Nan muka kawo karshen shirin
Da fatan kun ji dadin kasancewa da shirin.
Sunana Mohammed Abdu nake ce muku asuba ta gari.
Mohammed Abdu tare da taimakon A1
Da fatan kun ji dadin kasancewa da shirin.
Sunana Mohammed Abdu nake ce muku asuba ta gari.

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, BBC Sport
Argentina ta kai zagayen yan 16 a gasar cin kofin duniya, bayan da ta doke Cape Verde 3-2.
Kenan za ta fuskanci Masar a karawar yan 16.
Argentina ce mai rike da kofin duniya da ta dauka a Qatar a 2022.
Cape Verde ta yi kokari, wadda ta hana Kamaru zuwa gasar nan, amma ta yi kokari, sai a wasa na hudu ne ta yi rashin nasara, shi ne a hannun Argentina.
Koma dai yaya Argentina ta ji a jikinta, ba za ta taba manta Cape Verde ba, wadda sai da kai ruwa rana.
Cape Verde na kara sa matsi ta farke na ukun, amma kamar lokacin ya kure mata.
Sidny Cabral ya i bugun tazara kamar yadda ya zare na biyu, amma Emi Martinez ya gane mai yake son yi ya sawa kwallon hannu da bi saman raga.
An ce Cape Verde ce ta ci gida ta hannun Diney Borges.
Kwana ce aka kwaso daga wajen Messi, inda Romero ya yi tsalle ya saka kai ta fada raga.

Asalin hoton, Getty Images
Argentina ta yi canji nan da nan..
Gonzalo Montiel, wanda ya zura kwallo a wasan karshe a gasar cin kofin duniya ta 2022 a bugun fenariti, ya maye gurbin Nahuel Molina.

Asalin hoton, Getty Images
Za su karasa minti 15, idan wata tawaga ta ci kwallo shike nan idan ba haka ba sai dai bugun fenariti ya fitar da wadda za ta je zagayen gaba na yan 16 da za ta fuskanci Masar.
Kwallo ce daga bangaren hagu ya dan yi yanka daga nan ya fereta ta kuma yi kwana ta fada ragar Argentina tun daga wajen da'ira ta 18.
Kwallon ta yi kyau matuka. Cape Verde ba tab hakura ba, ana ci tana farkewa.

Asalin hoton, Getty Images
Kevin Pina da Deroy Duarte sun fita an kuma sa Yannick Semedo da Gilson Benchimol madadinsu.

Asalin hoton, Getty Images
An komawa wasan ne Argentina ta kwaso kwana daga hagu cikin gidan Cape Verde aka tashi cin kasuwar sama sai kwallon ta yi gefen dama, inda Martinez ya je a guje ya tara ya kuma sa kafar hagu ya buga da karfi ta fada raga.

Asalin hoton, Getty Images
Ko Cape Verde za ta ci gaba sa kwazon da zai kai bugun fenariti kuwa?
Za su dan huta su koma fili mu ci gaba da wasa na minti 30, kowanne zango minti 15, idan sakamakon ya canja mu tashi idan ba haka ba ta kaimu ga bugun daga kai sai mai tsaron raga.
Argentina ce ke rike da kofin da ta dauka a Qatar a 2022.

Asalin hoton, Getty Images
Messi ya buga, amma mai tsaron gidan Cape Verde ya yi kokawa da kwallon da ta kai Argentina ta samu sa mata kai, amma dai ya kama.
An kara minti takwas da zai iya bayar da kara kwallo na biyu ko kuma mu ci gaba da wasan minti 30 nan gaba.
Idan fa aka ci gaba da haka sai dai fenariti ta raba karawar, kenan an shiga ta mai rabo kenan.