Mai tsaron ragar Bayern Munich, Manuel Neuer, ya dawo daga ritayar, bayan da aka gayyace shi cikin tawagar Jamus da za ta je gasar cin kofin duniya ta 2026, inda koci, Julian Nagelsmann ya bayyana cewa zai yi amfani da ɗan wasan mai shekaru 40 a matakin mai tsaron ragar Jamus a gasar.
Neuer, wanda ya taimaka wa Bayern ta lashe kofin Bundesliga tare da kai wa wasan kusa da ƙarshe a Champions League a wannan kakar, ya buga wasansa na ƙarshe a Euro 2024, wanda ya yi wa kasar karawa 124.
Daga baya ya sanar da yin ritaya daga buga wa ƙasa wasanni, bayan da ya taimaka wa Jamus ta lashe kofin duniya a 2014 a Brazil.
Neuer ya buga kofin duniya sau huɗu, kuma yana daga cikin jerin ƴan wasan da shekarunsu suka kai 40 ko fiye da haka da aka zaɓa domin gasar ta bana da za a gudanar a Canada da Mexico da kuma Amurka.
Sauran ƴan wasan da suka kai shekara 40 ko fiye da haka da za su buga gasar kofin duniya a bana sun haɗa da ɗan wasan Portugal, Cristiano Ronaldo mai shekaru 41 da na Croatia Luka Modric mai shekaru 40 da mai tsaron raga Scotland, Craig Gordon mai shekaru 43 da da Edin Dzeko na Bosnia-Herzegovina mai shekaru 40.
Nagelsmann ya gayyaci ƴan wasan Premier League guda biyar a cikin tawagar mutane 26, ciki har da Kai Havertz na Arsenal da Pascal Gross na Brighton da Florian Wirtz na Liverpool tare da masu taka leda a Newcastle United, Malick Thiaw da Nick Woltemade.
Matashin ɗan wasan Bayern, Lennart Karl mai shekara 18 da kuma mai wasa a Galatasaray, Leroy Sane su ma suna cikin tawagar.
Jamus, wadda ta lashe kofin duniya sau huɗu, za ta fara wasanta da Curacao ranar 14 ga watan Yuni kafin ta kara da Ivory Coast da Ecuador a sauran wasannin rukuni.
Tun bayan lashe gasar a 2014, an fitar da Jamus daga matakin rukuni a kofin duniya a 2018 da kuma 2022.
Tawagar Jamus da za ta buga gasar kofin duniya 2026:
Masu tsaron raga: Oliver Baumann (Hoffenheim), Manuel Neuer (Bayern Munich), Alexander Nubel (Stuttgart)
Masu tsaron baya: Waldemar Anton (Borussia Dortmund), Nathaniel Brown (Eintracht Frankfurt), Joshua Kimmich (Bayern Munich), David Raum (RB Leipzig), Antonio Rudiger (Real Madrid), Nico Schlotterbeck (Borussia Dortmund), Jonathan Tah (Bayern Munich), Malick Thiaw (Newcastle United)
Masu buga tsakiya: Nadiem Amiri (Mainz), Leon Goretzka (Bayern Munich), Pascal Gross (Brighton and Hove Albion), Jamie Leweling (Stuttgart), Jamal Musiala (Bayern Munich), Felix Nmecha (Borussia Dortmund), Aleksandar Pavlovic (Bayern Munich), Angelo Stiller (Stuttgart), Florian Wirtz (Liverpool)
Masu cin ƙwallaye: Maximilian Beier (Borussia Dortmund), Kai Havertz (Arsenal), Lennart Karl (Bayern Munich), Leroy Sane (Galatasaray), Deniz Undav (Stuttgart), Nick Woltemade (Newcastle United)