Arteta ne na biyu da ya buga Premier ya kuma lashe kofin a matakin kociya, Premier League
A wani rubutu da aka wallafa a Facebook, ƙungiyar Professional Footballers’ Association ta yi ikirarin cewa Mikel Arteta shi ne “dan wasan Premier League na farko da ya taɓa lashe gasar a matsayin koci.”
Sai dai Arteta shi ne dan wasan Premier League na biyu da ya jagoranci ƙungiya ta lashe kofin Premier League a matsayin koci.
Tun bayan kafa gasar Premier League fiye da shekara talatin da suka gabata, akwai kociyoyi guda 13 da suka taba lashe kofin gasar.
Mikel Arteta shi ne mutum na farko da ya ɗauki kofin Premier League a matsayin kocin ƙungiyar da ya taɓa bugawa wasa a cikin gasar.
Sai dai Roberto Mancini ya riga shi yin hakan, lokacin da ya lashe Premier League a kakar 2011/12 a matsayin kocin Manchester City. Kafin nan, Mancini ya taɓa buga wasa a Premier League lokacin da aka aro shi zuwa Leicester City tsakanin watan Janairu da Fabrairu a shekarar 2001.
Kocin da ya fi kowa nasara a tarihin Premier League shi ne Sir Alex Ferguson, wanda ya lashe kofin 13 tare da Manchester United tsakanin kakar 1992/93 zuwa 2012/13. Ferguson ya yi duk rayuwar wasansa ne a Scotland, don haka bai taba buga wasa a Ingila ko Premier League ba.
Pep Guardiola ya lashe Premier League sau shida tare da Manchester City. Ya shafe mafi yawan rayuwar wasansa a Barcelona, kuma bai taba buga wa wata ƙungiyar Ingila tamaula ba.
Jose Mourinho ya lashe Premier League uku tare da Chelsea. Ya yi gajeriyar rayuwar wasansa gaba daya a Portugal.
Arsene Wenger ya lashe Premier League uku tare da Arsenal. Shi ma ya yi wasansa ne a Faransa.
Bayan Arteta da Mancini, sauran kociyoyin da suka taɓa lashe Premier League sun yi hakan sau daya kacal:
- Carlo Ancelotti, Antonio Conte da Claudio Ranieri – duk sun yi wasansu a Italiya
- Manuel Pellegrini – ya yi wasa a Chile
- Jurgen Klopp – ya yi wasa a Jamus
- Arne Slot – ya yi wasa a Netherlands
Sir Kenny Dalglish shi ne koci na karshe da ya lashe Premier League a kakar 1994/95. Ya taba buga wasa a matakin koli a Ingila tare da Liverpool, amma ya riga ya yi ritaya kafin fara kakar Premier League ta farko a watan Agustan 1992.