Yadda aka fafata a wasannin Premier mako na 14

Shafi ne da ke kawo maku rahotanni da sharhi kan wasannin Premier League kai-tsaye yayin da suke faruwa.

Rahoto kai-tsaye

Buhari Muhammad Fagge and Umar Mikail

  1. Danny Ings, Southampton 2-1 Watford

    Danny Ings ne ya ci kashi 50 na kwallon da Southampton ta ci a Premier bana, wannan ne babban kaso da wani ya samu a gasar.

    Abin farin ciki da murna.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  2. GOAL '82 Ward-Prowseeeeeeeeeeeee, Southampton 2-1 Watford

    James Ward-Prowse ya kara abin da ya saba, ya jefa kwallo ta biyu da bugun tazara, Mai tsaron ragar ya samu kwallon amma bai iya fidda ta ba.

  3. GOAL '78, Southampton 1 - 1 Watford

    Ings ne ya jefa kwallon bayan wuyar da Southampton din ta sha kafin ta jefa kwallon.

    Wasa ya dawo danye, kunnen doki, ko wanene zai yi nasara sai dai an tashi mun gani.

  4. Watford ta yi canji '74, Southampton 0-1 Watford

    Will Hughes ya fita kuma Nathaniel Chalobah ne ya canja shi.

  5. Southampton 0-1 Watford, Southampton 0-1 Watford

    Wasa daya kacal Southampton ta ci cikin 43 da ta buga a Premier idan har an zira mata kwallo a minti 45 na farko - ta yi canjaras 7 ta kuma yi rashin nasara 35, nasarar ita ce wadda ta ci Tottenham a watan Maris da ya gabata.

    Ita kuma Watford ta yi rashin nasara sau daya kacal cikin wasa 14 da ta buga a Premier wanda ta samu nasara cikin minti 45 na farko - ta ci 11 ta yi canjaras biyu, rashin nasarar shi ne wanda ta yi a hannun Tottenham da ci 2-1 a watan Junairun.

  6. Watford ta yi canji, Southampton 0-1 Watford

    Gerard Deulofeu ya fita yayin da Andre Gray ya shigo.

  7. , Southampton 0-1 Watford

    Ismail Saar ya kara kai wani mummunan hari sai dai ta yi sama.

  8. Ward-Prowse, Southampton 0-1 Watford

    Ward-Prowse sai kuskure yake yi a wasan.

  9. Katin gargadi, Southampton 0-1 Watford

    An bai wa Redmond katin gargadi bayan ketar da ya yi.

  10. An dawo hutun rabin lokaci, Southampton 0-1 Watford

  11. Mourinho ya ci wasan Premier na farko a gida, Tottenham 3-2 Bournemouth

    Jose Mourinho

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Nasara uku kenan a jere ga Mourinho

    Tottenham ta samu nasarar ta ta biyu a jere a gasar Premier tun bayan da Jose Mourinho ya karbi ragamar jagorancin kungiyar.

    Dele Alli ne ya jefa kwallo biyu a minti na 21 da kuma na 50, abin da ya bai wa kungiyar damar samun nasara uku a jere cikin wasa uku karkashin jagorancin Mourinho kuma nasara biyu da ta yi a jere a kakar bana.

    Sai dai an zira wa Tottenham kwallo a dukkanin wasannin.

    Sakamakon ya dago kungiyar a teburi, inda ta dawo cikin goman farko. Wasannin gobe ne za su tabbatar da matsayinta a teburin amma yanzu tana ta biyar.

    Moussa Sissoko ne ya kara ta uku da watsiya bayan da Son ya ba shi kwallon - ita ce kwallon farko da Moussa Sissoko ya ci cikin wasa 69 da ya buga tun bayan wadda ya ci Huddersfield a watan Afrilun 2017.

    A minti na 73 ne dan wasan Bournemouth din Harry Wilson ya farke kwallo daya da aka ci kungiyarsa, sai kuma a minti na 90 ya kara farke dayar, abin da ya sa hantar 'yan Tottenham ta kada.

    Duk da cewa Bournemouth ta yi yunkuri sosai a karshen wasan amma dai Tottenham ta samu nasarar lashe maki ukunta da kyar.

  12. An tafi hutun rabin lokaci, Southampton 0-1 Watford

  13. Southampton 0-1 Watford, Southampton 0-1 Watford

    Southampton na bukatar kwallo kuma tana yin duk abin da ya dace domin ta ci.

    Yanayin filin wasa na St Mary's ya dau harama ya ke bukatar kwallo.

  14. Southampton 0-1 Watford, Southampton 0-1 Watford

    Ismail Sarr shi ne dan wasa na 27 dan Senegal da yaci kwallo a Premier. a duk cikin kasashen Afrika Najeriya ce ta fi kowacce yawan yan kwallon da suka ci ball a Premier inda take da 31.

  15. Chelsea ta yi barin maki 6 a jere a Premier, Chelsea 0-1 West Ham

    Chelsea ta barar da maki shida a jere a gasar Premier bayan West Ham ta cinye ta har gida da ci 1-0 a wasan mako na 14.

    Kungiyar ta Lampard ita ce ta rike kashi 70% na wasan tun daga farko har karshe. Sai dai ba ta samu nasarar zira kwallo ko daya ba.

    A minti 45 na farko an buga wasan babu ci, sai dai a minti na 3 da dawowa zagaye na biyu dan wasan bayan West Ham Aaron Cresswell ya zira kwallon tilo da aka yi nasara da ita.

    Wannan ce nasara ta farko da West Ham ta samu cikin wasa uku da ta buga a Premier kuma nasara ta farko da ta samu cikin shekara 17 a gidan Chelsea a wasan hamayyar birnin Landan.

    A minti na 70 ne dan wasan gaban West Ham Michail Antonio ya kara kwallo ta biyu a ragar Chelsea, sai dai bayan duba na'urar VAR an gano ya taba kwallon da hannu kuma alkalin wasa ya kashe ta.

    Wannan nasara kamar ruwan sanyi ce ga wutar da take yunkurin cinye mai horarwa Manuel Palagrini, ganin irin kashin da kungiyar ta sha a baya-bayan nan.

    A bangaren Chelsea kuwa wannan ce rashin nasara ta uku a jere da ta yi, bayan kashin da ta sha a hannun Mancester City da ci 2-1 da kuma canjaras da Valencia a gasar Zakarun Turai ta Champions League a tsakiyar mako.

    Chelsea na da maki 26, abin da ya sa har yanzu take cikin cikin jerin kungiyoyi hudun farko - ita ce ta hudun.

    Chelsea

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Wasa uku kenan a jere Chelsea ba ta yi nasara ba
  16. Southampton 0 - 0 Watford, Southampton 0 - 0 Watford

    Southampton ne ke karbar bakuncin wasan.

    kungiyar dai na cikin tsaka mai wuya ganin cewa ta yi rashin nasara a Premier sau 6 cikin wasa 8 da ta buga a baya-bayan nan.

  17. Liverpool ta sha da kyar a hannun Brighton, Liverpool 2-1 Brighton

    jurgen Klopp

    Asalin hoton, @LFC

    Bayanan hoto, Klopp ya ji dadin sakamakon sosai

    Jagorar Premier Liverpool ta ci gaba da zama a saman teburin gasar amma wannan karon da tazarar maki 11 tsakaninta da Manchester City, bayan ta sha da kyar a hannun Brighton da ci 2-1.

    Kare jini biri jini aka yi a wasan, hasali ma Brighton ta fi rike kwallo da kashi 55%, Liverpool kuma ta rike kashi 45%.

    jadawali

    Asalin hoton, BBC Sport

    Dan wasan bayan Liverpool Virgil van Diijk ne gwarzon wasan sakamakon kwallo biyu da ya ci a minti na 18 da kuma 24.

    An kori mai tsaron ragar Liverpool Alisson Becker a minti na 76 bisa taba kwallo da ya yi da hannu a wajen yadi na 18. Minti biyu bayan haka kuma Dunk ya farke wa Brighton kwallo daya.

    Haka Liverppool ta ci gaba da kare gida har lafari ya tashi wasan.

    Idan Leicester City ta ci wasanta a gobe Lahadi za ta koma ta biyu a teburin kuma ta rage tazarar zuwa maki takwas maimakon 11 da ta bayar a yanzu.

  18. An tashi

    • Liverpool 2-1 Brighton
    • Chelsea 0-1 West Ham
    • Tottenham 3-2 Bournmouth
    • Burnley 0-2 Crystal Palace
  19. An tashi, Tottenham 3-2 Bournemouth

    Jinjina ga Mourinho da kuma tawagarsa.

    Nasara 3 a wasannin uku nasara 2 a premier.

  20. GOAL '90, Tottenham 3-2 Bournemouth

    Harry Wilson ya kara farke kwallo daya, sau ra daya wasan ya dawo danye.

    Abin tambayar anan shi ne, anya Jose zai kai bantensa kuwa?