450 tare da cin ƙwallaye 14, kwantiraginsa zai ƙare a ƙarshen watan Yuni.

    Ɗan wasan haifaffen Madrid ɗin ana kallonsa a matsayin gwarzon ƙungiyar kuma ɗaya daga cikin ƴan wasa mafi yawan lashe kofuna a tarihi, inda yake da 27 jimilla.

    Ya shiga makarantar horas da matasan Real Madrid daga 2002, sannan ya fara bugawa babbar ƙungiyar tamaula daga 2013, bayan da ya yi wasannin aro a kaka ɗaya a Bayer Leverkusen daga baya ya koma Madrid da murza leda.

    Carvajal ya lashe kofin Champions League sau shida — ɗaya daga cikin ƴan wasa biyar kacal da suka taɓa yin hakan — kuma shi ne kaɗai ɗan wasan da ya fara taka leda a dukkan wasan karshe shida da ya ci kofuna.

    A Real Madrid ya lashe La Liga huɗu da Copa del Rey biyu da Fifa Club World Cup shida da UEFA Super Cup guda biyar da kuma Spanish Super Cup huɗu.

    Ya kasance jigo a tawagar ƙasar Sifaniya tun daga 2014, inda ya buga wasa 51 tare da taimaka mata ta lashe UEFA Nations League a 2023 da kuma UEFA Euro 2024.

  3. Ƴanwasan da za su buga gasar kofin duniya ta ƙarshe a 2026, Gasar kofin duniya

    Daf ake a fara gasar cin kofin duniya da aka sauya mata fasali da tazawa 48 za ta kece raini a Amurka da Canada da kuma Mexico.

    Kawo yanzu an samnu dukkan kasashen da za su buga wasannin, har da waɗanda a karon farko za su buga babbar gasar tamaula ta duniya a tarihi.

    Wannan gasar za a yi tata ɓurza ganin tawagogin suna da yawa, an kara yawan wasanni da filaye da jami'an da za su gudanar da gasar ta 2026.

    Argentina ce mai rike da kofin da ta ɗauka a 2022 a Qatar, kenan Messi zai yi fatan kare kofin daga nan ya rataye takalmansa.

    Wasannin bana za a samu matasan da za su nuna kansu da kuma waɗanda tsuka yi tsufan da wannan ce gasar da za su halarta ta karshe. Latsa nan domin ci gaba da karanta labarin.

  4. Real Madrid ta je ta doke Sevilla a La Liga, Real Madrid

    Kylian Mbappé ya nuna bajinta a dawowarsa cikin ƴan wasan farko na Real Madrid, inda ya bai wa Vinicius Junior ƙwallon da ya ci Sevilla a filin wasa na Ramón Sánchez-Pizjuán ranar Lahadi.

    Bayan ƴan kwanaki da magoya baya Real Madrid suka yi masa ihu a wasan da suka yi nasara a kan Real Oviedo a gida, dan wasan tawagar Faransa ya buga karawar ba tare da wani matsi ba ko matsala.

    Wannan sakamakon ya sa Real Madrid ta ci gaba da zama a matsayi na biyu a teburin La Liga, yayin da Sevilla ta sauka zuwa matsayi na 13 kafin fafatawar karshen mako a kakar wasa.

  5. Mourinho ya kammala kakar bana ba tare da rashin nasara ba a Benfica., Benfica

    Jose Mourinho ya kammala kakar gasar lig ta bana ba tare da rashin nasara ba a Benfica, amma duk da haka ya kare a matsayi na uku a teburin babbar gasar ƙwallon ƙafa ta Portugal.

    Benfica ta doke Estoril da ci 3-1 a wasansu na ƙarshe a kakar nan, wanda ya tabbatar da cewa ta kammala Primeira Liga ba tare da rashin nasara ba, wadda ta ci wasa 23 tda kunnen doki 11.

    Sai dai ta kammala kakar da maki 80 — maki takwas a bayan wadda ta lashe kofin, Porto, sannan maki biyu tsakani da Sporting mai matsayi na biyu, sannan Benfica ta uku

    Nasarar da suka samu a kan Estoril za ta iya wasan ƙarshe da Mourinho ya jagoranci Benfica, saboda yana matakin ƙarshe na tattaunawa domin zama sabon kocin Real Madrid, shekaru 13 bayan wa’adinsa na farko a Bernabeu.

    Kociyan mai shekara 63 ya koma Benfica a watan Satumban bara kan kwantiragin shekaru biyu, amma shugaban Real Madrid, Florentino Perez na son ɗaukarsa aiki, bayan da suka fuskanci kalubale a bana

    Wannan ba shi ne karon farko da Benfica ta yi kakar lig ba tare da shan kashi ba, amma ta kasa lashe kofin gasar ba.

    A kakar 1977-78, Porto ta yi kunnen doki ƙasa da Benfica da wasanni biyu kuma ta lashe kofin lig saboda bambancin ƙwallaye.

    Benfica ta Mourinho yanzu ta shiga jerin ƙungiyoyin Turai kaɗan da suka yi kakar lig ba tare da shan kashi ba amma suka kasa lashe gasar, tare da FC Sheriff ta Moldova a kakar 2024-25 da kuma Red Star Belgrade ta Serbia a kakar 2007-08.

  6. Har yanzu Ronaldo na jiran ranar da zai fara lashe kofi a Al-Nassr

    Har yanzu Cristiano Ronaldo bai samu damar lashe babban kofi ba a Al-Nassr, bayan da suka mamakin rashin nasara 1-0 a gida a hannun Gamba Osaka a wasan ƙarshe a AFC Champions League Two.

    A gaban magoya baya 26,000 a filin wasa na King Saud University Stadium, tun farko ƙungiyar Saudiyya ta Al-Nassr ce aka fi sa ran za ta lashe gasar ƙwallon ƙafa ta mataki na biyu a nahiyar Asiya — wadda take daidai da Europa League ta Turai.

    Sai dai Deniz Hummet ya ci wa baƙi kwallo a Riyadh ranar Asabar.

    Wannan sabon koma baya ne ga Ronaldo bayan da a kwanaki huɗu baya da golan Al-Nassr Bento ya ci daf da tashi a ƙarshen wasa, wanda ya sa tauraron Portugal ɗin ya ci gaba da jiran babban kofi tun bayan komawarsa Al-Nassr a watan Janairun 2023.

    Wannan sakamakon ya bai wa abokan hamayyarsu na gasar Saudi Pro League, Al-Hilal, damar yin kunnen doki 1-1 tare da ci gaba da kasancewa maki biyu kacal a bayan Al-Nassr mai jagoranci yayin da wasa ɗaya ya rage a gasar.

    Sai dai ƙungiyar Ronaldo za ta zama zakarun Saudiyya karo na 11 — kuma na farko tun 2019 — idan ta doke Damac a gida ranar Alhamis.

    Al-Hilal, wadda ta lashe gasar sau 21, za ta buga wasan ƙarshe a kakar nan a gidan Al-Fayha a lokaci guda ranar Alhamis.

  7. , Daga Jaridu

    Juventus na shirin sake ruɓanya himmarta wajen ganin ta ɗauko ɗan wasa Bernardo Silva, da ke shirin barin Manchester City a kakar wasannin nan, wajen ganin sun yi nasarar kan Atletico Madrid da Barcelona wajen siyen ɗan wasan. (Corriere dello Sport - in Italian)

    Ana sa ran daraktan wasanni Bercelona Deco zai halarci gasar wasan ƙarshe na gasar F A a Ingila, don kallon yadda ɗan wasan Chelsea Joao Pedro zai taka leda, duk da cewar Chelsea ɗin ba ta son siyar da ɗan wasan. (Mail)

    Coventry City na son ɗauko ɗan wasan Netherlands Georginio Wijnaldum, da kwantaraginsa zai ƙare da Al-Ettifaq, a kakar wasannin nan. (Football Insider)

    Everton na harin ɗan wasan Burnley loum Tchaouna, da ke cikin tawagar ƴan wasan Faransa ƴan shekaru ƙasa da 21. (Football Insider)

  8. , Daga Jarida

    SC Freiburg na son siyen ɗan wasan gaban Leeds Unite Wilfried Gnonto, yayin da Leeds United ɗin ta ke shirin siyar da ɗan wasan, ko kuma ta bayar da shi aro amma da alƙawarin siyensa nan gaba. (Sky Sports Germany)

    Ana danganta mai tsaron bayan Italiya Alessandro Bastoni da Barcelona, sai dai ya na son ci gaba da zama a Inter Milan, idan har komawar ta sa zuwa ƙungiyar ta Spaniya ba ta tabbata ba. (Gazzetta dello Sport - in Italian)

    Juventus na iya duba yiwuwar baiwa ɗan wasan Brasil Douglas Luiz, da ke buga wasa a matsayin ɗan wasan aro a Aston Villa, damar burge mai horar da ƴan wasan ƙungiyar ko kuma ya siyar da shi. (Gazzetta dello Sport - in Italian)

    Bayern Munich na son ɗan wasan Atalanta Charles De Ketelaere, a wani shirin ko ta kwana idan aka sami rashin tabbacin komawar ɗan wasan Newcastle United Anthony Gardon bai yi nasara ba. (Football Italia)

  9. Napoli ta samu tikitin Champions League da za ta iya sayen Hojlund, Napoli

    Ana sa ran Rasmus Hojlund zai koma Napoli daga Manchester United, bayan da ya taimaka wa ƙungiyar ta Serie A wajen tabbatar da samun gurbin shiga Gasar Zakarun Turai ta Champions Leagueta baɗi, bayan nasarar da suka samu a kan Pisa.

    Ɗan wasan tawagar Denmark ɗin, wanda ya koma Naples buga wasannin aro a watan Agusta, ya bai wa tsohon abokin wasansa na United Scott McTominay ƙwallon farko a minti na 21 da ya zura a raga a filin wasa na Stadio Romeo Anconetani.

    Mai tsaron baya Amir Rrahmani ya ƙara ta biyu, kafin Hojlund ya ci ta uku a karin lokaci, wanda ya kai yawan ƙwallayensa da ya zura a raga a Serie A zuwa 11 a wannan kakar.

    Nasarar ta tabbatar wa Napoli za ta kammala kakar a cikin huɗun farko a Serie A, inda ƙungiyar Antonio Conte ke da tazarar maki biyar a kan Como mai matsayi na biyar yayin da wasa ɗaya ya rage.

    A matsayin wani ɓangare na yarjejeniya tsakanin Man United da ƙungiyar Italiya, yanzu Napoli za ta biya kuɗin sayen Hojlund kan fam miliyan 38.

    Ɗan wasan mai shekara 23 ya ci ƙwallo 15 tare da bayar da takwas aka zura a raga a wasa 43 a dukkan kakarnan, tun bayan komawarsa Italiya, inda ya taɓa taka leda a Atalanta kafin ya koma Man United kan kuɗin fam miliyan 64 a shekarar 2023.

    Napoli za ta tabbata a matsayi na biyu idan ta doke Udinese a wasan ƙarshe a kakarbana.

  10. Fernandes ya yi kan-kan-kan a yawan bayar da ƙwallo a zura a raga a Premier League, Manchester United

    Bruno Fernandes ya yi kan-kan-kan a tarihin bayar da bayar da ƙwallo a zura a raga a kakar gasar Premier League, yayin da Manchester United ta doke Nottingham Forest 3-2 a wasan mako mai na 37 da suka buga ranar Lahadi a Old Trafford.

    Ƙwallon da Fernandes ya bai wa Bryan Mbeumo ya zura a raga da sakamakon ya koma 3-1, hakan ya sa kyaftin ɗin United ya yi kafaɗa da kafaɗa da Thierry Henry da Kevin de Bruyne wajen bayar da ƙwallo a zura a raga karo na 20 a kaka guda — yayin da wasa ɗaya ya rage a kammala wasannin bana.

  11. Barkanmu da shiga fagen labarin wasanni

    Jama'a barkanmu da kasancewa a cikin shirin labarin wasanni da za mu ke sanar da ku wainar da ake toyawa daga wannan ranar zuwa Asabar 18 ga watan Afirilu.

    Sunana Mohammed Abdu za ku iya tafka muhawara a BBC Hausa Facebook ko kuma ku bibiyi labaran da muke wallafawa a BBC Hausa WhatsApp.