Katin gargadi, Newcastle 1-1 Man City
An bai wa Fernandinho katin katinb gargadi bayan ya yi laifi.
Keta ya yi a wuri mai hadari ga Man City.
Jonjo Shelvey na Newcastle ya buga bugun tazara kuma ya yi kyau sosai.
Shafi ne da ke kawo maku rahotanni da sharhi kan wasannin Premier League kai-tsaye yayin da suke faruwa.
Buhari Muhammad Fagge and Umar Mikail
An bai wa Fernandinho katin katinb gargadi bayan ya yi laifi.
Keta ya yi a wuri mai hadari ga Man City.
Jonjo Shelvey na Newcastle ya buga bugun tazara kuma ya yi kyau sosai.
Gabriel Jesus ya yi satar gida

Asalin hoton, BBC Sport
Idan Newcastle ta ci wasan nan zai zama karon farko kenan da ta taba cin Man City wasa biyu a jere cikin shekara 17 a gasar Premier, bayan ta cinye City din 2-1 a watan Janairun da ya gabata.
Babu tabbas ko za ta ci wasan amma dai suna kokari sosai
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Jetro Willems ya kwanta rike da cikinsa bayan De Bruyne ya riba shi da kwallo a bakin ragarsu.
Sai da ya fita waje aka ba shi kulawa ta musamman.
Allan Saint-Maximin na kawo wa City barazana, yana budewa ya karbi kwallo ya ja Fernandinho a guje sai dai dan kasar Brazil din ya ki yarda da wayon.
Ya kwace kwallon cikin salon burgewa.
City na neman kari, sai dai Newcastle na nuna dagiya da jajircewa a wasan.
Raheem Sterling ya sheka wa Dubravka kwallo mai zafi amma mai tsaron ragar ya yi ta maza ya bige tare da rungume kayarsa.
Joelinton ya yi satar gida
Yau fa Saint-Maximin kawai kasuwarsa yake ci. Da kwallo ta je kafarsa ake fara ihu da shewa domin ana sa rai zai yi abin da ya kamata.
Jetro Willems ya farke wa Newcastle, cikin abin da ya gaza minti biyu Newcastle ta farke kwallon ta. Yanzu wasa ya dawo kunnen doki.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Ilkay Gundogan ya karbi katin gargadi.
Raheem Sterling ya yi abin da ya saba, ya jefa kwallo ta farko a yau cikin ragar Newcastle. kwallo ta takwas a Premier. kwallo ta 15 cikin wasa 20 da ya buga a kasarsa da kuma City.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Shelvey ya buga amma ta yi waje.
De Bruyne ya yi keta a wuri mai hadari Newcastle za ta yi bugun tazara.
Kwana mai kyau City ta samu Fernandinho ya sa mata kai, amma ta yi yawa ta fita waje.
Fernandez ya ceci Newcastle domin da Mahrez ya samu kwallon da ya ci.

Asalin hoton, BBC Sport
Kora mai kyau City ta dauka, Amma Shelvey ya kwace kwallon ya kuma tura wa mai taron raga Dubravka ya fidda ta.