An gano yaɗuwar wani sikari mai illa a Najeriya

Asalin hoton, VICTOR DE SCHWANBERG/SPL
Hukumar kare haƙƙin masu sayayya ta Najeriya, wato Consumer Protection Commission, ta gano wani nau'in sikari mara inganci, wanda ba a yi wa rajista ba, da ake sayarwa a kasuwannin ƙasar, musamman ma a shiyyoyin kudu maso yamma da arewa maso gabas na Najeriyar.
Hukumar ta ce tana ƙoƙarin shawo kan lamarin, kamar yadda ta bayyana a wata sanarwa da ta fitar.
Sanarwar da hukumar kare haƙƙin masu sayayyar ta Najeriya, ta wallafa a shafinta na X, ta ce sikarin mara ingancin da ta bankaɗo a wasu kasuwannin ƙasar, wasu kamfanoni ne suka yi satar shigar da shi daga ƙasar Brazil.
Hukumar ta yi nuni cewa an gano sikarin ba ya ɗauke da sinadarin vitamin A da ake matuƙar buƙatar ya ƙunsa, wanda kuma muhimmin abu ne ga inganta lafiyar ido, da kare garkuwar jiki, da kuma kyautata lafiyar bil'Adama.
Hakan ne ma ya sa wannan sukari yake da haɗari ga lafiyar jama'a, baya ga kassara ƙimar kamfanonin sikari na gida, da kuma dama lissafin farashin sukari a ƙasar.
Wasu bayanan sirri da aka kwarmata wa hukumar ne suka kai jami'anta ga gudanar da cikakken bincike a tsanake a sassan Najeriya, musamman a yankunan kudu maso yamma da arewa maso gabas na ƙasar.
Binciken ya gano cewa, mafi yawan sukarin da aka tantance ba shi da wata tartibiyar alama da za a iya shaida sahihancinsa, ciki kuwa har da rashin kwanan watan da aka sarrafa shi da kuma ranar da zai surace.
Sikarin kuma ba shi da rajistar nan ta hukumar NAFDAC da akan wajabta yi wa kayan abinci da magunguna da na masarufi da dai sauransu.
Hukumar kare haƙƙin masu sayayyar ta Najeriyar dai ta lashi takobin bin dukkan matakan da suka kamata, wajen ganin ta dakile bazuwar wannan sukari da ma sauran wasu abubuwa marasa inganci da ake sayarwa a kasuwannin Najeriya.









