Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda aka fafata a wasannin Premier mako na 14
Shafi ne da ke kawo maku rahotanni da sharhi kan wasannin Premier League kai-tsaye yayin da suke faruwa.
Rahoto kai-tsaye
Buhari Muhammad Fagge and Umar Mikail
An take wasa, Chelsea 0-0 West Ham
Harry Kane
ya zuwa yanzu Harry Kane ya ci kwallo 23 cikin wasa 23 da ya buga a kungiyarsa da kuma kasarsa a wannan kakar.
Tawagar Tottenham
Jose Mourinho ya yi canji uku a tawagar da ta samu nasarar cinye Olympiakos a Champions.
Yan wasa:Gazzaniga, Aurier, Alderweireld,Sanchez, Vertonghen, Dier, Sissoko, Alli, Ndombele, Son, Kane
Yan canji:Whiteman, Rose, Winks, Walker-Peters, Lo Celso, Eriksen, Moura
Tawagar Bournemouth
Yan wasa: Ramsdale, S. Cook, Ake, Rico, Lerma, Solanke, C. Wilson, Danjuma Groeneveldm, L.Cook, Stacey, Rico, Fraser
Yan canji :Boruc,Gosling, H.Wilson, Simpson, Mepham, Kilkenny, Saydee
Newcastle ta rike wa Man City wuya, Newcastle 2-2 Man City
Tawagar Pep Guardiola ba ta iya samun nasara kan Newcastle masu masaukin baki ba duk da irin wasan da ta buga, inda wasa ya tashi 2-2 a filin wasa na St. James' Park.
Manchester City ce ta rike kashi 77% na wasan amma Newcastle ta nuna cewa a gidanta ake yin sa, inda Willems ya farke kwallon da Sterling ya ci cikin minti biyu kacal - bayan minti 22 da fara wasa.
Ana saura minti takwas a tashi daga wasan ne kuma Kevin De Bruyne ya kara ta biyu.
Nan take Newcastle ta yi wani babban yunkuri ta kafar Shelvey, inda ya shauda kwallo cikin ragar City ana saura minti biyu a tashi daga wasan, bayan wani bugun tazara da aka yaudari 'yan wasan City - maimakon a buga cikin raga sai aka bai wa Shelvy fasin.
Duk da canjaras din, Man City ta koma ta biyu a teburi amma fa kafin Leicester ta yi wasanta a gobe Lahadi.
Idan Liverpool ta ci wasanta tazara tsakaninta da City za ta zama maki 11 kenan, abin da ba zai yi wa mai horarwa Guardiola dadi ba musamman ganin yadda muke tunkarar watan Disamba, inda za a fara wassanni ba ji ba gani kuma kungiyoyi da dama za su san matsayinsu.
Wasanni na gaba:
- Liverpool 4:00 Brighton
- Chelsea 4:00 West Ham
- Tottenham 4:00 Bournmouth
- Burnley 4:00 Crystal Palace
- Southampton 6:30 Watford
Za mu kawo maku su duka a wannan shafin.
Tawagar Liverpool
Jurgen Klopp ya yi canji uku cikin tawagar da ta buga wasan Champion ta yi canjaras da Napoli.
Fabinho na jinyar raunin da ya ji, yayin da Joe Gomez da Milner suke benci.
Yan wasa :Alisson, Alexander-Arnold, Lovren, van Dijk, Robertson, Henderson, Wijnaldum, Oxlade-Chamberlain, Salah, Firmino, Mane.
Yan benci :Milner, Keita, Gomez, Adrian, Lallana, Shaqiri, Origi.
Tawagar Brighton
Canji hudu Brighton ta yi bayan kashin da ta sha har gida a hannun Leicester City da ci biyu ba ko daya ranar Asabar din da ta gabata.
Wannan ne zai zama wasa na biyu da aka fara da Yves Bissouma dan kasar Mali yayin da Lewis Dunk da Pascal Gross da kuma Aaron Connolly duk suke cikin wasan.
Yan wasa :Ryan, Montoya, Webster, Dunk, Burn, Bissouma, Stephens, Propper, Gross, Connolly, Mooy.
Yan canji :Duffy, Maupay, Trossard, Murray, Schelotto, Button, Alzate.
Jonjo Shelvey
An tanbayi Jonjo Shelvey game da kwallom da ya ci:
"Na san zan iya cin irinta saboda ina yawan gwadawa a filin atisaye"
An tashi kunnen doki, Newcastle 2-2 Man City
Wannan sakamako ba zai yi wa Guardiola dadi ba ko kadan.
Yanzu haka idan Liverpool ta ci wasanta, wanda za a take da karfe 4:00, ta bai wa City tazarar maki 11 kenan. Hakan na nufin City za ta fita daga cikin masu yunkurin lashe Premier.
Jonjo Shelvey, Newcastle 2-2 Man City
Nasan dai a yanzu duk inda magoya bayan Liverpool suke a duniya suna cike da farin ciki da abin da tsohon dan wasan kungiyar Jonjo Shelvey ya yi a yau.
GOAL '87 Shelvyyyyyy, Newcastle 2-2 Man City
Bugun tazara ne aka samu mai kyau, dan wasan da zai buga ya yi kamar cikin ragar City zai kwaso ta, kawai ya gara wa Jonjo Shelvey shi ko ya yi mata wani makahon bugu ba ta tsaya ko'ina ba sai cikin ragar City.
Ita ce kwallonsa ta farko a Premier ga Newcastle.
GOAL '81 De Bruyne, Newcastle 1-2 Man City
De Bruyne ya cika aiki!
Kwallo ya ajiye a kirjinsa kuma ya dada ta da kyau tun daga kusa da yadi na 23 - babu abin da mai tsaron raga Dubravka zai iya yi game da kwallon illa ta shiga rag bayan ta bugi turke na saman raga.
An saba gani da ma indai De Bruyne ne!
De Bruyne, Newcastle 1-1 Man City
Babu hagu ba dama da kowacce kafa De Bruyne harba kwallon yake, a iya wasannan ya buga shot ya kai hudu.
City ta yi canji, Newcastle 1-1 Man City
Riyad Mahrez ya fita Philip Foden ya shiga, haka shima David Silva ya bai wa Bernardo Silva ya dana.
Bernardo Silva, Newcastle 1-1 Man City
Bernardo Silva ya buga mai kyau a cikin yadi na 18 na Newcastle amma kwallo ta yi fadi.
Newcastle 1-1 Man City, Newcastle 1-1 Man City
City na ci gaba da kai hari, a lokaci daya Gabriel Jesus ya buga kwallo ba ta shiga ba mai tsaron raga Dubravka ya ciro ta haka shi ma De Bruyne ya kara amma duk da haka ba ta shiga ba.
Dole a jinjinawa Dubravka.
Manchester City, Newcastle 1-1 Man City
Yadda Manchester City take rike kwallo tare da gara kwallon a cikin filin ka iya cewa ba zai yiwu a tashi ba tare da ta ci wasan ba.
Amma kuma a lokaci guda Newcastle ba ta nuna gajiyawa ba domin kuwa ba ta fasa zuwa gindin ragar City ba.
Guardiola dai ba zai taba yin na'am da wani sakamako ba sabanin nasara musamman ganin halin da yake ciki a teburi.
Newcastle 1-1 Man City, Newcastle 1-1 Man City
Wanna ba karamin kokari Newcastle take ba. Raheem Sterling da David Villa na kokari suga sun fasa bayan Newscastle.
De Bruyne, Newcastle 1-1 Man City
De Bruyne ya sheka kwallo saman raga bayan wani shot da buga daga kusan yadi na 20.