Labarin wasanni daga 21 zuwa 31 ga watan Oktoban 2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Asabar 25 zuwa 31 ga watan Oktoban 2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Real Madrid 1-0 Barcelona

    Ƴan wasan tawagar matan Sifaniya sun samu halartar Santiago Bernabeu domin kallon El Clasico da ya haɗa da Laia Aleixandri, Aitana Bonmati, Claudia Pina, Alexia Putellas da kuma Patri Guijarro.

  2. Katin gargaɗi ga Valverde, Real Madrid 1-0 Barcelona

    An bai wa Federico Valverde na Real Madrid katin gargadi na farko da aka fara a wasan na hamayya.

  3. GOAL Real Madrid 1-0 Barcelon, Kylian Mbappe

    Mbappe

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙwallo ce mai kyau da Jude Bellingham ya samu sai kawai ya juya cikin gwaninta ya bai wa Kylian Mbappe shi kuwa ya buga ta wuce mai tsaron ragar Barcelona, Wojciech Szczesny da faɗa raga.

  4. , Real Madrid 0-0 Barcelona

    Bayan da aka duba sai aka ga cewar Mbappe yana gaban Pau Cubarsi, shi ya sa aka ce satar gida.

    Har yanzu Mbappe yana ta saka kaimi, domin ya zura ƙwallo a ragar Barcelona a wasan na El Clasico.

  5. An soke ƙwallon da Real Madrid ta ci, Real Madrid 0-0 Barcelona

    Daga baya alkalin wasa ya soke ƙwallon da Real Madrid ta ci ta hannun Mbappe da cewar an yi satar gida.

  6. GOAL Real Madrid 1-0 Barcelona, Kylian Mbappe

    Mbappe

    Asalin hoton, Getty Images

    Barcelona ce ta yi sakaci daga tsakiya sai Arda Guller ya samu ƙwallon ya kuma bai a Mbappe shi kuma bai ɓata lokaci ba ya buga ta faɗa raga tun daga wajen da'ira ta 18.

  7. , Real Madrid 0-0 Barcelona

    Duk lokacin da ƙwallo ya je wajen Yamal, sai kaji magoya bayan Real Madrid na ihu da kuwwa. watakila suna tsoron kada ya yi musu sakiyar da ba ruwa.

  8. , Real Madrid 0-0 Barcelona

    Motsi mai kyau daga Barcelona, an yi bani in baka tsakanin Marcus Rashford da Alejandro Balde, amma dai Eduardo Camavinga ya ɓata ƙwallon.

  9. Video Assistant Referee, Real Madrid 0-0 Barcelona

    An soke fenaritin da cewar an yi satar gida tun kafin ƙwallon ya je wajen Vinicius.

  10. PENALTY Real Madrid ta samu fenariti, Real Madrid 0-0 Barcelona

    Vinicius Junior ne zai buga ƙwallo sai Lamine Yamal ya sa kafa, amma dai alkalin wasa ya je ya duba a VAR.

  11. KICK-OFF An take wasa tsakanin Real da Barca, Real Madrid 0-0 Barcelona

  12. Wasu wasannin El Clasico da aka buga a baya, Real Madrid 0-0 Barcelona

    An buga El Clasico bakwai tun daga farkon kakar 2023-24. Real Madrid ta yi nasara uku a 2023-24, yayin da Barcelona ta ci huɗu a kakar da ta wuce

    2023-24

    • Barcelona 1-2 Real Madrid (La Liga)
    • Real Madrid 4-1 Barcelona (Supercopa final)
    • Real Madrid 3-2 Barcelona (La Liga)

    2024-25

    • Real Madrid 0-4 Barcelona (La Liga)
    • Real Madrid 2-5 Barcelona (Supercopa final)
    • Barcelona 3-2 Real Madrid (Copa del Rey final)
    • Barcelona 4-3 Real Madrid (La Liga)
  13. Jude Bellingham ya ƙwan da sanin yadda ake buga El Clasico, Real Madrid 0-0 Barcelona

    El Clasico

    Asalin hoton, Getty Images

    Jude Bellingham ɗan wasan tawagar Ingila ya fuskanci Barcelona karo da yawa a dukkan fafatawa, tun bayan da ya koma Real Madrid a 2023.

    Bellingham ya ci ƙwallo uku a wasa biyu da ya fara a La Liga a El Clasicos a 2023-24, inda Real Madrid ta yi nasara gida da waje 2-1 da kuma 3-2.

    Haka kuma yana cikin ƴan wasan da Barcelona ta doke Real Madrid karo huɗu a bara a wasan karshe a Supercopa da Copa del Rey da na La Liga gida da waje.

    Haka kuma Bellingham bai ci ƙwallo ba a dukkan wasa huɗun a bara.

    Shin a wannan karawar Bellingham zai ci Barcelona?

  14. Bellingham da Rashford za su buga El Clasico ranar Lahadi, Real Madrid 0-0 Barcelona

    Xabi Alonso ya yi canji daga ƴan wasa 11 da Real Madrid za ta fuskanci Barcelona.

    Dean Huijsen da Arda Güler da Vinicius Junior suna cikin ƴan wasa, yayin da David Alaba na jinya, haka kuma Rodrygo da Franco Mastantuono na benci.

    Trent Alexander-Arnold ya warke daga jinya amma yana benci

    Real Madrid 11: Courtois, Carreras, Huijsen, Militao, Valverde, Vinicius Junior, Camavinga, Tchouameni, Arda Güler, Mbappe, Bellingham.

    Masu jiran ko-ta-kwana: Lunin, Carvajal, Endrick, Rodrygo, Alexander-Arnold, Gonzalo Garcia, Asencio, Ceballos, Fran Garcia, Brahim, Mendy, Mastantuono.

    Barcelona ta yi sauyi daga ƴan wasan da suka kara da Girona da ta ci 2-1.

    Za a fara da Fermin Lopez da Ferran Torres da suka maye gurbin Toni Fernandez yayin da Marc Casado na beenci.

    Haka kuma za a fara da Marcus Rashford, bayan da Robert Lewandowski da Raphinha na jinya.

    Barcelona 11: Szczesny, Balde, García, Cubarsí, Koundé, López, De Jong, Pedri, Rashford, Torres, Yamal.

    Masu jiran ko-ta-kwana:Araujo, Casado, Martin, Bernal, Torrents, Dro Fernandez, Bardghji, Toni Fernandez, Diego Kochen, Aller, Espart.

  15. Aston Villa na cin Manchester City, Aston Villa 1-0 Manchester City

    Premier

    Asalin hoton, Reuters

    Aston Villa ta ci Manchester City 1-0 a wasan mako na tara a Premier League, kuma Matty Cash ne ya ci ƙwallon ta hannun Emi Buendia.

  16. Abubuwa 10 da ya kamata ku sani kan wasan El Clasico

    El Clasico

    Asalin hoton, Getty Images

    Real Madrid za ta karɓi bakuncin Barcelona a La Liga, wasan farko na hamayya da ake kira El Clasico a bana ranar Lahadi a Santiago Bernabeu.

    Real Madrid mai masukin baki tana ta ɗaya a kan teburi da maki 24, bayan cin wasa takwas da rashin nasara ɗaya a karawa tara baya a gasar.

    Itama Barcelona mai karawa tara tana ta biyun teburi da tazarar maki biyu tsakani da Real Madrid, sakamakon cin wasa bakwai da canajaras ɗaya aka doke ta fafatawa ɗaya.

  17. An kusan take leda tsakanin Real Madrid da Barcelona, El Clasico

    Real Madrid za ta karɓi bakuncn Barcelona a wasan hamayya na El Clasico ranar Lahadi a Santiago Bernabeu.

    Real Madrid ce ta ɗaya a kan teburin La Liga da maki 24 da tazarar biyu tsakani da Barcelona ta biyu.

  18. United ta ci wasa biyu a jere a gida karon farko bayan 2023

    Man United

    Asalin hoton, Reuters

    Manchester United ta doke Brighton 4-2 a wasan mako na tara a Premier League ranar Asabar a Old Trafford.

    Tun kan hutu United ta ci ƙwallo biyu ta hannun Matheus Cunha da Casemiro.

    Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Bryn Mbeumo ya ci uku rigis har da ta daf a tashi.

    Kafin nan Brigton ta zare biyu ta hannun Danny Welbeck da kuma Kostoulas - karo na biyar da Welbeck ya ci United a wasa huɗu baya.

    Wannan shi ne karo na uku da United ta yi nasara uku a jere a Premier League karkashin Ruben Amorim, tun bayan watan Mayu zuwa Agustan 2024.

    Ƙungiyar da United ta doke ta haɗa da Sunderland 2-0 a Old Trafford da kuma cin Liverpool 2-1 a Anfield da Brighton 4-2 a Old Trafford.

    Haka kuma karon farko da United ta ci wasa biyu a jere a gida karshin ɗan kasar Portugal tun bayan Agustan 2023.

    Kenan ta yi nasara a kan Sunderland da kuma Brighton a Old Trafford.

    Da wannan sakamakon United za ta buga wasan gaba a Nottingham Fores da gidan Tottenham daga nan ta kece raini da Everton a gida.

  19. Gossip

    Asalin hoton, Getty Images

    Chelsea za ta iya samun ragin fam miliyan 52 idan har ta dakatar da batun sayen ɗan wasan bayan Faransa Dayot Upamecano har zuwa bazara mai zuwa lokacin da zai kasance ɗan wasa mai zaman kansa - amma akwai haɗarin za ta iya rasa ɗan wasan mai shekara 26 idan har Bayern Munich ta yanke shawarar cefanar da shi a watan Janairu, inda Liverpool ke cikin ƙungiyoyin da ke sha'awar ɗan wasan. (Football.London)

    Duk da cewa ɗan wasan tsakiya na Sporting ɗan ƙasar Denmark Morten Hjulmand, mai shekara 26, yana da farashin fam miliyan 70, Manchester United na da ƙwarin gwiwar cewa za ta iya sayen shi a kan fam miliyan 50. (Teamtalk)

    Har ila yau Manchester United na ci gaba da zawarcin ɗan wasan Bayern Munich da Jamus Aleksandar Pavlovic, mai shekara 21. (Caught Offside)

    Real Madrid na da niyyar kashe Yuro miliyan 100 don sayen ɗan wasan gaban Turkiyya Kenan Yildiz mai shekara 20 daga Juventus. (Fichajes)

    Fulham na ƙara ƙaimi wurin amincewa da sabon kwantiragi da kocinta Marco Silva, inda ta ke fafutukar hana kocin ɗan ƙasar Portugal tafiya a ƙarshen kakar wasa ta bana. (Football Insider)

  20. Hakimi ya ci ƙwallo biyu a wasan da PSG ta doke Brest a Ligue 1

    PSG

    Asalin hoton, Reuters

    Paris St Germain ta je ta doke Brest 3-0 a Ligue 1 ranar Asabar.

    Achraf Hakimi ne ya ci biyu da kuma Desire Doue da hakan ya sa Paris St-Germain ta koma kan teburin Ligue 1.

    Brest ta samu damar cin ƙwallo, bayan da aka ba ta fenariti, amma sai dai Romain del Castillo ya buga ƙwallon ya yi faɗi.

    Wanda ya lashe Ballon d'Or, Ousmane Dembele ya shiga canjin ɗan wasa karon farko tun cikin watan Agusta, sakamakon jinya da ya sha fama.

    PSG za ta buga wasa na gaba a babar gasar tamaula ta Faransa ranar Laraba, bayan da za ta je Lorient.