Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 21/11/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 21/11/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Abdullahi Bello da Isiyaku Muhammed

  1. Tsohon mataimakin firaiministan Burtaniya Lord John Prescott ya rasu

    Burtaniya

    Asalin hoton, Getty Images

    Lord John Prescott, tsohon mataimakin firaiministan Burtaniya ya rasu yana da shekara 86.

    Marigayin, wanda tsohon ɗan fafutikar jin daɗin ma'aikata ne, tsohon mataimakin Tony Blair ne.

    A wata sanarwar bayyana rasuwarsa, matar Lord Prescott da ƴaƴansa biyu sun ce ya kwana biyu yana fama da jinyar cutar Alzheimer.

  2. Za a hana yara ƴan ƙasa da shekara 16 hawa soshiyal midiya a Australiya

    Sadarwa

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Australia ta gabatar da ƙuduri domin samar da dokar da za ta haramta wa yara ƴan ƙasa da shekara 16 amfani da shafukan sada zumunta.

    Ministar yaɗa labaran ƙasar, Michelle Rowland, ta shaida wa majalisar dokokin ƙasar cewa wannan shi ne ƙuduri irinsa na farko da zai kare martabar yara da tarbiyyarsu a matakin da zai inganta ƙuruciyarsu.

    Ƙudurin zai buƘaci manhajoji kamar Instagram da TikTok, su tabbatar da bin dokar ko kuma su biya tarar miliyoyin daloli. Manhajojin na da sama da shekara guda domin fitar da tsarin yadda za su katange yara daga shiga shafukan nasu.

    Sai dai haramcin bai shafi wasannin gyam da yara ke yi a shafukan ba.

    Sai dukkan majalisun Austraila sun amince da ƙudurin ne kafin zai zama doka.

  3. ...Daga Bakin Mai Ita tare da Fa'iza Amatullah

    Bayanan bidiyo, ...Daga Bakin Mai Ita tare da Fa'iza Amatullah

    A wannan makon muna kawo muku filin ..Daga Bakin Mai Ita tare da Fa'iza Muhammad da aka fi sani da Amatullah a fina-finan masana'antar Kannywood.

    Fa'iza dai an haife ta a jihar Jigawa inda kuma ta tashi a garin Mubi da ke Adamawa sannan kuma ta koma birnin Kano domin yin harkar fim.

    Jarumar ta ce ta samu damar cika burinta na shiga sana'ar fim ne bayan ta haihu.

  4. Najeriya ta fara farfaɗowa daga matsin tattalin arziki – Shettima

    Shettima

    Asalin hoton, Senator Kashim Shettima/X

    Mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Kashim Shettima ya ce Najeriya ta kama hanyar farfaɗowa daga matsalolin matsin tattalin arzikin da take ciki.

    Shettima ya ce tattalin arzikin ƙasar na cikin gida wato GDP ya haɓaka da kashi 2.98 a rubu'in farko na wannan shekarar.

    Mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne a lokacin da ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya domin buɗe kasuwar duniya ta Legas ta bana, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, inda ya ƙara da cewa tsare-tsaren da gwamnatin Tinubu ta ɓullo da su, an yi su ne domin haɓaka tattalin arzikin ƙasar.

    Shettima, wanda mai taimaka masa na musamman kan ci gaban yankuna, Dr Marian Tomitope Marshall ta wakilta, ya buƙaci waɗanda za su halarci kasuwar duniyar su yi amfani da damar domin kawo hanyoyin inganta tattalin arziki.

    Ya ce gwamnatin Tinubu tana ƙoƙarin samar da hanyoyin sauƙaƙa harkokin kasuwa, domin jin daɗin ƴankasuwa na ciki da wajen ƙasar.

  5. Isra'ila ta kai hare-hare a Gaza - Rahoto

    Gaza

    Asalin hoton, Anadolu via Getty Images

    Ma'aikatan asibiti a arewacin Gaza sun ce mutane da dama sun rasu a wasu hare-hare da Isra'ila ta kai a Gaza.

    Ma'aikatan agaji sun ce sun fara aikin ceto ne da sanyin safiya bayan Isra'ila ta jefa bama-bamai a aƙalla manyan gidaje biyar a Bet Lahia a Gaza.

    Kafofin sadarwa mai alaƙa da Hamas ta ruwaito cewa gomman mutane sun rasu, sannan wasu da dama suna ƙarƙashin baraguzan ƙasa - ciki har da mata da ƙananan yara.

    Har yanzu babu wata sanarwa daga sojojin Isra'ila, sai dai a kwanakin nan ta ƙara ƙaimi wajen kai hare-hare a arewacin Gaza, inda suke cewa suna hakan ne domin hana ƴan Hamas domin sake taruwa da sake shiri.

  6. Wani lauya ya kai ministan Abuja ƙara kan kama mabarata

    Kotu

    Asalin hoton, Getty Images

    A yau ake sa ran babbar kotun tarayya a Najeriya za ta sanya rana domin fara sauraron wata ƙara da wani lauya mai rajin kare haƙƙin ɗan'adam ya shigar inda yake ƙalubalantar matakin kama mabarata a Abuja, babban birnin ƙasar.

    A makwannin baya ne, ministan Abuja Mista Nyesom Wike ya ƙaddamar da matakin kama mabarata waɗanda ya ce sun cika titunan Abuja, har ma sun zama barazana ga tsaron birnin, kuma suna zubar da mutuncin Nijeriya a idon baƙi da ke zuwa kasar.

    Sai dai, Barrista Abba Hikima, wanda ya shigar da ƙarar ya ce matakin ya saɓa wa tsarin mulkin Nijeriya, inda ya ce yanayin ƙasar ce ta jefa mutane halin da suke ciki.

  7. Majalisar Dattawa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

    Lakurawa

    Asalin hoton, Getty Images

    Majalisar Dattijan Najeriya ta buƙaci rundunar sojojin ƙasar da sauran hukumomin tsaro su ƙaddamar matakan katse hanzarin ƙungiyar ƴan bindigar nan ta Lakurawa.

    Majalisar ta kuma yi kira da a ɗauki dukkan matakan da suka dace domin hana su faɗaɗa ayyukansu a yankin arewa maso yammacin ƙasar.

    Ta kuma nemi a ci gaba da sa-ido a yankunan da Lakurawan suka mamaye, inda ta yi gargaɗin cewa a ɗauki matakan da suka dace, domin a cewarsu, haka Boko Haram ta fara.

    Lakurawa dai ƙungiyar ƴanbindiga ne da suka daɗe suna zuwa wasu yankuna na jihohin Sokoto da Kebbi, inda yanzu harkokinsu suka fara ta'azzara.

  8. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Alhamis daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu riƙa kawo muku labarai kai-tsare na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo.

    Ku kasance tare da mu.