, Australia 1-1 Masar
Kai Trewin, wanda ya shiga wasan daga baya ya samu bugun kusurwa.
Mohammed Abdu tare da taimakon A1
Kai Trewin, wanda ya shiga wasan daga baya ya samu bugun kusurwa.
Australia sai kara kai kora take gidan Masar musamman ta bangaren dama, kuma lokaci na tafiya.

Asalin hoton, Getty Images
Karim Hafez ya faita daga wasan, wanda ya maye gurbinsa shi ne tsohon dan wasan Aston Villa Trezeguet.
Ta fitar da Nestory Irankunda da Cristian Volpato ta saka Ajdin Hrustic da Mo Toure.

Asalin hoton, Getty Images
Sauran kasa da minti 20 lokaci ya cika.
Ko Masar za ta kara ko wasan zai kai ga karin lokaci ne?
Karawar dai ba ta wani kyau yadda ya kamata babu samun damarmaki babu wani abin bajinta sosai.
Mostafa Ziko da Hamdy Fathy sun fita, an kuma maye gurbinsu da Haissem Hassan da kuma Hossam Abdelmaguid.
An je hutun shan ruwa kafin nan kuma Masar ta yi canjin yan wasa.
Tun da aka koma zagaye na biyu Nestory Irankunda yana matsawa masu tsaron bayan Masar, kuma su kula da shi sosai, domin yana da gudu ga karfi kuma.

Asalin hoton, Getty Images
Ana yin bugun tazara zuwa gidan Masar yan wasa suka yi tsalle sama, amma Hany da yake ya fi kowa tsawo shi ne ya sa kai ta fada gida.
Wasan ya koma 1-1 kenan.

Asalin hoton, Getty Images
Australia ta samu bugun tazara daga gefen hagu daf da gidan Masar ko za ta amfana kuwa.

Asalin hoton, Getty Images
An yi bugun tazara, inda yan wasan Australia biyu suka hada a kokarin tare kwallon, Connor Metcalfe da Mohamed Hany.
Za a buga minti 45 za kuma a yi hutun shan ruwa daga nan a tashi a wasan zango na biyu.
Idan aka tashi haka Masar ta kai zagayen yan 16 a karon farko a tarihi.
Idan aka farke za mu je karin lokaci kenan na minti 30, idan sakamakon bai canja ba, a yi bugun fenariti.
An fitar da mai tsaron baya, Kai Trewin, an maye gurbinsa da Jordan Bos.

Asalin hoton, BBC Sport
An je hutu, za su yi hutun minti 15 daga baya su dawo a karasa zango na biyu na 15 za kuma a kara yin hutun shan ruwa.