Crystal Palace za ta buga wasa hudu cikin kwana takwas, sakamakon da ta kai zagayen kwata fainal a Carabao Cup ranar Laraba.
Palace ta yi waje da Liverpool 3-0 a Anfield da ta kai ta samu gurbin buga wasannin ƴan takwas, za kuma ta fuskanci Arsenal ranar 15 ga watan Disamba.
Palace za ta karɓi bakuncin Manchester City a Premier League ranar 14 ga Disamba da fuskantar KuPS a Conference League ranar 18 ga Disamba daga nan ta ziyarci Leeds United a Premier League ranar 21 ga watan Disamba.
Man United ba za ta yi gaggawar sai Martinez ya dawo buga mata wasa ba
Asalin hoton, Getty Images
Manchester United ba ta gaggawar sai Lisandro Martinez ya dawo buga mata wasa, bayan da yake jinya.
Ɗan wasan tawagar Argentina ya fara jinya tun daga watan Fabrairu, sakamakon raunin da ya ji a wasa da Crystal Palace.
Rauni na huɗu da mai shekara 27 ke jinya a United da ta kai bai yi karawa 52 ba a Premier League, wanda ya koma Old Trafford daga Ajax a 2022.
Hakan ne ya sa Ruben Amorim baya gaggawar sai ya bukaci ɗan wasan ya dawo ya tsare masa baya, ya gwammace ya yi jinyar da ta dace.
Ranar Asabar United za ta Nottingham Forest a Premier League ranar 1 ga watan Nuwamba.
Serbia ta naɗa Veljko Paunovic sabon kociyanta
Asalin hoton, Getty Images
Serbia ta ɗauki tsohon kociyan, Real Oviedo, Veljko Paunovic a matakin wanda zai ja ragamar tawagar daga ranar Alhamis, sakamakon da Dragan Stojkovic ya ajiye aikin.
Stojkovic ya yi ritaya bayan da Albania ta ci Serbia 1-0 a wasan neman shiga gasar kofin duniya, hakan ya sa ta ci karo da koma baya, wadda take ta uku a teburi bayan Ingila da kuma Albania a rukuni na 11.
Hakan ne ya sa hukumar ƙwallon kafar kafar Serbia ta ɗauki Paunovic, wanda ya lashe mata kofin duniya na matasa ƴan kasa da shekara 20 a 2015.
Serbia na fatan neman shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a Amurka da Canada da kuma Mexico a 2026, duk da saura wasa bibiyu a kammala karawar cikin rukuni.
Paunovic ne ya mayar da Oviedo gasar La Liga, bayan shekara 24 rabonta da babbar gasar tamaula ta Sifaniya, amma sai ƙungiyar ta sallamae shi a watan nan, bayan da take ta 17 a kasan teburi da cin wasa biyu kacal.
Paunovic zai ja ragamar wasan da zai fuskanci Ingila ranar 13 ga Nuwamba, kwana uku tsakani ya kece raini da Latvia.
Doue zai yi jinyar maƙonni, bayan rauni a wasan Lorient
Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan Paris St Germain, Desire Doue ya ji rauni zai kuma yi jinyar maƙonni, kamar yadda ƙungiyar ta sanar ranar Alhamis.
Mai shekara 20 ya fita daga fili a minti na 62 a wasan da PSG ta tashi 1-1 da Lorient ranar Laraba.
Kenan Doue ba zai buga wa Paris St Germain wasan Champions League ba da Bayern Munich da na tawagar Faransa da za ta kara a neman shiga gasar kofin duniya a cikin watan Nuwamba.
A baya ɗan wasan ya sha jinya, har ma bai yi wa PSG karawa shida ba da kuma tawagar Faransa.
Doue ya ci ƙwallo uku ya bayar da ɗaya aka zura a raga a kakar bana a dukkan fafatawa.
Arsenal za ta kara da Palace a kwata fainal a Carabao Cup
Asalin hoton, Getty Images
Arsenal za ta kara da Crystal Palace a zagayen kwata faina a jadawalin Carabao Cup da aka fitar a ranar Laraba.
Gunners ta kai wannan matakin bayan doke Brighton 2-0, karo na takwas a jere ta ci wasa a dukkan fafatawa.
Ita kuwa Liverpool ta ci karo da tasgaro, bayan da Crystal Palace ta yi waje da ita da cin 3-0 a Anfield - karo na biyu da Palace ta yi nasara a kan Liverpool a kakar nan - wasa na shida da aka ci Liverpool daga bakwai baya a dukkan fafatawa.
Manchester City ta je ta doke Swansea City 3-1 da wanda Chelsea ta yi waje road da Wolverhampton da cin 4-3 a Molineu, yayin da Newcastle United ta caskara Tottenham 2-0 a St James Park.
Za a fara wasannin daga 15 ga watan Disamba.
Real Madrid na neman diyya daga Uefa
Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid na neman biyan diyya daga hukumar ƙwallon kafar nahiyar Turai, Uefa, bayan da wata kotu a Sifaniya ta kori ɗaukaka karar da Uefa da hukumar ƙwallon kafar Sifaniya da ta La Liga, kan abinda ya shafi Super League.
Real Madrid tana daga ƙungiya 12 da ta yi kokarin kafa sabuwar gasa a 2021, daga baya aka soke tsarin, bayan matsi daga magoya baya da kuma gwamnati.
Haka kuma Uefa ta dakatar da shirin kafa sabuwar gasar Super League da yin barazanar ɗora takunkumi ga ƙungiyoyin da suke da hannu a shirin da bai kai labari ba.
Sai dai kuma a watan Disambar 2023 wata kotu a Turai ta ce Uefa da Fifa sun saɓa dokar Turai da suka yi hakan.
Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan tsakiyar Brazil mai shekara 28, Lucas Paqueta, na shirin barin West Ham a watan Janairu. (Times - subscription required)
Tottenham na fatan ɗauko ɗan wasan tsakiyar Scotland mai shekara 28, Scott McTominay daga Napoli. (Teamtalk)
Napoli za ta ƙara yunƙurin sayen ɗan wasan tsakiyar Ingila mai shekara 20, Kobbie Mainoo daga Manchester United a watan Janairu. (Gazzetta dello Sport - in Italian)
Manchester City ta fara tattaunawa da ɗan wasan tsakiyar Sifaniya mai shekara 29, Rodri, a kan ƙulla sabuwar kwangila da shi kafin ƙarshen shekarar nan(TBR Football)
Tottenham za ta ɗauko Marc-Andre ter Stegen daga Barcelona a watan Janairu, amma mai tsaron gidan na Jamus mai shekara 33 na da zaɓin tafiya aro a Chelsea.(Teamtalk)
Pedri zai yi jinya, kuma na 12 da ya ji rauni a Barca da fara kakar bana
Asalin hoton, Getty Images
Barcelona ta sanar cewar Pedri ya ji rauni a kafarsa ta hagu, ya shiga jerin ƴan ƙwallon da ke jinya a ƙungiyar.
Ana sa ran mai shekara 22 zai yi jinyar mako huɗu, ba zai buga wa Barcelona wasa uku nan gaba ba, kamar yadda ta sanar.
Haka kuma Pedri ba zai yi wa tawagar Sifaniya wasan neman shiga gasar kofin duniya ba da za ta kara da Georgia da kuma Turkiya a cikin watan Nuwamba.
Kawo yanzu ƴan wasa Barcelona 12 ne suka ji rauni tun daga fara kakar bana.
Wasu daga ciki da ke jinya sun hada da Robert Lewandowski da Gavi da Raphinha da Marc-Andre ter Stegen da kuma Dani Olmo.
Barcelona tana mataki na biyu a teburin La Liga da maki 22 da tazarar biyar tsakani da Real Madrid mai jan ragama.
Saka na fatan lashe kofin duniya da na Premier League a 2026
Asalin hoton, Getty Images
Bukayo Saka ya ce da yiwuwar ya lashe kofin duniya da na Premier League a tawagar Ingila da Arsenal a 2026.
Saka yana daga kashin bayan Arsenal a bana, wadda ke taka rawar gani da fara kakar nan, gunners ta kare a mataki na biyu sau uku a teburin Premier League, tana jan ragamar teburin Premier da tazarar maki huɗu bayan kammala karawa tara.
Ɗan wasan tawagar Ingila ya ce Gunners tana da dukkan damar da take bukata, domin lashe Premier League a bana, kuma Thomas Tuchel zai iya lashe kofin duniya, bayan rawar da Ingila ta taka a Euro 2024.
Saka ya ce Tuchel yana da kwarewar da ya samu a Faransa da Ingila da Jamus da ɗaukar Champions League a Chelsea a 2021.
Kenan Saka na fatan Ingila za ta ɗauki kofin duniya a gasar da Amurka da Canada da kuma Mexico za su gudanar.
An yi wa ɗan wasan Napoli, De Bruyne tiyata cikin nasara
Asalin hoton, Getty Images
An kammala yi wa ɗan wasan Napoli, Kevin De Bruyne tiyata cikin nasara, wanda ya ji rauni a karawar da Napoli ta doke Inter Milan 3-1 a Serie A, kamar yadda ta sanar ranar Laraba.
Ɗan wasan tawagar Belgium ya ji rauni ne, bayan da ya buga fenariti ya kuma ci ƙwallon farko daga nan ya faɗi kasa, sai da masu duba lafiyar ɗan wasa suka kai masa agaji.
Har yanzu Napoli ba ta fayyace ranar da mai shekara 34 zai kammala jinya ya koma fagen daga ba.
De Bruyne ya yi fama da irin raunin da ya ji lokacin da yake wasa a Manchester City da ta kai aka yi masa tiyata a 2023.
Napoli mai rike da kofin Seria A, wadda ke jan ragamar teburi za ta karɓi bakuncin wadda take ta takwas, Como ranar Asabar a babbar gasar tamaula ta Italiya.
Birnin Rabat na Morocco zai karɓi bakuncin wasannin cike gurbin shiga gasar kofin duniya daga nahiyar Afirka a filaye uku, kamar yadda hukumar ƙwallon kafar Afirka ta sanar ranar Laraba.
Najeriya za ta kara da Gabon ranar 13 ga watan Nuwamba daga nan a kece raini tsakanin Kamaru da Jamhuriyar Dimukraɗiyyar Congo.
Ranar Alhamis za a fayyace filin da zai karɓi bakuncin wasan farko da na biyu tsakanin Stade El Barid da Prince Heritier Moulay El Hassan Sports Complex.
Za a buga karawar daf da karshe ranar 16 ga watan Nuwamba a Stade Prince Heritier Moulay Abdellah, kuma duk wadda ta yi nasara za ta je ta buga wani wasan cike gurbin da wata daga sauran nahiyar a cikin watan Maris.
Tuni aka samu kasashe tara daga Afirka da suka samu gurbin shiga gasar kofin duniya da za a yi a Amurka da Canada da kuma Mexico, bayan jan ragamar kowanne rukuni.
Asalin hoton, Getty Images
Chelsea da Tottenham sun nuna sha'awar ɗan wasan tsakiyar Ingila mai shekara 23, Morgan Rogers, amma Aston Villa ta fara tattauna ƙulla sabuwar kwangila da ɗan wasan.(Fabrizio Romano)
Fabio Carvalho zai bar Brentford a watan Janairu, amma ana duba yadda ƙungiyar za ta iya sayen ɗan wasan na Portugal mai shekara 23.
Liverpool na cikin ƙungiyoyin da ke zawarcin ɗan wasan bayan Club Brugge, mai shekara 21, Joel Ordonez. (Ekrem Konur)
Manchester United na zawarcin ɗan wasan gaban AIK da Sweden mai shekara 16, Kevin Filling. (Florian Plettenberg)
Vinicius ya bayar da haƙuri kan ficewa daga fili a wasan El Clasico
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Vinicius Jr
Ɗan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid Vinicius Junior ya nemi afuwar masoya ƙungiyar kan abin da ya aikata a lokacin da aka sauya shi a wasan hamayya tsakanin Madrid da Barcelona a ranar Lahadi.
An cire Vinicius ne daga wasa a minti na 72, inda a maimakon ya koma kan kujerar ƴanwasa sai ya zarce ɗakin sauya kaya domin nuna rashin jin daɗi da matakin.
Daga baya Vinicius ya fito ya koma kan benci a wasan, wanda Madrid ta yin nasara da ci 2-1, sannan bayan hura tashi daga wasa ya shiga cikin ƴanwasan da suka ƙalubalanci ɗan wasan Barcelona Lamine Yamal.
A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Vinicius ya ce: "A yau na nemi afuwar dukkanin Madridistas saboda abin da na aikata a lokacin da aka sauya ni a wasan Clasico".
Ya ƙara da cewa "ina kuma son na nemi afuwar abokan wasana da ƙungiyar da kuma shugabanta.
"Wani lokaci shauƙi yakan rinjaye ni kasancewar a kodayaushe nakan so na yi nasara kuma na taimaki ƙungiyata.
"Ƙoƙarina na ganin na yi gogayya ya samo asali ne daga ƙaunar da nake yi wa wannan ƙungiya da duk wani abu da ya jiɓance ta".
Real Madrid ta ɗauki
Vinicius ne daga ƙungiyar Flamengo a shekarar 2018 kan kudi fam miliyan 38.7,
kuma tun daga lokacin ya ci wa Madrid ƙwallaye 111 a karawa 335.
Sai dai babu
tabbas kan ci gaba da zaman matashin a Madrid, inda rahotannin baya-bayan nan
ke nuna cewa ƙungiyar a shirye take ta sayar da ɗan wasan idan suka samu tayi
mai gwaɓi.
A cikin sanarwar
neman afuwa da ya fitar, Vinicius bai ambaci sunan mai horaswa Xabi Alonso kai tsaye ba a
cikin waɗanda ya bai wa haƙuri, yayin da ake ci gaba da raɗe-radin cewa mutanen
biyu ba sa ga-maciji.
Saliba da Martinelli ba za su buga wa Arsenal Carabao Cup ba da Brighton
Asalin hoton, Getty Images
William Saliba da Gabriel Martinelli ba za su buga wasan zagaye na huɗu ba a Carabao Cup tsakanin Arsenal da Brighton ranar Laraba.
Mai tsaron baya, SSaliba ya ji rauni ne a wasan da Gunners ta doke Crystal Palace 1-0 a Premier League ranar Asabar, a kuma karawar ce Martinelli ya fama rauni, wanda ya shiga karawar daga baya.
Sai dai kociyan Arsenal, Mikel Arteta ya tabbatar da cewar Riccardo Calafiori da Declan Rice da kuma Bukayo Saka za su buga wasan.
Asalin hoton, Getty Images
Manchester United da Newcastle na bibiyar ɗan wasan tsakiyar Ingila, Elliot Anderson, inda Nottingham Forest ke neman a biya ta £120m kan ɗan wasan mai shekara 22. (Florian Plettenberg)
Barcelona na kan gaba wajen zarwarcin ɗan wasan gaban Marseille da Ingland Mason Greenwood, duk da cewa Tottenham da West Ham na neman sayen ɗan wasan mai shekara 24. (Teamtalk)
Jobe Bellingham baya da sha'awar komawa Manchester United, wadda ke neman aron ɗan wasan tsakiyar Borussia Dortmund da Ingila mai shekara 20.(Mirror)
Manchester United za ta ƙi amincewa da buƙatar sauya sheƙar ɗan wasan tsakiyar Ingila mai shekara 20, Kobbie Mainoo, da takwaransa na Netherlands mai shekara 24 Joshua Zirkzee, idan suka nemi barin ƙungiyar a watan Janairu. (Sun)
Manchester United ta bai wa Napoli damar kammala sayen ɗan wasan gaban Denmark maishekara 22, Rasmus Hojlund a watan Janairu.(Mirror)
Ramsey ya kara farashi zuwa dalar Amurka 20,000 ga duk wanda ya ga karensa
Asalin hoton, Aaron Ramsey
Ɗan wasan tawagar Wales, Aaron Ramsey ya kara farashi zuwa dalar Amurka 20,000 ga duk wanda yaga karensa da ya ɓata a Mexico.
Tsohon ɗan wasan Arsenal da Cardiff, wanda ke taka leda a Pumas UNAM a birnin Mexico, ya ce karen na sa mai suna Halo an ganshi a San Miguel de Allende a Mexico a yankin Guanajuato.
Ya kuma ɓata ne ranar 9 ga watan Oktoba dauke da na'urar da ke tantance zirga-zirgar karen, kuma Ramsey ya bayyana hoton taswirar wajen karshe da karen yake.
Golan Inter, Martinez ya buge wani mutum da mota a keken guragu ya mutu
Asalin hoton, Getty Images
Wani mutum a kan keken guragu mai aiki da wutar lantarki ya mutu ranar Talata, bayan da golan Inter Milan, Josep Martinez ya buge shi da mota a yankin Como, kamar yadda ƴansanda suka sanar.
Lamarin ya faru ne ranar Talata, kuma ƴansanda sun ce mutumin ne ya faɗo kan titi.
Har yanzu mahukunta na bincike kan lamarin.
Sai dai Inter ta soke ganawa da ƴan jarida ranar Talata kan wasan da ya kamata ta buga da Fiorentina ranar Laraba a Serie A.
Martinez, mai shekara 27 ya buga wa tawagar Sifaniya wasa ɗaya, kuma shi ne mai jiran ko-ta-kwana a gurbin mai tsare ragar Inter Milan.
Ya koma Inter daga Genoa a bara, kawo yanzu ya buga mata karawa 12.
Inter ta ƙi cewa komai kan lamarin.
Asalin hoton, Getty Images
West Ham ta zage damtse wajen zawarcin ɗan wasan bayan Lille da Brazil, Alexsandro a watan Janairu, inda aka yi wa ɗan wasan mai shekara 26 farashin £26m. (ESPN Mexico - in Portuguese)
Vinicius Jr mai shekara 25 na duba yiwuwar barin Real Madrid bayan nuna damuwa kan canza shi da kocin ƙungiyar, Xabi Alonso, ya yi a wasan hamayya na El Clasico a ranar Lahadi. (AS - in Spanish)
Juventus ta fara tattaunawa da tsohon kocin Napoli da Italiya, Luciano Spalletti mai shekara 66, kan harar da ƙungiyar bayan sallamar Igor Tudor. (Gianluca di Marzio - in Italian)
Tottenham da Arsenal da kuma Newcastle na bibiyar ɗan wasan gaban Porto da Sifaniya, Samu Aghehowa mai shekara 21. (Fichajes - in Spanish)
PSG ta sanar da samun yuro miliyan 837 a kakar 2024/25
Asalin hoton, Reuters
Paris St Germain ta sanar da samun yuro miliyan 837 a kakar 2024/25, kamar yadda ta sanar ranar Talata.
Kenan ƙungiyar Faransa ta samu kuɗin shiga da ya haura na kakar bara yuro miliyan 806.
Mai buga gasar Ligue 1 ta samu yuro miliyan 367 a fannin tallace-tallace da yuro miliyan 175 a fannin kallon wasanninta a Parc des Prince.
Kakar 2024/25 ta zama ta tarihi a PSG da ba za ta taɓa mantawa da ita ba, sakamakon lashe Champions League a karon farko.
A kuma kakar da ta wuce ƙungiyar ta ɗauki kofin Ligue 1 da French Cup da Trophee des Champions da kai wa wasan karshe a Club World Cup, wanda Chelsea ta lashe.
Kamfanin Qatar Sports mai zuba hannun jari ya mallaki PSG A 2011.
Cikin kididdigar da PSG ta yi har da kuɗin da ta samu a Fifa Club World zuwa zagayen kwata fainal, sai kuma a rahoton kakar baɗi za ta saka sauran lissafin har zuwa zagayen karshe.
Sai a bara PSG ta sanar da faɗuwa kasuwancin yuro miliyan 60.
Ban yi nufin baƙantawa kowa ba a El Clasico - Vinicius Jr
Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan Real Madrid, Vinicius Jr ya ce bai yi nufin baƙanta ran kowa ba a lokacin da aka samu hayaniya da ƴan ƙwallon Barcelona a karawar El Clasico ranar Lahadi.
Ɗan kasar Brazil mai shekara 25 bai ji daɗi ba da aka sauya shi a wasan ba, wanda kai tsaye ya wuce ɗakin hutun ƴan wasa.
Daga baya ya dawo kan benci, kuma bayan tashi daga karawar da Real Madrid ta yi nasara 2-1, sai ya je zai kalubalanci matashin ɗan wasa mai shekara 18, Lamine Yamal daga nan aka samu yamutsi tsakanin ƴan wasan.
Vinicius yana daga cikin ƴan ƙwallo biyar da aka bai wa kati a rikicin, yayin da mai tsaron ragar Real Madrid, mai jiran ko-ta-kwana Andriy Lunin aka yi masa jan kati.
Tun kafin wasan Yamal ya harzuka Real Madrid da magoya bayanta kan kalaman da ya yi kan ƙungiyar.