Me ya sa a yanzu mutane ba su son haihuwar ƴaƴa da yawa?

Wata mata riƙe da ɗanta suna tafiya cikin wani wurin shakatawa

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Stephanie Hegarty
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Global Population Correspondent
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Namrata Nangia tare da mijinta na ta tunani kan batun sake samun wani yaro tun bayan da suka haifi ƴarsu mai shekara biyar.

Sai dai tambayar ita ce: Shin za a iya ɗaukar nauyin haka?"

Tana zaune ne a birnin Mumbai na Indiya, kuma tana aiki a wani waje sayar da maguguna mallakin wani kamfani. Sai dai tsadar kula da yara na ƙaruwa.

Kuɗin makaranta da na motocin bas na ɗaukar ɗalibai har ma da na ganin likita na ƙara saka iyalan cikin matsi.

Yanayin daban yake lokacin da Namrata ke tasowa. "Mun saba zuwa makaranta babu wani abu na daban, sai dai yanzu sai ka tura yaranka su yi iwo, za ka tura su yin zane-zane, za ka kuma kalli ƙarin wani abin da za su yi."

A cewar sabon rahoton hukumar kula da yawan al'umma ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNFPA), ta ce ba a cika samun irin yanayin da Namrata ke ciki ba a duniya.

UNFPA ya gudanar da bincike kan mutum 14,000 a faɗin ƙasashe 14 kan yawan yaran da suke so su haifa.

Mutum ɗaya cikin biyar sun ce ba su samu ba ko kuma ba su yi tsammanin samun yawan yaran da suke so ba.

Ƙasashe da aka yi bincike a kansu sun haɗa da - Koriya ta Kudu, Thailand, Italy, Hungary, Jamus, Sweden, Brazil, Mexico, Amurka, Indiya, Indonesiya, Moroko, Afrika ta Kudu da kuma Nijeriya - inda suke da kashi uku na yawan al'ummar duniya.

Sun ƙunshi ƙasashe masu karfi, matsakaita da kuma karamin karfi da kuma waɗanda ke da yawa da kuma karamin alkaluman haihuwa.

UNFPA ya kuma yi bincike kan matasa da kuma waɗanda suka wuce shekarun haihuwa.

Wata mata zaune tana kallon na'urar ɗaukar hoto

Asalin hoton, Namrata Nangia

Bayanan hoto, Namrata Nangia ta ce akwai matsaloli na kuɗi wajen kula da yara a yau
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"An fara samun raguwar haihuwa a duniya ba kaɗan ba," in ji Dakta Natalia Kanem, shugabar hukumar UNFPA.

"Yawancin mutane da aka yi bincike a kansu na son yara biyu ko fiye da haka. Ana samun raguwar alkaluman masu haihuwa ne sakamakon da yawa na ganin ba su iya samar da iyalan da suke so. Kuma wannan shi ne babbar matsala," in ji ta.

"Kiran wannan da matsala, kamar cewa hakan gaske ne. Ina tunanin akwai sauyi," in ji wata masaniya kan yawan al'umma Farfesa Anna Rotkirch - wadda ta yi bincike kan masu son niyyar haihuwa a Turai, wadda kuma ke bai wa gwamnatin Finland shawara kan tsarin al'umma.

"Gaba-ɗaya, akwai batutuwa da dama kan haihuwa," a cewar Farfesa Rotkirch. Yanzu alamu na nuna cewa ana samun ƙaruwar masu haihuwa kaɗan a duniya maimakon a baya. Ta yi bincike sosai kan haka a Turai, kuma tana son ganin haka a matakin duniya.

Ta ce ta ji mamaki lokacin da waɗanda aka yi bincike kansu da suka haura sama da shekara 50 suka ce sun samu yara kaɗan maimakon wanda suka yi niyyar haihuwa tun da farko.

Wata mata a kan lilo da ƴarta suna wasa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Bincike ya nuna cewa ana samun raguwar haihuwa tsakanin mutane da yawa a duniya

Binciken ya gano cewa kashi 39 na mutane waɗanda suka samu adadin yaran da suke so ba sun ce wasu abubuwa ne suka taƙaita musu yin haka. Koriya ita ce ke da yawan irin waɗannan mutane da kashi 58, sai Sweden mai kashi kaɗan da 19.

Gaba-ɗaya, kashi 12 na mutane ne kaɗai suka bayar da dalili na matsalar rashin haihuwa - ko kuma wahala wajen ɗaukar ciki - a matsayin dalilin da ya sa ba su samu irin yawan yaran da suka yi niyyar haihuwa ba.

Sai dai alkaluman sun fi yawa a Thailand (kashi 19), Amurka (kashi 16), Italiya da Afrika ta Kudu (kashi 15), Nijeriya (kashi 14) dai kuma Indiya (kashi 14).

Iyalai huɗu ƴan gida ɗaya na tafiya cikin wani wuri.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ƙwararru sun ce ana samun raguwar masu haihuwa ne saboda mutane suna jin ba su iya renon iyalan da suke so

"Wannan shi ne karon farko da MDD ta fito don yin duba kan batun raguwar haihuwa," a cewar Farfesa Gietel-Basten, masani kan yawan al'umma a jami'ar kimiyya da fasaha a Hong Kong.

Kafin baya-bayan nan, MDD ta fi mayar da hankali ne kan matan da suka haifi yara da yawa fiye da abin da suke so da kuma "rashin cika buƙatar" shan magungunan tsarin iyali, sai dai a baya-bayan nan ana samun raguwar haihuwa a ƙasashe matsakaita, inda UNFPA ta fi mayar da aikace-aikacenta.

Duk da haka, hukumar na gargaɗi kan ɗaukar mataki dangane da raguwar haihuwa.

"A halin yanzu, abin da muke gani bala'i ne, ko dai na ƙaruwar al'umma ko kuma karewar al'umma, in ji Dakta Kanem. "Wannan ne ya janyo irin wannan martani, na ƙoƙarin ganin mata sun samu ƴaƴa da yawa, ko kaɗan."

Ta yi nuni da cewa shekara 40 da suka wuce China, Koriya, Japan, Thailand da kuma Turkiyya dukkansu na cikin damuwa cewa al'ummominsu sun yi matukar yawa. Zuwa 2015 kuwa suna son ƙara yawan haihuwa.

"Muna son mu yi ƙoƙarin ganin mun kauce wa tsare-tsare masu tayar da hankali da waɗannan ƙasashe suke ɓullo da su," a cewar Farfesa Gietel-Basten. "Idan muna suna cikin firgici kan makomar duniya, to me ye ribar ƙara ƙara saka su cikin fargaba?"

Yayin da ƙasashe da dama sun riga da sun fara saba wa da batun raguwar masu haihuwa ta hanyar ƙara ƴan ci-rani da ke shiga ƙasashen ko kuma ƙara yawan mata a wuraren aiki, wannan ya janyo mummunan martani.

"Muna ganin raguwar haihuwa da kuma tsufar al'ummomi wanda ake amfani da shi a matsayin dalili na bijiro da tsare-tsare na hana ƴan ci-rani shiga ƙasashen," in ji ta.

Wani titi cike da dandazon mutane a wani birni.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ƙwararru sun yi gargaɗin cewa raguwar alkaluman masu haihuwa wani lokaci zai iya janyo zazzafar martani

Hukumar kula da yawan al'umma ta MDD ɗin ta kuma gano cewa rashin lokaci, babban dalilin ne da ya sa wasu ba sa samun haihuwa yadda ya kamata. Ga Namrata a Mumbai hakan gaskiya ne.

Tana shafe kusan awa uku a rana zuwa da kuma dawowa daga wurin aikinta. Lokacin da ta koma gida ta gaji sosai - amma tana son keɓe lokaci da ƴarta. Iyalanta ba sa samun isasshen barci.

"Bayan dawowa daga aiki, kina jin cewa a matsayinki na uwa, ba ki samun isasshen lokaci da ƴarki," in ji ta.

"Don haka, za mu mayar da hankali kan guda ɗaya ne kawai."