Haruna Ibrahim Kakangi da Aisha Babangida da Aisha Aliyu Jaafar
Gwamnatin Ghana ta roƙi ma'aikatan lafiya da ungozoma su janye yajin aiki
Gwamnatin Ghana ta buƙaci ma'aikatan lafiya da ungozoma da ke yajin aiki tun ranar 2 ga Yuni da su janye yajin aikin wanda yanzu ya shiga mako na biyu.
Yajin aikin in ji gwamnatin ƙasar na haddasa cikas sosai ga tsarin kula da lafiya a ƙasar.
Yajin aikin ya ƙara ta'azzara ne a ranar Litinin lokacin da ma’aikatan suka janye ayyukansu gaba ɗaya daga cibiyoyin lafiya.
Rahotannin kafafen yaɗa labarai na cikin gida sun nuna cewa yajin aikin, wanda ya samo asali daga rikici kan albashi, ya jefa asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya cikin wani hali na rudani da cunkoso da kuma gazawa.
Gwamnatin ta roƙi ma’aikatan da su yi sassauci tare da janye yajin aikin domin ceton rayukan marasa lafiya da ke cikin matsanacin hali.
Mamakon ruwan sama da aka yi a birnin Niamey ya haddasa ambaliya a wasu sassan birnin, inda ruwa ya toshe magudanan ruwa da wasu hanyoyin wucewar ruwa, wanda hakan ya jefa jama’a cikin damuwa.
A yankin Wadata, inda ake da tashar motoci mafi girma, da kuma wasu unguwanni na birnin, an sami cunkoson ababen hawa matuƙar gaske, har da motocin gwamnati da ba su iya wucewa saboda ruwan ambaliya da ya mamaye hanyoyi.
Wasu mazauna birnin Niamey sun bayyana damuwarsu kan yadda magudanan ruwa suka toshe tun da aka fara ruwan sama a bana, lamarin da ke ƙara tsananta halin da ake ciki.
Wani mazaunin birnin da ba a bayyana sunansa ba ya bayyana rashin jin daɗinsa da yadda hukumomin birnin ke tafiyar da lamarin, yana mai cewa: “Hukumomin yankin su ne ke da alhakin tsaftace shara da kuma gyaran matsalolin da suka shafi Niamey gaba ɗaya.”
Ya ƙara da cewa, “Saboda ruwan sama mai yawa da ke ci gaba da sauka a garin, mun fuskanci ambaliya a kusan ko’ina. Muna kira ga hukumomin yankin Niamey da su gaggauta ɗaukar matakin da ya dace domin shawo kan wannan matsala.”
“Muna buƙatar a sake duba dukkan magudanan ruwa da hanyoyin fitar ruwa domin kauce wa afkuwar wasu bala’o’in da ke da nasaba da sauyin yanayi,” in ji shi.
Rikici ya ɓarke kan shirya jana’izar tsohon shugaban Zambia
Asalin hoton, AFP/Getty Images
Shirin jana’izar tsohon shugaban ƙasar Zambia, Edgar Lungu, ya haifar da rikici tsakanin iyalansa da gwamnati da kuma jam’iyyarsa ta siyasa, Patriotic Front (PF), lamarin da ya jefa jama’ar ƙasar cikin ruɗani game da yadda za a gudanar da girmamawar ƙarshe ga mamacin.
Lungu, wanda ya jagoranci Zambia daga shekarar 2015 zuwa 2021, ya rasu a ranar Alhamis da ta gabata yana da shekara 68.
Mutuwarsa ta girgiza ƙasar baki ɗaya, inda duk gidajen rediyo ke kunna waƙoƙin yabo domin karrama mamacin da ya ci gaba da taka rawa a siyasar Zambia duk da hana shi tsayawa takara a zaɓen 2026.
Zambia ƙasa ce da ta bayyana kanta a matsayin ƙasar Kiristoci, kuma al’ummar ƙasar na ɗaukar addini da lokacin makoki da muhimmanci ƙwarai.
Gwamnati ta sanar da cewa za a shirya masa jana’izar ƙasa tare da ayyana wani otal mallakin gwamnati da ke Lusaka, babban birnin ƙasar, a matsayin wurin gudanar da taron girmamawa.
Sai dai jam’iyyar PF ta ƙi amincewa da wannan tsari, tana mai umurtar magoya bayanta da su yi alhini a hedikwatar jam’iyyar.
Iyalin marigayin kuma sun bayyana cewa ba su da matsala da shirya jana’izar ƙasa, amma sun dage cewa dole ne su zaɓi wanda zai jagoranci jana’izar.
Lauyan iyalan mamacin, Makebi Zulu, ya shaida wa BBC cewa iyalan Lungu na son tabbatar da cewa ana bin tsarin da ya dace da ra’ayinsu da na marigayin kansa.
Yayin da ake ci gaba da shirin jana’izar, rikicin da ya kunno kai tsakanin ɓangarorin daban-daban na siyasa da iyalai na barazana ga daidaiton shirin, tare da barin jama’a cikin ruɗani da tambayar inda za su nuna girmamawa ga tsohon shugaban da suke kauna.
Ƴan majalisa sun gayyaci ministan cikin gida kan mutuwar malami a Kenya
Asalin hoton, Andalou via Getty Images
An kira ministan cikin gida na Kenya da manyan jami’an ‘yan sanda na ƙasar da su bayyana gaban kwamitin ‘yan majalisa a yau domin bayar da shaida kan mutuwar wani malamin makaranta a hannun ‘yan sanda.
Mutuwar malamin mai suna Albert Ojwang a hannun ƴansanda ya tayar da ƙura a faɗin ƙasar.
Sakamakon binciken sanadin mutuwa kan gawar malamin makarantar da aka yi jiya ya nuna cewa ya mutu ne sakamakon bugun a kansa da aka masa, kuma akwai alamun cewa an yi masa dukan tsiya – wanda hakan ya banmbanta da bayanin da ‘yan sanda suka bayar cewa ya ji wa kansa rauni ne da kansa.
An tsare Ojwang ne a ranar Asabar, bisa zargin cewa ya wallafa wani rubutu a dandalin X inda ya soki ‘yan sanda.
Zanga-zangar goyon bayan baƙin haure na ƙara bazuwa a wasu biranen Amurka
Asalin hoton, Los Angelos
Zanga-zangar nuna goyon baya ga masu nuna ƙin amincewa ga samamen da gwamnatin Trump ke yi kan baƙin haure na ƙara samun karɓuwa a wasu biranen Amurka.
A New York, inda mutum 2,000 suka yi zanga-zanga, ƴansanda sun kama mutane da dama da suka toshe hanya yayin da a Chicago aka ƙara kama wasu.
Tun da farko wani alƙali a Amuka ya ƙi amincewa da buƙatar gaggawa daga gwamnan California ta hana amfani da dakarun tsaron da aka tura Los Angeles domin daƙile zanga-zangar.
Wakilin BBC ya ce tura sojojin ƙundumbalar da Trump ya yi ne ya fusata mutane da dama har da gwamnan.
Mista Trump ya ce aike sojojin ƙundumbala da dakarun tsaro zuwa birnin ya zama dole domin hana abokan gaba samun galaba a Los Angeles.
Assalamu alaikum
Masu bin shafin BBC Hausa kai tsaye, barkanmu da safiyar ranar Laraba, ta bawa ranar samu, kamar yadda Hausawa ke yi mata kirari.
Sannunmu da sake haɗuwa a wanann shafi domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.
Ku kasance da mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.