An kammala wasan sai bugun fenariti, Australia 1-1 Masar
Za a fara da mutum biyar-biyar daga nan muga abin da zai faru.
Mohammed Abdu tare da taimakon A1
Za a fara da mutum biyar-biyar daga nan muga abin da zai faru.
Australia ta yi bugun tazara daga gidan Masar, amma an yi karo tsakanin yan wasa biyu kowanne yana kwance. Alkalin wasa ya busa.
An saka dogon gola mai suna Mat Ryan ya maye gurbin Patrick Beach.
Kowa ya san me hakan yake nufi cewar Ryan ya gwanance a tare fenariti.
Bari mu gani an yi karin minti daya.
An buga kwallon ba ta yi kyau ba, domin ta bugi masu tsaron baya ta je jifa, kenan kwallon ya bugi katanga.
Hany na Masar ya yi keta an samu bugun tazara daga irin wajen da Australia ta farke kwallonta.

Asalin hoton, Getty Images
Kamar wani karin karfi ne ya karu a tawagar Masar sai kokarin cin kwallo take, ko tana tunanin bugun fenariti tana da matsala, gwara ta kammala wasan tun yanzu.
Salah ne ya buga kwana ta shiga cikin gidan Australia, amma yan baya sun fitar da ita.
Sai yanzu ne Masara ta buga kwallo mai kyau ta yi bani in baka har ta kai ga Ashour ya samu dama ya buga a cikin gidan Australia, amma ta taba masu tsaron baya ta yi waje zuwa kwana.
Bangarorin biyu suna da ƙarin canji guda ɗaya. Yadda za a yi amfani da shi watakila idan ta kai ga bugun fenariti shi ne abin ji. Za a iya sa mai tsaron raga da ake ganin yana da gogewa a fannin tare fenariti ko kuma wani dan wasan da ya kware a cin bugun daga kai sai mai tsaron raga.
An koma karin lokaci na biyu da za a buga minti 15, idan babu tawagar da ta zura kwallo a raga daga nan sai bugun fenariti da ake kira sai mai rabo.
An kammala minti 15 za a dan huta sannan a koma fili a karasa minti 15 nan gaba.
Kawo yanzu yan wasa sun ci gida sau 13 a gasar cin kofin duniya ta 2026, Ita ce kan gaba da aka yi haka a tarihi. Koda yake da sauran wasanni a gaba, watakila su fi haka, domin za a kai ga zagayen yan 16 da kwata fainal da daf da karshe da wasan karshe.
Dan wasan Masar, Mohamed Hany ya zama na biyu da ya ci gida a wasa biyu a gasar kofin duniya guda, bayan dan Bulgaria, Ivan Vutsov a gasar 1966.
Wannan shi ne karo na hudu a zagayen yan 32 da aka yi karin lokaci a gasar cin kofin duniya ta 2026.
Biyu an kai ga bugun fenariti, yayin da wasan Belgium da Senegal aka kammala shi daf a tashi inda Belgium ta kai zagayen yan 16.
Shin yaya wannan wasan zai kaya?
An bai wa matakin kociya, Ibrahim Hassan katin gargadi na Masar saboda ya yi korafi ga alkalin wasa.
Damar farko da Salah ya samu a wasan nan.
Kwallo ce a cikin gidan Australia daga gefen hagu ya yi kokarin bugata, amma ta yi fadi.
Shi kansa ya san cewar ya kamata kokarinsa ya fi haka.

Asalin hoton, Getty Images
Za a fara yin minti 15 daga nan a juya zango na biyu a kara wani minti 15 daga nan a je bugun fenariti idan babu wadda ta kara cin kwallo.
Za a yi karin lokacin da zai sa a yi minti 15 kowanne zango idan an ci kwallo shi kenan idan babu mu je bugun fenariti.
Masar ta kusan cin kwallo daga bugun da Salah ya yi aka sa kai a daidai wajen da golan Australia yake ya sa hannu ya yi mata gada ta yi waje. Da wasan ya canja yanzun nan.
Lokaci ya cika an yi karin minti biyar.
Idan an ci kwallo mun tashi idan hakan bai yi bu za mu kara minti 30 daga nan aje bugun fenariti duk idan ba a kara cin kwallo ba.