Alaƙata da Musk ta ƙare ba sauran shiri - Trump

Elon Musk da Donald Trump

Asalin hoton, Getty Images/AP

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce alakarsa da tsohon mai ba shi shawara kuma shakikin abokinsa, babban attajirin duniya, Elon Musk ta kare - babu saura.

A lokacin wata tattaunawa da Trump din ya yi da kafar yada labarai ta NBC a ranar Asabar, ya ce babu wata magana ta sasanto a tsakaninsu daga yanzu.

Kalaman su ne na baya-bayan nan da shugaban ya yi kan irin sukar juna da tsofaffin abokan junan ke yi wa juna, tun bayan da aka samu sabani tsakaninsu game da shirin haraji na Trump din da kuma kudurin gwamnatin Amurkar na kasafin kudi.

Tun bayan da Elon Musk wanda a 'yan kwanakin da suka gabata yake zaman tamkar dan-lele kuma kusa a gwamnatin Trump, da ke shugabantar sabuwar ma'aikatar da Trump ya samar tare da damka wa hamshakin attajirin hukumar ta Goge, ya ajiye mukamin aka fara sa-in-sa tsakaninsu.

Hukumar da ya damka masa wuka da dama don abin da shugaban ya kira inganta ayyukan gwamnati - wadda ta rika zaftare yawan ma'aikatan gwamnati da sunan tsuke bakin aljihu, ya raba gari da abokin nasa a alakar da ta taso tamkar ta auren zobe, suka rika caccakar juna a shafukansu na sada zumunta da muhawara.

Sabanin ya bayyana ne bayan da attajirin lamba daya a duniya - wanda ya bayar da madudin kudi a yakin zaben Trump, ya fito fili ya soki kudurin dokar da ke gaban majalisar dokokin kasar, na tsarin na Trump na haraji da da kashe kudade - kudurin da ke zaman wata babbar manufa ta cikin gida a gwamnatin.

Mafiya yawan 'yan jam'iyyar Republican sun mara baya ga shugaban kasar, har ma mataimakin shugaban JD Vance, ya fito fili shi ma yana sukar Musk, inda ya bayyana shi da cewa ya harzuka ya kuma bar turba, yana abubuwan da suka saba wa hankali, kuma da wuya su sake karbarsa a tafiyarsu.

Vance ya sheda wa, dan jarida mai yada labarai ta intanet, Theo Von, cewa babban kuskure ne ga shugaban kamfanin da ke kera mota mai amfani da lantarki ta Tesla da kuma shirin zuwa sararin samaniya na SpaceX, ya soki shugaban kasar.

Tsawon makonni, attajiri Musk ke caccakar wannnan muhimmin kudurin doka na Trump, yayin da ake shirin mika kudurin ga majalisar dokoki.

A sukar, Mista Musk ya ce, idan har aka amince da kudurin to zai kara wagegen gibi na tiriliyoyin dala ga gibin da tuni ake da shi a kasafin kudin kasar. Bugu da kari kudurin zai sabauta aikin da ya riga ya yi a matsayinsa na shugaban waccan ma'aikata ko hukuma ta inganta ayyukan gwamnati, da kuma ayyukan da ta yi na rage kudaden da gwamnati ke kashewa.

Jim kadan bayan ajiye aikinsa na shugabantar wannan ma'aikata bayan kwana 129, Musk ya rubuta a shafinsa na X cewa, kudurin abin kaico da takaici ne - amma kuma a lokacin bai fito fili ya soki Shugaba Trump ba, kai tsaye.

To amma a martaninsa ranar Alhamis Mista Trump shi kuwa ya fito fili yana cewa, ya ji takaicin halayyar Musk.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Daga nan ne kuma tsofaffin aminan biyu suka bude babin caccakar juna, inda Musk ya mayar da martani da suka bayan suka a shafin na X - har ta kai ga yana cewa idan ba don shi ba da Trump ya sha kasa a zabe, har ma ya yi barin zance da cewa sunan Trump na cikin takardun tuhumar attajirin nan Jeffrey Epstein, wanda ya kashe kansa a gidan yari - na lalata da kananan yara

Kodayake daga baya ya goge wannan rubutu da ya sanya a shafin, kuma lauyan Epstein ya fito ya musanta wannan zargi na alakanta Trump da batun.

Shi ma Trump ya sake mayar da martani da cewa Musk ya dimauce. Har ma ya yi barazanar soke kwangilolin da gwamnati ta bai wa Mista Musk.

Bugu da kari a hirar da ya yi da kafar yada labarai ta NBC, ranar Asabar, Trump din ya ce Musk ya ci mutuncin ofishin shugaban kasa.

Attajirin na daya a duniya wanda ya bayar da gudummawar kusan dala miliyan 250, ga yakin neman zaben Trump, ya nuna alamun cewa ta yiwu ya mara baya ga abokan hamayyar Trump a lokacin zaben rabin wa'adi da za a yi a shekara mai zuwa, ya goyi bayan abokan karawar 'yan majalisar dokokin jam'iyyar Republican da suka mara baya ga kudurin dokar harajin Trump din.

Ko da aka yi wa Trump tambaya a game da yuwuwar Musk ya goyi bayan 'yan takarar majalisar dokoki na jam'iyyar hamayya ta Democrat a karawarsu da 'yan Republican, sai Trump ya kada baki ya ce, ''ai kuwa zai dandana kudarsa''.

Mista Musk na ci gaba da sukar kasafin ku'din gwamnatin, sannan kuma ya yi hasashen fara jam'iyyarsa.

Tun bayan da ya sake hawa mulkin Amurka a karo na biyu, Mista Trump, ya rika bujuro da wasu manufofi da ke janyo sa-in-sa a tsakaninsa da sauran kasashen duniya da ma cikin gida.

Manufofin sun hada da na lafta harai a kan kasashen da ke shigar da hajojinsu Amurka da baki da ke kasar ta Amurka, har ma da wasu jami'o'in kasar, musamman fitacciyar jami'ar nan ta Harvard, wadda ya dakatar da tallafin kudin da gwamnatin kasar ke ba ta, tare da hana ta daukar dalibai na kasashen waje, a kan cewa tana yada akidu na kyamar Yahudawa.