Labarin wasanni daga 21 zuwa 31 ga watan Oktoban 2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Asabar 25 zuwa 31 ga watan Oktoban 2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Gossip

    Asalin hoton, Getty Images

    Manchester City da Chelsea da Manchester United na daga cikin ƙungiyoyin da ke neman ɗan wasan Cologne ɗan ƙasar Jamus Said El Mala mai shekara 19. (Sport 1)

    Ɗan wasan gaban Brazil Gabriel Jesus, mai shekara 28, yana son ci gaba da zama a Arsenal aƙalla har zuwa lokacin da kwantiraginsa zai ƙare a watan Yunin 2027. (ESPN)

    Yarjejeniyar aro da Crystal Palace ta ƙulla da Getafe kan ɗan wasan gaban Najeriya Christantus Uche mai shekara 22 za ta zama na dindindin idan har ɗan wasan ya buga wasanni 10 ko fiye da haka. (Sport)

  2. Niger Tornadoes ta doke Kano Pillars a jihar Katsina

    Ahmed Musa

    Asalin hoton, Kano Pillars

    Kano Pillars ta yi rashin nasara 2-0 a hannun Niger Tornadoes a wasan mako na 10 a Premier ta Najeriya ranar Asabar.

    Ƙungiyoyin sun tasshi ba ci 45 ɗin farko, bayan da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu ne Tornadoes ta zura biyu a raga ta hannun Abdulrasheed Shehu Dabai da kuma Terdoo Shimagande.

    Pillars mai ƙwantan wasa tana da maki takwas a mataki na 18 a kasan teburin Premier League.

    Ta buga wasan ne a Katsina, sakamakon hukuncin da hukumar gudanar da gasar ta yanke, bayan hayaniyar da ta ɓarke a wasan da Pillars ta yi a Kano.

  3. Barkanmu da shiga sharhi da bayanan wasanni

    Jama'a barkanmu da shiga shirin sharhi da bayanan wasanni kai tsaye tare da ni Mohammed Abdu Mamman Skipper Tw.

    Za ku iya tafka muhawara a shirin ko bayar da gudunmuwa a BBCHausa Facebook.