Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Arbeloa zai bar aikin kociyan Real Madrid a karshen kakar bana

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga 17 zuwa 24 ga watan Mayun 2026.

Taƙaitattu

  • Ingila za ta buga gasar kofin duniya ba tare da Foden da Palmer da Arnold
  • Burin Ronaldo ya ci ya lashe babban kofin Saudiyya a bana
  • Manchester United ta tabbatarwa da Carrick mukamin kociyanta
  • Guardiolazai bar Manchester City bayan sama da shekara 10 a Etihad
  • Mourinho na son Rashford a Madrid, Everton na harin Osula
  • Arbeloa zai bar Real Madrid a karshen kakar nan
  • Brazil ta saka Neymar cikin ƴan wasan da za su buga mata kofin duniya
  • Ku shiga zaurenmu na BBC Hausa WhatsApp
  • Za ku iya tafka muhara a shafnmu na sada zumunta a BBC Hausa Facebook

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Arsenal ta ci kwallo daga bugun kwana, Kai Havert

    Bukayo Saka ya kawo bugun kusurwa mai matuƙar kyau, sannan Kai Havertz ya yi tsalle sama ya saka kai ya taba ƙwallon da ta fada raga a gefen kusurwar raga.

  2. An yi korafin fenariti, Arsenal 0-0 Burnley

    Babban ƙorafi ya taso na neman fanareti ga Arsenal.!

    Bukayo Saka ya yi ƙoƙarin kai ƙwallo cikin raga amma ya faɗi a cikin akwatin fanareti sakamakon karo da Lucas Pires.

    Magoya bayan Arsenal sun yi ƙarfi wajen neman hukunci, amma har yanzu ba a yanke hukunci daga alkalin wasa ba.

  3. , Arsenal 0-0 Burnley

  4. Katin gargadi, Arsenal 0-0 Burnley

    A wannan karon Hannibal Mejbri ya samu katin gargadi (yellow card) bayan da ya yi karo da Gabriel Magalhães.

    Halin nasa bai yi wa magoya bayan Arsenal daɗi sosai ba, domin yana neman tayar da hankali a filin wasa na Emirates.

  5. , Arsenal 0-0 Burnley

    Burnley ta samu damar kai hari ta hanyar Loum Tchaouna wanda ya kutsa daga dama shi kaɗai.

    Ya aika da ƙwallo cikin fili zuwa Hannibal Mejbri, wanda ya yi kokarin taɓawa, amma ya yi mummunan bugun da kwallon ya yi waje sosai.

    An rasa wata babbar dama, domin da an sa natsuwa da ƙwarewa da Burnley ka iya cin ƙwallon.

  6. , Arsenal da Burnley

    Burnley ta yi nasara a wasan waje na ƙarshe a kakar Premier League sau biyu kacal cikin kamfen guda tara — da Aston Villa a 2014-15 da Norwich City F.C. a 2019-20.

  7. Lokacin da Leandro Trossard ya buga kwallo ta bugi turke

  8. , Arsenal 0-0 Burnley

    Eberechi Eze yana yawo a filin ya samu dama, sai ya gano Bukayo Saka a gefen dama.

    Saka ya shigo da ƙafarsa ta hagu ya yi ƙoƙarin buga ƙwallo mai lankwasa, amma ya wuce aka tura ta baya ba tare da ta kai ga burin da ya yi nufi ba.

  9. Kadan ya rage Arsenal ta ci kwallo, Arsenal 0-0 Burnley

    Arsenal ta yi bugun kusurwa dan gajere zuwa cikin fili zuwa Kai Havertz wanda yake cshi kadai a sarari.

    Havertz ya doki ƙwallon da ƙafa ɗaya ya yi ƙoƙarin hakan cikin sauri, amma sai ta bi gefe ta fita waje.

  10. , Arsenal 0-0 Burnley

    Bukayo Saka ya buga ƙwallo mai lankwasa zuwa kusurwar nesa, amma Maxime Estève ya yi kokari da ya turata waje, wanda ya haifar da bugun kusurwa ga Arsenal.

  11. , Arsenal 0-0 Burnley

    Loum Tchaouna ya karɓi ƙwallo a gefen dama a kusa da akwatin fanareti, ya tunkari Riccardo Calafiori, amma ɗan Italiya ɗin ya tsaya da ƙarfi ya yi tare kwallon da aka buga.

  12. , Arsenal 0-0 Burnley

    Declan Rice ya yi bugun tazara cikin salo, amma mai tsaron raga Martin Dúbravka ya yi tsalle ya fitar da ƙwallon da hannu da ƙarfi kafin Gabriel Magalhães ya yi ƙoƙarin bugawa da volley amma ya tura ta waje sosai.

  13. , Arsenal 0-0 Burnley

    Loum Tchaouna ya sa ƙafa cikin sakaci inda ya tare Eberechi Eze, lamarin da ya bai wa abokan hamayyarsa bugun tazara a wuri mai kyau domin kai hari.

  14. , Arsenal F.C. 0-0 Burnley F.C.

    Ana jin ihu daga sassa daban-daban a filin Emirates, yayin da tsohon ɗan bayan Manchester City, Kyle Walker, ke ɓata lokaci kafin ya jefa ƙwallon daga gefe.

  15. , Arsenal da Burnley

    Burnley ba ta taɓa cin fiye da ƙwallo ɗaya ba a duk haduwarta 19 da Arsenal a Premier League (jimillar ƙwallaye 9 kacal ta zura a raga). Wannan shi ne mafi yawan lokutan da wata ƙungiya da ta kara da wata ba tare da cin ƙwallaye biyu a wasa guda ba a tarihin gasar.

  16. , Arsenal 0-0 Burnley

    Jaidon Anthony ya yi bugun kusurwar mai gajeren zango zuwa kusa da sandar raga, kuma Burnley ta sake samun wani bugun kusurwa.

  17. , Arsenal 0-0 Burnley

    A halin yanzu babu wata fargaba tsakanin magoya bayan Arsenal. Yanayin filin ya koma kamar biki, domin sun san yadda ƙungiyar tasu ke kusa da cimma burinta na lashe Premier League.

    Sai dai duk da haka, Burnley ce ta fara samun bugun kusurwa na farko a wasan.

  18. An take ƙwallo Arsenal 0-0 Burnley, Arsenal v Burnley

  19. Wasan da ke gaban Arsenal na lashe kofi a bana

  20. Wasan Arsenal biyar baya a Premier League