Manchester City na shirye-shiryen rabuwa da Pep Guardiola a Etihad, bayan wasan Premier League a ranar Lahadi a karawa da Aston Villa.
Majiyoyi sun shaida wa BBC cewa ana sa ran fitaccen kocin zai bar Etihad Stadium a ƙarshen kakar bana.
City dai tana nan kan matsayinta cewa Guardiola yana da kwantiragi har zuwa kakar wasa mai zuwa, kuma tana fatan zai ci gaba da zama a kungiyar.
Sai dai ana ci gaba da shirye-shiryen ficewarsa a karshen kakar bana, inda wasu ma’aikata ke ganin zai bar aikin.
Haka kuma an fahimtar cewa wasu daga cikin ƴan wasan suna tsammanin zai yi bankwana bayan wasan ƙarshe a kakar bana da Villa.
Tsohon kocin Chelsea, Enzo Maresca, wanda ya taba aiki ƙarƙashin Guardiola a City, shi ne kan gaba wajen maye gurbin mai shekara 55.