Yadda aka fafata a wasannin Premier mako na 14

Shafi ne da ke kawo maku rahotanni da sharhi kan wasannin Premier League kai-tsaye yayin da suke faruwa.

Rahoto kai-tsaye

Buhari Muhammad Fagge and Umar Mikail

  1. , Liverpool 2-0 Brighton

    Mun gan shi yana matsayin dan baya mai hana ci, kuma mun gan shi yana ci.

    Virgil

    Asalin hoton, BBC Sport

    Bayanan hoto, Virgil
  2. An dawo daga hutun rabin lokaci

    • Liverpool 2-0 Brighton
    • Chelsea 0-0 West Ham
    • Tottenham 1-0 Bournmouth
    • Burnley 0-1 Crystal Palace
  3. Wai ina Giroud ya shiga?, Chelsea 0-0 West Ham

    A farkon wasan ba a ga Olivier Giroud ba, yayin da yake ta kokarin kwatar hannu domin ture Tammy Abraham gefe ya zama a gaba.

    Dan wasan Faransan sau 11 kacal ya taba kwallo, kowa ya fi shi taba kwallo a duka bangarorin biyu.

    Olivier Giroud

    Asalin hoton, bb

    Bayanan hoto, Olivier Giroud
  4. Wilfred Zaha, Burnley 0-1 Crystal Palace

    Babu mamaki Wilfred Zaha ya farfado - ya ci wa Crystal palace kwallo a wasa biyu a jere kenan bayan shafe wasa 13 ba tare da cin ko daya ba.

    Zaha

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Wilfred Zaha
  5. An tafi hutun rabin lokaci

    • Liverpool 2-0 Brighton
    • Chelsea 0-0 West Ham
    • Tottenham 1-0 Bournmouth
    • Burnley 0-1 Crystal Palace
  6. David Martin, Chelsea 0-0 West Ham

    An buga Daya, Biyu, Uku!

    Sai dai mai tsaron raga David Martin ya hana Chelsea rawar gaban hantsi.

  7. Dele Alli, Tottenham 1-0 Bournemouth

    Da alama Dele Alli ya ji dadin zuwan Jose Mourinho Tottenham - sai karade fili yake cikin kuzarin da muka kwana biyu ba mu gani ba.

    Shi ne ya ci wa Tottenham a minti na 21.

  8. Liverpool 2-0 Brighton

    Tun daga farkon kakar wasanin bara, Trent Alexander-Arnold ya fi kowanne dan baya a Premier yawan bayar da kwallo aci, ya bada kwallo 17 an ci, yayin da a lokaci guda kuma Virgil van Dijk ya fi kowanne dan baya yawan cin kwallo, ya ci kwallo 7.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  9. Liverpool 2-0 Brighton, Liverpool 2-0 Brighton

    Ko mai Brighton ta yi a yau shririta yake zama, in ta je gaba wanda ba kasafai take ba sai kwallon ta lalace, ba dai ta komi da zai nuna tana son zare kwallonta.

  10. VAR ta hana kwallon ta biyu, Tottenham 1-0 Bournemouth

  11. GOAL '24, Liverpool 2-0 Brighton

    Van Dijk ne dai ya kara kwallon da salo irin na farko, wato da kai.

  12. GOAL, Tottenham 1-0 Bournemouth

    Dele Alli ya jefa kwallon wadda aka bugo daga baya, harin farko da Tottenham

    ta fara kai wa a wasan kenan.

  13. GOAL '17, Liverpool 1-0 Brighton

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  14. Liverpool 0-0 Brighton, Liverpool 0-0 Brighton

    Adam Webster ya matukar kokari kwace kwallon da ya yi daga kafar Virgil van Dijk yayin da yake neman ya bai wa Mo Salah a cikin yadi na 18

  15. Abraham yana benci, Chelsea 0-0 West Ham

    Yau Chelsea tana wasa ba tare da Tammy Abraham ba yayin da Giroud ya maye gurbinsa.

  16. Mount, Chelsea 0-0 West Ham

    Mason Mount ya buga shot daga wajhen yadi na 18, sai dai mai tsaron ragar West Ham David Martin ya damke kwallon

  17. Antonio, Chelsea 0-0 West Ham

    Antonio ya kai harin farko a ragar Chelsea, inda ya buga kwallo amma ta tsallake turke a cikin yadi na 18.

    Wasan adawa ne na birnin Landan.

  18. An take wasa hudu

    An take waanni har hudu a yammacin nan.

    Za mu gani nan da minti 90, maki nawa Liverpool za ta bayar a saman teburi, sannan wace kungiya ce za ta koma kasan teburi.

  19. An take wasa, Burnley 0-0 Crystal Palace

  20. An take wasa, Liverpool 0-0 Brighton