Rufewa
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu
A madadin sauran abokan aiki, ni Aisha Aliyu Jaafar nake cewa mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 11/06/2025
Haruna Ibrahim Kakangi da Aisha Babangida da Aisha Aliyu Jaafar
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu
A madadin sauran abokan aiki, ni Aisha Aliyu Jaafar nake cewa mu kwana lafiya.
Isra'ila ta ce ta gano gawarwakin ƴan ƙasarta biyu da ake tsare da su daga Gaza.
Ɗaya daga cikin gawarwakin na Yair Yaakov ne, na biyun kuma ba a bayyana sunansa ba.
Sojojin Isra'ila sun ce an kashe Mista Yaakov ne a Kibbutz Nir Oz a lokacin harin ranar 7 ga watan Oktoba, sannan aka tafi da gawarsa Gaza.
Firaminista Benjamin Netanyahu ya godewa dakarun Isra'ila kan abin da ya kira ''wani ƙoƙarin dawo da waɗanda aka yi garkuwa da su da aka yi nasara''.
A yanzu saura mutane 53 da ake riƙe da su a Gaza.
An kawo karshen takun saka da aka kwashe tsawon lokaci ana yi tsakanin gwamnatin milkin soji a jamhuriyar Nijar da malaman makaranta na ƙawancen ƙungiyoyin Dynamique.
A jiya ne ɓangarorin biyu suka cimma matsaya, lamarin da ya sa malaman janye yajin aikin da suka tsunduma a farkon mako wanda shine karo na 4 a jere.
An kwashe tsawon lokaci ana tattaunawa, inad gwamnatin ta amince zata biya muhiman buƙatun malaman guda biyu, ciki har da ɗaukan ma'aikata na din-din-din a wannan shekara tare da fara biyansu a shekara mai zuwa, hakazalika ta amince da biyansu alawus alawus da suke bi ta hanyar basu filaye domin a cewar gwamnatin, ba ta da kuɗin biyan waɗannan kuɗaɗe.
An kuma kafa kwamiti domin tattauna yadda za a biya sauran buƙatun malaman kamar bayar da kariya na musamman ga malamai da ke yankunan da ke da haɗari.
Sai dai duk da malaman sun ce sun janye, sun ce a shirye suke su koma yajin aikin idan har gwamnati ta saɓa alƙawuran da ta ɗauka.

Aƙalla makonni biyu da afkuwar ambaliyar ruwan da ta hallaka mutane tare da share gidaje masu dimbin yawa a garin Mokwa na jihar Neja, jama'ar yankin na kokawa kan yadda aka soma jin warin gawarwakin mutanen da har kawo yanzu ba a kai ga ganowa ba.
Jama’a dai na ci gaba da bayyana cewa warin na iya haifar da matsala ga lafiya, musamman ana fargabar barkewar kwalara kasancewar da dama daga rijiyoyin jama’a da suke samun ruwan sha sun rufta.
Daga cikin wadanda BBC ta zanta da su, sun ce tun daga ranar asabar ta karshen makon daya gabata suka soma jin warin gawarwakin.
Sai dai wasu mazauna garin na Mokwa sun ce a yanzu dai fargabar da ake da ita ta ɗan ragu bayan da aka soma yin feshin magani a wasu wurare.
Sun kuma ce Unicef ta bayar da wasu magunguna da ake sawa cikin ruwan da za ayi amfani da shi masu kashe ƙwayoyin cutuka.
Daraktan hulda da jama’a na hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa reshen jihar Niger, Dakta Ibrahim Hussaini Audu ya ce tun daga soma samun warin gawarwakin da ba a kai ga ganowa ba har yanzu, gwamnatin jihar ta dauki matakan gaggawa na raba mutane da wurare, da kuma kai musu tsaftattacen ruwa domin sha.
Tun bayan aukuwar ambaliyar ruwan ta Mokwa da ta yi matuƙar muni, hukumomi a jihar ta Niger sun ce adadin mutanen da suka mutu sun haura 230, yayin da har yanzu ba gano sama da mutum 400 ba.

Asalin hoton, Getty Images
Brian Wilson wanda ya yi haɗin gwiwa wajen kafa ƙungiyar mawaƙa ta Beach Boys cikin shekarun 1960 a Amurka, kuma ya mayar da ita ɗaya daga cikin makaɗan pop mafi tasirin faɗa-a-ji ya rasu yana da shekara 82.
Wilson ya riƙa amfani da sabbin dabaru wajen haɗa kiɗansu na pop, inda ya ɗaukaka hikimomin naɗar waƙa zuwa wani sabon matsayi.
Ya shahara a matsayin ɗaya daga cikin gawurtattun marubutan waƙoƙi mafiya ɓullo da sabbin dabaru a cikin ƙarni na 20.
Ya rubuta kuma ya yi haɗin gwiwar rubuta gomman waƙoƙin da suka yi gagarumin fice ga ƙungiyarsa ta Beach Boys, a ciki har da waƙarsu mai suna God Only Knows da Good Vibrations da California Girls.

Asalin hoton, Nyesom Wike/Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu ya gayyaci ministan Abuja, Nyesom Wike da ya shiga jam'iyyarsu ta APC bisa la'akari da irin ayykan alkairi da yake shimfiɗa wa a babban birnin.
Tinubu wanda ya mika gayyatar ranar Laraba lokacin ƙaddamar da tituna a Abuja, ya ce yana miƙa goron gayyata ga Wike a duk lokacin da ya yanke shawarar sauya sheƙa.
Tinubu ya ce Wike na aiki tuƙuru a gwamnatin APC duk kuwa da cewa shi ba mamba ba ne a jam'iyyar.
“Muna da jajirtaccen mutum mai suna Nyesom Wike. Ba ɗan jam'iyyarmu ba ne ta APC. Amma kuma duk ranar da ya niyyar sauya sheƙa zuwa APC to za mu yi maraba da shi domin mu taya shi baƙanta musu rai." In ji Tinubu.
Nyesom Wike dai ɗan jam'iyyar PDP ne kuma ya ce babu inda zai je duk da halin rikicin cikin gida da jam'iyyar ke fama da shi a yanzu haka.

Asalin hoton, Nigerian Senate/X
Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta yi watsi da ƙorafe-ƙorafe biyu da shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya shigar tare da hukunta shi da biyan kuɗin tarar naira dubu 100
Wani kwamitin alƙalan kotun mai mutum uku ƙarƙashin jagorancin mai Shari’a Hamman Barka ne ya yanke hukuncin, bayan da lauya mai wakiltar Akpabio ya nemi a janye ƙarar.
A cikin ƙorafe-ƙorafen, Akpabio ne mai gabatar da ƙara, inda waɗanda ake ƙara suka haɗa da sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da Shugaban Kwamitin Majalisar dattawa kan Hakkoki, Ladabi da Ƙorafe-ƙorafe, Sanata Neda Imasuen.
A cikin ƙarar, Akpabio ya nemi kotu ta ba da izinin tsawaita lokacin da zai iya neman izinin ɗaukaka ƙara kan hukuncin da babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke a ranar 10 ga Maris, 2025, a shari’ar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta shigar da wasu jami’an majalisa guda uku.
Kotun, a hukuncinta, ta ce ta amince da buƙatar janye ƙorafe-ƙorafen guda biyu, kuma ta yi watsi da su.
Kotun ɗaukaka ƙarar ta kuma umarci Akpabio da ya biya Sanata Natasha tarar naira 100,000, tare da bayyana cewa an yi watsi da daukaka ƙarar gaba ɗaya.

Asalin hoton, Coordination headquarters for the treatment of POWs/ Telegram
Ukraine ta ce Rasha ta dawo mata da gawarwakin sojojinta 1,212 a wani ɓangare na yarjejeniyar musayar fursunoni tsakanin ƙasashen biyu masu yaƙar juna.
Ita ma a nata ɓangaren, Rasha ta ce ta ƙarbi gawarwaki 27, in ji babban mai shiga tsakani na ƙasar Vladimir Medinsky.
Yarjejeniyar musayar fursunoni ita ce kaɗai abin da aka cimma a tattaunawar sulhu da aka yi a Turkiyya a makon da ya gabata, inda ɓangarorin biyu suka amince su mayar wa juna aƙalla gawarwaki 6,000, da marasa lafiya, da fursunonin da suke da munanan raunuka, da kuma waɗanda ba su kai shekara 25 ba.
Medinsky ya sanar da cewa Rasha za ta soma musayar '' fursunoni masu ɗauke da munanan raunuka'' ranar alhamis.
Cibiyar kula da fursunonin yaƙi na Ukraine ta ce nan ba da jimawa ba za ta tabbatar da sunaye da bayanan mamatan.

Asalin hoton, IYALIN Raghuvanshi
Ƴansanda a Indiya sun ce wata amarya da ta yi ɓatan-dabo bayan an gano mijinta da aka yi wa mummunan kisa a lokacin tafiyar cin amarci ta miƙa kanta, kuma a yanzu haka ana tsare da ita.
Tun farko iyalan ma'auratan sun yi zargin cewa ita ma amaryar an kashe ta ne ko kuma an yi garkuwa da ita, inda suka yi ta fafutikar ganin an sako ta.
A yanzu ƴansanda na zargin amaryar mai suna Sonam Raghuvanshi, mai shekara 25 a duniya, ita ce ta ɗauki wasu ƴan daba suka kashe mijinta mai suna Raja mai shekara 30 a duniya a lokacin da suka yi tafiyar cin amarci zuwa jihar Meghalaya da ke arewa maso gabashin ƙasar ta Indiya.
A yanzu an kama wasu ƙarin mutum huɗu.
Mahaifin amaryar, Devi Sigh ya kare ƴarsa tare da cewa "ba ta da hannu a lamarin, ba za ta iya yin wannan aika-aika ba."
Sabbin ma'auratan waɗanda ke zaune a birnin Indore da ke jihar Madhya Pradesh sun yanke shawarar zuwa Meghalaya domin shan amarci ne saboda labarin da suka ji na cewa jihar na da kwazazzabai masu ban sha'awa, kamar yadda ɗan'uwan Raja, Sachin Raghuvanshi ya shaida wa BBC kafin kama amaryar.
A ranar 11 ga watan Mayun da ya gabata ne aka gudanar da bikin aurensu a birnin Indore inda iyalan dukkanin ma'auratan suka yi maraba da bikin.
"An shirya aurensu ne wata huɗu da suka gabata kuma dukkaninsu sun yi murna da lamarin sannan babu wani rikici tsakaninsu kafin, da kuma bayan ɗaura auren," kamar yadda ɗan'uwan angon ya bayyana.
Ma'auratan sun bar gida ne a ranar 20 ga watan Mayu. Sai dai ba a sake jin ɗuriyarsu ba bayan kwana hudu.
Ƴansanda da masu aikin ceto da kuma mutanen yankin sun shiga aikin neman ma'auratan. Masu ceto sun riƙa shiga surƙuƙi da ramuka a ƙoƙarin neman ma'auratan, sai dai hukumomi sun ce ruwan sama da hazo sun zama ƙalubale gare su.
Bayan mako ɗaya an tsinci gawar Raja wadda ta fara ruɓewa, inda aka yi masa yankan rago sannan aka yi awon-gaba da lalitarsa da zoben zinare da kuma sarƙarsa ta wuya. Sai dai ba a ga amaryar ba sama ko ƙasa.
Iyalan ma'auratan sun matsa ƙaimi wajen ganin an gano ta, inda suka zargi jami'an ƴansanda da gazawa wajen aiki.
A Juma'ar da ta gabata iyalan sun rubuta wa Firaministan Indiya, Narendra Modi takarda suna neman a matsa ƙaimi wajen gano Sonam.

Asalin hoton, IYALIN Raghuvanshi
Sai dai a safiyar ranar Litinin, baturen ƴansanda na Meghalaya ya ce Sonam ta miƙa kanta ga ofishin ƴansanda a gundumar Ghazipur da ke jihar Uttar Pradesh.
Daga baya a lokacin ganawa da manema labarai ƴansanda sun ce an kama mutum hudu da ake zargi da hannu.
Duk da cewa bai yi cikakken bayani ba amma ya bayyana amarya Sonam a matsayin "babbar wadda ake zargi".
Mahaifin amaryar ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na ANI cewa Sonam ta samu kanta ne a bakin wata hanya a garin Ghazipur a cikin dare, inda ta ari wayar salula ta kira ɗan'uwanta wanda shi kuma ya sanar da ƴansanda.
Ya ce bai samu magana da ƴar tasa ba amma yana da yaƙinin cewa "ta samu wata hanyar tserewa ne daga hannun masu kisan" kuma ya dage kan cewa "ba ta da hannu" a lamarin.
Ya kuma zargi ƴansandan da "kitsa labarin kisan" sannan ya bukaci ministan harkokin cikin gida Amit Shah ya bayar da umarnin gudanar da bincike domin fayyace gaskiya.

Asalin hoton, Gift of the Givers
Adadin mutanen da suka mutu a lardin Eastern Cape a Afirka ta Kudu ya kai 49 bayan shafe kwananki cikin yanayi mai tsanani na ambaliya da zubar dusar ƙanƙara da kuma tsananin sanyi da ba a saba samu ba.
Cikin waɗanda suka mutu har da yara shida ƴan makaranta da direbobinsu biyu wanda aka gano gawarwakinsu kusa da wani kogi bayan ruwan sama ya tafi da motar su a jiya.
Gwamnatin lardin ta kafa tawagar bayar da agajin gaggawa kuma masu aikin ceto na cigaba da aiki.
Hukumomi sun bayyana yanayin da ake ciki a matsayin iftilai mafi muni a shekarun baya bayan nan, kuma suna ganin adadin mutanen da suka mutu zasu ci gaba da ƙaruwa musamman a ƙauyen Decoligny.
Jami'ai sun ce zuwa yanzu ana ci gaba da neman yara huɗu.
Lardin Eastern Cape na daga cikin yakunan da abin ya fi shafa, inda ɗaruruwan mutane ke kwana a rumfuna bayan ruwa ya shanye gidajensu.
Ruwan sama ya kuma lalata makarantu da tituna da kuma layukan wutar lantarki, lamarin da ya ƙara ta'azzara ayyukan agaji.

Asalin hoton, Getty Images/AP
Hamshaƙin mai kuɗinnan Elon Musk ya ce ya yi da-na-sani kan wasu kalamai da ya yi kan shugaban Amurka Donald Trump a lokacin da suka yi ta cacar baka a shafukan sada zumunta, inda ya ce wasu kalaman sunyi tsauri.
Mutanen biyu sun sami saɓani bayan Musk ya soki ƙudurin harajin Trump.
Kalaman da Musk ya wallafa sun biyo bayan kalaman Trump da ke ayyana cewa alaƙarsu ta zo ƙarshe, kuma ba shi da burin daidaita alaƙar.
Kasafin kuɗin, wanda majalisar wakilai ta amince da shi a watan da ya gabata, a yanzu kuma ƴan majalisar dattawa na nazari kansa ya ƙunshi rage haraji da kuma ƙara kuɗaɗen kashewa a fannin tsaro.
Musk ya buƙaci Amurkawa su yi kira ga wakilansu a Washington su ƙi amincewa da ƙuduri, saboda a ganinsa zai kawo ''koma bayan tattalin arzziki a cikin watanni shidan ƙarshe na shekarar''.
Musk ya yi ikirarin cewa sunan Trump na cikin wasu takardun gwamnati da ba a fitar ba da ke da alaƙa da mutumin nan Jeffrey Epstein wanda kotu ta kama da laifin lalata da ƙananan yara, ba tare da hujja ba.
A nasa martanin, Trump ya yi barazanar soke kwantiragin gwamnati da aka ba Musk wanda suka kai na kusan dala biliyan 38.
Musk ya goge da dama daga rubuce rubucen da ya wallafa a ƙarshen mako, ciki har da wanda ya yi kiran a tsige Trump.

Asalin hoton, KwaZulu-Natal government
Aƙalla mutum 12 ne suka mutu a Afirka ta Kudu sakamakon tsananin sauyin yanayi da ya haɗa da ambaliyar ruwa da yanayin sanyi da kuma zubar dusar ƙanƙara.
Jaridar Eyewitness News ta ruwaito cewa mutum bakwai sun rasa rayukansu a lardin Eastern Cape bayan mummunar ambaliya inda aka gano gawar mutum shida a yankin Decoligny, Mthatha, yayin da kuma gawa ta bakwai aka gano a Tsolo, kusa da Kogin Bedlana.
Jami’an ceto na ci gaba da neman motar bas ɗin makaranta da ambaliyar ta tafi da ita a jiya.
Haka kuma mutane biyar sun mutu a wani hatsarin mota da ya faru a kan babbar hanyar N2, bayan direba ya gwada kauce wa itacen da ya fadi sakamakon zubar dusar ƙanƙara.
A birnin Johannesburg, hukumar wutar lantarki ta City Power ta fitar da gargaɗi kan yiwuwar tangarda ko faduwar tsarin rarraba wutar lantarki, sakamakon ƙaruwar buƙatar wutar.
Afirka ta Kudu kan fuskanci zubar dusar ƙanƙara a lokacin hunturu daga Yuni zuwa Agusta, tare da tsananin sani.

Asalin hoton, Getty Images
Zanga-zanga ta bazu a faɗin Amurka kwanaki bayan zanga-zangar da aka yi a birnin Los Angeles kan kamen ƴan ci-rani da gwamnatin Amurka ta yi.
Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya tura dubban sojoji da ɗaruruwan sojojin ruwa zuwa Los Angeles domin dakile zanga-zangar, abin da ya jawo saɓani tsakanin gwamnati da wasu ’yan siyasar jihohi.
Rikicin ya samo asali ne bayan jami’an shiga da fice suka kama gungun ƴa n ci-rani marasa izini a yankunan da ke da yawan al’ummar Latino.
Tuni aka fara gudanar da gagarumar zanga-zanga daga gaɓar tekun gabas har zuwa yammacin ƙasar, kuma an shirya gudanar da ƙarin zanga-zanga a kwanaki masu zuwa.
Ga jerin wasu biranen da zanga-zangar ta yaɗu zuwa yanzu.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana cewa kusan yara miliyan ɗari da talatin da takwas ne ake tilastawa yin aikin ƙwadago a faɗin duniya.
Hukumar UNICEF tare da ƙungiyar ƙwadago ta Duniya ne suka fitar da wani rahoto na haɗin gwiwa inda suka ce, duk da ci gaban da aka samu, an kasa cika burin kawo ƙarshen yaran yin ƙwadago a shekarar 2025.
Sun bayyana cewa kusan rabin waɗannan ya na fuskantar barazana ga lafiyarsu yayin da suke aiki a ma'adinai, da masana’antu ko gonaki.
A cewar rahoton, da irin wannan yanayi na sauri da ake tafiya da shi yanzu, zai ɗauki daruruwan shekaru kafin a kawar da aikin ƙwadago na yara gaba ɗaya.

Asalin hoton, Governor Plateau state/Facebook
Hare-haren da aka kai a Jihar Filato sun hallaka aƙalla mutum 20 a wannan makon, in ji majiyoyin gwamnati da ƙungiyoyin agaji a ranar Laraba.
Wannan lamari na daga cikin sabbin hare-hare da tashin hankali da ke ci gaba da faruwa a yankin.
Hare-hare daban-daban guda uku da suka faru a yankin ƙaramar hukumar Mangu a ranar Litinin da Talata, sun biyo bayan jerin hare-hare da ramuwar gayya da ake kyautata zaton sun fara ne yayin da mutane ke aikin haƙar ma’adinai a yankin da ke da arzikin Tin, a cewar shugaban ƙaramar hukumar, Emmanuel Bala, da ya shaida wa Kamfanin dillancin labarai na AFP.
"Makiyayan Fulani Musulmai masu yawo da dabbobi sun daɗe suna samun saɓani da manoma da suke zauna a Jihar Filato — waɗanda mafi yawansu Kiristoci ne — kan rikicin mallakar fili da albarkatun ƙasa." in ji shugaban.
Ya ƙara da cewa hare-haren da ake kai wa a yankin sau da yawa na da nasaba da bambancin ƙabila da addini, wanda ke haifar da hare-haren ramuwar gayya marasa kakkautawa.
“Watanni da suka wuce, wasu mazauna yankin na aikin haƙar ma’adinai, sai aka kai musu hari da adduna, kodayake babu wanda ya mutu a harin farko."
"Amma bayan jerin ramuwar gayya da martani, an kai hare-hare uku a ranar Litinin da Talata, wanda ya yi sanadin mutuwar akalla mutum 20", in ji Bala
Wani jami’in Red Cross ya tabbatar da adadin waɗanda suka mutu cikin sa’o’i 24 a harin Chinchin, yana mai cewa adadinsu na iya kai wa 21.

Asalin hoton, Tinubu/X
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu zai yi jawabi ga al’ummar ƙasar da misalin ƙarfe 7 na safe a ranar Alhamis domin bikin ranar Dimokuraɗiyya ta shekarar 2025.
Cikin wata sanarwa da kwamitin shirya bikin ranar Dimokradiyyar ya fitar, ya ce da rana kuma Tinubu zai halarci zaman haɗin gwiwa da ƴan majalisar dokokin ƙasar.
Sai dai sanarwar ta bayyana cewa ba za a gudanar da taron faretin ranar ba a bana. A maimakon haka, za a gudanar da muhawarar jama'a a ɗakin taro na fadar shugaban ƙasa da ƙarfe 4 na yamma.
Bikin na bana na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasar ke cika shekara 26 ƙarƙashin mulkin dimokradiyya ba tare da katsewa ba tun bayan kawo ƙarshen mulkin soja a 1999.
A baya ana bikin ranar dimokradiyya a ranar 29 ga Mayu, wadda ke zama ranar rantsar da shugabannin ƙasa da gwamnoni da kuma ƴan majalisar tarayya da na jihohi.
Amma daga shekarar 2018, an sauya ranar zuwa 12 ga Yuni domin girmama zaɓukan 1993 da aka soke - da MKO Abiola ya lashe - zaɓen da ake ganin mafi sahihanci a tarihin Najeriya.

Asalin hoton, saudigazette
Ma’aikatar Hajji da Umarah ta ƙasar Saudiyya ta sanar da buɗe ƙofarta ga masu son zuwa aikin Umarah na shekarar Hijira ta 1447, wanda zai fara daga ranar Talata, 10 ga Yuni.
Ma’aikatar ta tabbatar da cewa za a fara bayar da takardar izinin Umarah ga ƴan ƙasashen waje daga yau Laraba, 11 ga watan Yuni, ta manhajar "Nusuk".
Saudiyya ta dakatar da bayar da izinin aikin Umarah a watan Afrilun 2025, sannan ta ayyana 29 ga Afrilu a matsayin rana ta ƙarshe da masu Umarah za su bar ƙasar, gabanin aikin Hajjin shekarar 2025.
Mutane sama da miliyan ɗaya da dubu ɗari shida ne suka gudanar da aikin hajjin bana a ƙasar Saudiyya.
Ma’aikatar ta bayyana cewa an fara shirye-shirye tare da haɗin gwiwa da hukumomi da masu ruwa da tsaki, domin tabbatar da saukin aiwatar da dukkan matakai da kuma ci gaba da ingantawa na ayyukan ibada.
Haka kuma ta ce ana ci gaba da ƙoƙari wajen fadada ayyukan gwamnati ta tsarin fasahar zamani da kuma wayar da kai a cikin harsuna daban-daban, da kuma samar da ingantattun matakan tsaro da jin dadi ga masu Umarah.

Asalin hoton, Getty Images
Namrata Nangia tare da mijinta na ta tunani kan batun sake samun wani yaro tun bayan da suka haifi ƴarsu mai shekara biyar.
Sai dai tambayar ita ce: Shin za a iya ɗaukar nauyin haka?"
Tana zaune ne a birnin Mumbai na Indiya, kuma tana aiki a wani waje sayar da maguguna mallakin wani kamfani. Sai dai tsadar kula da yara na ƙaruwa.
Kuɗin makaranta da na motocin bas na ɗaukar ɗalibai har ma da na ganin likita na ƙara saka iyalan cikin matsi.
Ga cikakken labarin - https://bbc.com.im/hausa/articles/ce8270nr63qo%3C/a%3E%3C/p%3E%3C/div%3E%3C/div%3E%3C/article%3E%3C/li%3E%3Cli class="css-xxlek1">