Yadda aka fafata a wasannin Premier mako na 14

Shafi ne da ke kawo maku rahotanni da sharhi kan wasannin Premier League kai-tsaye yayin da suke faruwa.

Rahoto kai-tsaye

Buhari Muhammad Fagge and Umar Mikail

  1. An tashi, Liverpool 2-1 Brighton

    Liverpool ta sha da kyar. duk da cewa ta yi kokari na rike wasan bayan jan katin da aka bai wa mai tsaron ragarta.

  2. Chelsea 0-1 West Ham, Chelsea 0-1 West Ham

    Duka 'yan wasa 22 na dunkule a gidan West Ham har da mai tsaron ragar Chelsea amma har yanzu sakamakon da ake nema ya ki zuwa.

  3. Liverpool na bukatar nutsuwa, Liverpool 2-1 Brighton

    Brighton na kara matsawa cikin minti hudun da aka kara, domin samun nasarar farke kwallonta

  4. Jan katin Allison, Liverpool 2-1 Brighton

    Allison ne Mai tsaron ragarn Liverpool na farko da aka bai wa jan kati a Premier, tun Doni da aka bai wa a wasan Blackburn a watan Afrilun 2012.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  5. GOAL '78, Burnley 0-2 Crystal Palace

    Jeffrey Schlupp ne ya jefa ta biyu bayan da Zaha ya ci ta farko.

    Kyakkyawan sakamako ga Palace.

  6. Liverpool ta yi canji, Liverpool 2-0 Brighton

    Origi ya karbi Roberto Firmino, Adrian ya karbi Oxlade-Chamberlain.

  7. Sauyi karkashin Jose

    Moussa Sissoko ya ci kwallonsa ta farko a Premier cikin wasa 69 da ya buga, rabonsa da cin kwallo tun wadda ya ci Huddersfield a watan Satumbar 2017.

    Abin sha'awa.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  8. GOAL '79, Liverpool 2-1 Brighton

    Dunk ya farke wa Brighton kwallo daya bayan ya faki idon 'yan Liverpool ya buga wani bugun tazara ta tsakanin bangon da suka kafa.

  9. An bai wa Liverpool Jan kati, Liverpool 2-0 Brighton

    An kori mai tsaron ragar Liverpool Alisson Becker

  10. Kungiyoyin sun yi canji, Liverpool 2-0 Brighton

    An cire Mo Salah an saka Adam Lallana.

    Martin Montoya ya fita Steven Alzate ya shigo, Leandro Trossard ya cire Yves Bissouma.

  11. GOAL '69, Tottenham 3-0 Bournemouth

  12. GOAL VAR ta hana kwallon, Chelsea 0-1 West Ham

    Antonio ya taba kwallon da hannu kafin ta shiga raga.

  13. Chelsea ta yi canji biyu lokaci guda, Chelsea 0-1 West Ham

    Lampard ya sauya lissafin wasan, inda ya yi canji biyu lokaci guda.

    Willian ya karbi Pedro sai kuma Kante da ya karbi Jorginho.

  14. Wacce irin rashin sa a ce wannan, Burnley 0-1 Crystal Palace

    kwata kwata bai kamata a zubar da wannan damar ba, Chris Wood ya barar da dama mai kyau bayan da Cheikhou Kouyate ya mayar da wata kwallo gida da ka, bai san ya rufe kofa da barawo ba.

    Yana cikin kusan yadi na bakwai ko na takwas, babu kuma kowa a jikinsa, mai tsaron raga ne kawai ya rage ya yanka amma ya buga kwallon waje.

    Kashhhh.

  15. Katin gargadi, Chelsea 0-1 West Ham

    An bai wa Fornals na West Ham katin gargadi.

  16. Chelsea, Chelsea 0-1 West Ham

    Mai tsaron ragar Chelsea Kepa ya ture kwallo mai hadarin gaske ta-ci da aka bugo masa, sannan aka bugo kwana ya kuma tare wani harin na daban.

    Kila ya wanke kansa daga kuskuren da ya yi a tsakiyar mako a wasa tsakaninsu da Valencia, inda ya kyale kwallo ta shiga raga haka kawai, yana tunanin waje za ta fita ba raga ba.

  17. Liverpool 2-0 Brighton

    kadan ya hana Lewis Dunk ya farke wa brighton kwallo daya cikin biyun da aka ci ta.

    Alisson na jin jiki.

  18. Tottenham 2 - 0 Bournemouth, Tottenham 2 - 0 Bournemouth

    Tsaftataccen wasa da har yanzu babu katin gargadi cikinsa.

  19. GOAL '48 Alliiiii, Tottenham 2-0 Bournmouth

    Dele Alli yana wuta yau din nan. Ya ci ta biyu

    Alli ya ci biyu Tottenham ta ci biyu. Kai, Mourinho ma ya ci ma biyu!

  20. GOAL '47, Chelsea 0-1 West Ham

    Aaron Cresswell ne ya jefa kwallon, sai da ya yanka dan bayan ya nuna masa lanbar bayansa sannan ya sa kafar dama ya jefa kwallon kusurwar dama ta ragar Chelsea.

    Ko me Lampard zai yi domin rama kwallon nan? Kar ku nmanta babu Abraham a tawagar sannan kuma Willian yana benci har yanzu.