Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Arbeloa zai bar aikin kociyan Real Madrid a karshen kakar bana
Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga 17 zuwa 24 ga watan Mayun 2026.
Taƙaitattu
- Ingila za ta buga gasar kofin duniya ba tare da Foden da Palmer da Arnold
- Burin Ronaldo ya ci ya lashe babban kofin Saudiyya a bana
- Manchester United ta tabbatarwa da Carrick mukamin kociyanta
- Guardiolazai bar Manchester City bayan sama da shekara 10 a Etihad
- Mourinho na son Rashford a Madrid, Everton na harin Osula
- Arbeloa zai bar Real Madrid a karshen kakar nan
- Brazil ta saka Neymar cikin ƴan wasan da za su buga mata kofin duniya
- Ku shiga zaurenmu na BBC Hausa WhatsApp
- Za ku iya tafka muhara a shafnmu na sada zumunta a BBC Hausa Facebook
Rahoto kai-tsaye
Mohammed Abdu
Wasannin Burnley biyar baya
, Arsenal da Burnley
Arsenal ta yi nasara a wasa 16 a Premier League a wannan kakar ba tare da an zura mata ƙwallo ba a raga. Ta taɓa yin haka sau 17 a kakar 2023-24 (17).
Bakwai daga cikin nasarorin sun kasance 1-0, kuma rabon da ta yi nasara fiye da haka da wannan sakamakon shi ne a 1998-99 (guda tara).
, Arsenal da Burnley
Burnley ta yi nasara sau ɗaya kacal cikin wasa 27 na baya bayan nan a Premier League (canjaras takwas aka doke ta 18).
Ta samu maki 11 kacal a wannan lokaci — maki ɗaya fiye da wanda ta samu a wasa tara na farko da fara kakar (guda 10).
, Arsenal da Burnley
Arsenal ta ci ƙwallo 17 daga ƴan wasan da suka suka yi canji daga zaman benci a wannan kakar — mafi yawa a gasar.
Ƙwallon da Leandro Trossard ya zura a raga a wasan West Ham United, Martin Odegaard ne ya taimaka masa da ƙwallon bayan da ya shiga karawar daga baya.
Tara daga cikin ƙwallaye 14 na Viktor Gyökeres a Premier League a wannan kakar sun zo ne a wasannin gida. ‘Yan wasan Arsenal uku kacal suka ci 10 ko fiye da haka a gida a kakar su ta farko da ƙungiyar:
Thierry Henry (11 a 1999-00)
Olivier Giroud (10 a 2012-13)
Alexandre Lacazette (11 a 2017-18)
Wasannin da suka rage na fidda wadda za ta lashe Premier League
Bangaren Arsenal
Arsenal v Burnley - A daren nan
Crystal Palace v Arsenal - Ranar 24 ga watan Mayu
Bangaren Man City
Bournemouth v Man City - Ranar Talata
Man City v Aston Villa -Ranar 24 ga watan Mayu
Labarin yadda Arsenal za ta fuskanci Burnley, Arsenal da Burnley
Bayan da Ben White ya ji raunin gwiwa da zai hana shi buga gasar kofin duniya, tuni Arsenal ta maye gurbinsa da Mosquera a wasan ranar Litinin.
Wannan shi ne ɗaya daga canji uku da Gunners daga yan wasan da suka ci West Ham 1-0.
Ƴan wasan Arsenal 111: Raya, Calafiori, Gabriel, Saliba, Mosquera, Odegaard, Rice, Trossard, Eze, Saka, Havertz.
Ƴan zaman benci: Arrizabalaga, Hincapie, Lewis-Skelly, Zubimendi, Dowman, Martinelli, Madueke, Jesus, Gyokeres.
Labari kan ƴan wasan Burnley da za su fuskanci Arsenal, Arsenal da Burnley
Tuni dai ta bar Premier League za ta koma buga champions League a baɗi - ta kuma sanar da ƴan wasa 11 da suka tashi 2-2 da Aston Villa ranar 10 ga watan Mayu.
Ƴan wasan Burnley 11: Weiss, Pires, Esteve, Tuanzebe, Walker, Ugochukwe, Florentino, Anthony, Mejbri, Tchaouna, Flemming.
Masu zaman benci: Dubravka, Hartman, Humphreys, Worrall, Ward-Prowse, Laurent, Bruun Larsen, Amdouni, Edwards.
Sakamakon wasannin da aka buga ranar Lahadi, Premier League
Teburin Premier League
Ya kamata a soke ƙwallo na biyu da Man United ta ci Forest an sa hannu, Premier League
Ya kamata a soke ƙwallo na biyu da Manchester United ta ci Nottingham Forest a wasan Premier League ranar Lahadi, saboda ta taɓa hannu kafin ta faɗa raga, kamar yadda Professional Game Match Officials Limited (PGMO) ta amince.
Hukumar alkalan ta tuntubi Nottingham Forest ranar Litinin domin tabbatar da cewa an yi kuskure wajen yanke hukunci daga alƙali wsa, Michael Salisbury, wanda ya ƙi amincewa da shawarar amfani da Video Assistant Referee (VAR) domin soke ƙwallon.
Ƙwallon ta taɓa hannun ɗan wasan Manchester United, Bryan Mbeumo kafin ya buga ƙwallon wani mai tsaron baya ya tare.
Daga nan abokin wasansa Matheus Cunha ya samu ƙwallon ya buga ta wuce mai tsaron ragar, Nottingham Forest Matz Sels.
An kira Salisbury zuwa wajen kallon abinda ya faru daga jami’in VAR Matt Donohue domin ya soke ƙwallon.
Sai dai Salisbury ya yanke hukuncin cewa bai taɓa ƙwallon da hannun da gangan ba, saboda haka ya tsaya kan hukuncinsa na farko cewa ƙwallon ta halatta.
Tsohon mataimakin De Zerbi ya zama kociyan, Ukraine
Andrea Maldera, tsohon mataimakin kocin Tottenham, Roberto De Zerbi, an naɗa shi a matsayin sabon mai horar da tawagar Ukraine.
Ɗan Italiya shi ne ɗan kasar waje na farko da zai jagoranci Ukraine, inda ya maye gurbin Serhiy Rebrov wanda ya bar aikin a watan Afrilu bayan ƙasar ta kasa samun tikitin shiga gasar FIFA World Cup.
A baya, Maldera ya yi shekara biyar yana aiki a matsayin mataimaki ga Andriy Shevchenko, wanda yanzu shi ne shugaban hukumar ƙwallon kafar Ukrainian, lokacin da yake jagorantar tawagar ƙasar daga 2016 zuwa 2021.
Maldera ya yi aiki tare da De Zerbi a Brighton & Hove Albion da kuma Olympique de Marseille — waɗanda su ne ayyukan De Zerbi biyu na baya-bayan nan kafin ya koma Tottenham.
McGregor zai koma buga UFC bayan jinya, UFC
Tsohon zakaran kambun duniya a wasan damben MMA, Conor McGregor, zai dawo fagen fama a UFC a ranar 11 ga watan Yuli a Las Vegas, kamar yadda shugaban wasan, Dana White ya sanar a wani taron UFC.
Ɗan ƙasar Ireland ɗin, wanda rabon da ya yi wasa tun bayan karya ƙafa a wasa da Dustin Poirier a watan Yulin 2021,
zai fuskanci Max Holloway ɗan Hawaii a babban wasan UFC da za a gudanar a T-Mobile Arena da ke Las Vegas, a ajin lightweight/welterweight.
, Daga Jarida
Chelsea na son ɗaukar ɗan wasan Aston Villa, Morgan Rogers, sai dai Arsenal da Manchester United, da Paris St-Germain na son ɗaukar sa su ma. (Talksport)
Barcelona, da ke jan ƙafa wajen biyan Euro miliyan 30 kan ɗan wasan Manchester United Marcus Rashford da ke a matsayin ɗan wasa aro a Barca zuwa na din-din-din, na sa ne da aniyar Auston Villa na son ɗaukar ɗan wasan Ingilar. (Mundo Deportivo - in Spanish)
Chelsea na neman mai tsaron ragar, kuma hankalinsu ya fi karkata kan mai tsaron Ragar Sunderland Robin Roefs. (Mirror)
Shekara ɗaya ya ragewa ɗan wasan tsakiya na Spaniya, Rodri a Manchester City, sai dai ya ce hankalinsa a kwance ya ke, sannan ya mayar da hankalinsa kan yadda zamansa zai kasance har zuwa ƙarshen kakar wasanni a ƙungiyar. (Marca - in Spanish)
Arsenal na harin ɗan wasan gaban Brazil Gaberial Jesus kan fam miliyan 30, a dai dai lokacin da ake alaƙanta shi da Ac Milan da Juventus. (Caught Offside)
Wadley zai sake dambatawa da Dubois a kambun WBO, Damben boksin
Fabio Wardley ya sake kulla yarjejeniyar dambatawa da takwaransa dan Burtaniya, Daniel Dubois a damben boksin, domin ƙwato kambunsa na WBO Ajin babban Nauyi
A wasan farko da suka buga a turmi na 11 aka dakatar da damben, sakamakon munanan rauni da Wardley ya ji, amma duk da haka ya ki mika wuya a fafatawar.
Duk wanda ya yi nasara zai fuskanci ɗan kasar Ukraine, Oleksandr Usyk, tsohon wanda ya taɓa riƙe dukkan kambi - kambi, yanzu yana da na WBA da WBC da IBF bayan da ya ajiye na WBO.
Sai dai Usyk zai kara da Holland Rico Verhoeven a ranar 23 ga wannan watan a Masar.
Croatia ta sa Modric cikin waɗanda za su buga mata gasar kofin duniya duk da yana jinya, Gasar kofin duniya
Croatia ta saka sunan tsohon ɗan wasan Real Madrid, Luka Modrić cikin tawagarta, domin gasar kofin duniya ta bana, kuma ana sa ran zai murmure daga karayar ƙashin kumatu kafin fara wasannin.
Mai shekara 40, wanda ke taka leda a Inter Milan, ya samu raunin ne bayan buguwa a kai a wasan da suka yi da Juventus a ƙarshen watan Afrilu.
Modrić, wanda ya lashe ƙyautar Ballon d'Or a 2018, an yi masa tiyata bayan raunin, amma duk da haka koci Zlatko Dalić ya saka shi cikin jerin ƴan wasa 26 a tawagar.
Tsohon ɗan wasan Real Madrid da Tottenham ya taka muhimmiyar rawa wajen kai Croatia wasan ƙarshe a kofin duniya a 2018 da kuma wasan kusa da ƙarshe a 2022. Wannan zai kasance kofin duniya na biyar da zai buga.
An kuma saka mai tsaron bayan Manchester City, Joško Gvardiol, duk da cewa ya samu karayar ƙashin ƙafa a watan Janairu.
Dalić ya ce ɗan wasan mai shekara 24 zai samu damar taka leda a wasannin shirye-shirye shiga gasar kofin duniya, domin ya samu kuzari kafin a fara gasar a ranar kofin duniya ranar 11 ga watan Yuni.
Croatia za ta fara karawa da Ingila ranar 17 ga watan Yuni a AT&T Stadium kafin ta kara da Panama da Ghana a fafatawar cikin rukuni.
Yahayan Tarasa ya lashe damben gwamnan Kano, bayan buge Alasan, Damben gargajiya
Yahayan Tarasa ya lashe damben gwamnan jihar Kano ranar Lahadi, bayan da ya doke Alasan Shagon Bahagon Ƴan Sansa a gidan wasa dake Ado Bayero Square a Kano, Nigeria.
Yahayan Tarasa, Guramada ya yi nasara ne a kan ɗan Jamus, Alasan a turmi na biyu, kuma zai karɓi naira miliyan biyu da rabi, yayin da Alasan ya ke da naira miliyan daya da dubu dari biyu da hamsin.
Autan Mamman ne na uku da kuma Bahagon Mancha na hudu, dukkansu daga Jamus a gasar.
An fara damben gwamna bayan da baki ya bude da yan wasa 96, 41 daga Jamus da 30 Guramada da kuma 25 daga Kudu - yanzu kuma za a fara damben Sarauta ana kammala shagulgulan babbar sallah
Sinner ya lashe Italian Open bayan doke Casper Ruud
Jannik Sinner ya lashe Italian Open ranar Lahadi, bayan da ya doke Casper Ruud da ci 6-4, 6-4, karo na shida a jere a gasar Masters 1000 kenan.
Yanzu haka Sinner wanda yake na ɗaya a kwallon tennis a duniya, ya yi bajintar da ake kira a Turance “Golden Masters” wato ya ɗauki dukkan manyan kofunan ATP, kuma na farko dan Italiya, tun bayan bajintar Adriano Panatta shekaru 50 da suka gabata.
Novak Djokovic ne kaɗai ya taba lashe dukkan Masters 1000 guda tara -
Sinner zai shiga gasar Roland Garros da za a fara a watan nan, bayan nasarar lashe wasa 29 a jere - karo na biyar da ya doke Ruud cikin haduwarsu biyar a gasar tennis.
, Daga Jarida
Brentford ta bi sahun Brighton da Chelsea wajen ɗaukar ɗan wasan Congo Said El Mala. (Mail)
Leeds United na son tsawaita kwnataragin ɗan wasan tsakiyar Wales Ethan Ampadu, inda ƙungiya ke sa ran zai amince da hakan, saboda yadda yake son ganin an sabunta masa kwantaragin. (Football Insider)
Mai horar da ƴan wasan Napoli Antonio Conte ya sanar da cewar zai iya barin ƙungiyar a ƙarshen kakar wasan nan, bayan samun nasarar kai ƙungiyar shiga gasar Champion. (Football Italia)
Akwai yiwuwar mai horar da ƴan wasan Lazio Maurizio Sarri, na tattaunawa da Napoli don maye gurbin Conte, inda ya ce yana cikin farin ciki, da rashin sauraren sa da ƙungiyar da ya ke, ke yi masa.(Football Italia)