Da gaske ne APC ta gargaɗi Ndume kan kalaman da ya yi game da zaɓen 2027?

Asalin hoton, OTHER
Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta musanta cewa ta gargadi daya daga cikin sanatocinta wato Sanata Muhammad Ali Ndume, mai wakiltar mazabar Borno ta kudu a majalisar dattawan kasar a game da wasu kalamai da ya furta, inda ya bayar da shawara ga shugaba Bola Ahmed Tinubu a kan ya yi kaffa-kaffa da nuna amincewar da ake ta yi masa tun yanzu, a game da zaben shekara ta 2027.
Kalaman Sanatan tsokaci ne ga shugaba Bola Ahmed Tinubu, cewa nuna amincewar da ake ta yi masa tun yanzu na iya zama shigo-shigo ba zurfi.
Daraktan yada labarai na jam'iyyar APC Bala Ibrahim, ya tofa albarkacin bakin jam'iyyar, amma ya shaida wa BBC cewa shi sanata Ndume, dan jam'iyyar APC ne da ake mutuntawa, sannan a baya ya sha yin maganganu a kan yadda APC ke mulkin kasar.
Ya ce," A wani lokaci maganganun da Ndume ke yi na cin karo da abin da jam'iyya ke yi, to amma da yake ita jam'iyyar APC na da sassaucin ra'ayi tana ba wa 'ya'yanta damar bayyana ra'ayoyinsu idan dai bai sabawa ka'ida ba."
Bala Ibrahim, ya ce," Ni a ganina wannan kalamai na Ndume na baya bayannan kamar kashedi yake yi wa shugaba Tinubu, amma da ake Ambato cewa kamar an masa gargadi to babu wanda ya yi masa gargadi sannan babu wanda ya ce zai dauki mataki a kansa, amma kuma jam'iyya na da hanyoyin da ta ke bi wajen ladaftar da duk wani dan jam'iyya da ya aikata ba dai-dai ba."
To sai dai kuma a nasa bangaren, sanata Ali Ndume, ya shaida wa BBC cewa duk abin da ya fada menene ba dai-dai ba?, idan har a kwai hujjar da ta fi abin da na fada to zan amsa na yi laifi har ma na ba da hakuri idan kuma hukunta ni za a yi sai a hukunta ni a kan laifin da na yi.
Ya ce," Dole ne mu fadi abin da ke damun jama'a, ni ba sukar jam'iyar APC nake ba na fadi gaskiya ne a waje domin ba a samun ganin shugaban kasa ballantana ka fada masa wadannan abubuwan, duk wata hanya da zan bi don naga shugaba Tinubu na bi ta amma ban samu ganinsa ba."
" Ni fa ba zan daina fadar gaskiya ba ko ina jam'iyya ko bana jam'iyya in yaso idan jam'iyya ta ga dama ta kore ni ni ba zan fasa fadin gaskiya ba." In ji shi.
Ya zuwa yanzu dai a iya cewa dan majalisar dattawan ya zama gugar karfe sha kwaramniya, sakamakon ire-iren kalamansa na sukar abin da yake ganin an yi a gwamnatance ba dai-dai ba, ko kuma ba zai yi wa talaka dadi ba.
Al'amarin da har ya kai ga a baya aka dakatar da shi daga majalisa, tare da haddasa abin da yakan kira mayar da shi saniyar ware.
Ali Ndume, sanata ne wanda ya yi suna wajen sukar manufofin gwamnati, yayin da magoya bayansa ke masa kallon mai faɗin albarkacin bakinsa ba tare da tsoro ba.
Wannan dai ba shi ne karo na farko da Majalisar Dattijan Najeriyar ta dakatar da wani wakili nata ba.












