Wolves 0-1 Sheff Utd
Wasannin Sheffield United a waje a Premier a bana
Bournemouth 1-1
Chelsea 2-2
Everton 2-0
Watford 0-0
West Ham 1-1
Tottenham 1-1
Wolves 1-0
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shafi ne da ke kawo maku rahotanni da sharhi kan wasannin Premier League kai-tsaye yayin da suke faruwa.
Buhari Muhammad Fagge and Umar Mikail
Wasannin Sheffield United a waje a Premier a bana
Bournemouth 1-1
Chelsea 2-2
Everton 2-0
Watford 0-0
West Ham 1-1
Tottenham 1-1
Wolves 1-0
Aubameyang ya buga finaritin farko ya zubar, alkalin wasa ya ce mai tsaron raga Krul ya baro layi kafin a buga, hakan yasa aka sake bugawa a karo na biyu kuma aka ci.
Aubameyang na da kwallo 11 kenan cif a Premier.
Sheffield United ta rike wasan yadda ya kamata. a wannan shekarar akwai wani abu tattare da Sheffield, matukar ta fara jan ragamar wasa da wahala a samu nasara kanta daga baya.
Teemu Pukki ya sakada wa Arsenal kwallo a zare - ita ce kwallonsa ta bakwai yanzu.
Wannan ba shi ne abin da magoya bayan Arsenal suka tsammata ba.
Freddie Ljungberg ya abin yake ne? Amma muna da sama da minti 60 a wasan ai.
McLean ya kai wani mummunan hari sai dai Leno na nutse ya kuma yi caraf da kwallon.
Yanayin yadda Arsenal ke kwallo a yau, irin yanayin da Tottenham ne ta tsinci kanta a wasan Mourinho na farko.
Matukar kwallon za ta ci gaba da tafiya a haka to da alamun nasara ga Arsenal.
Ya zuwa yanzu Sheffield United ta koma matsayi na 5 saman Tottenham a teburin gasar Premier,
Arsenal fa ta fara barin wuta a wasan nan - hari biyu lokaci guda daga Aubameyang da kuma Lacazette a cikin yadi na 18.
Arsenal ta bugo kwana ta farko kuma babu hadari ga Norwich.
Raul Jimenez ya ci kwallo a wasa uku da kungiyar ta buga a jere a Premier, dan wasa daya ne kawai a tarihin kungiyar ya taba ci a wasa hudu a jere a duka gasar da kungiyar ta buga Henri Camara, wanda ya ci kwallo a wasa biyar a jere a watan Afrilun 2004.
Lys Mousset ne ya bci kwallon - za ka yi mamakin abin da 'yan bayan Wolves suka tsaya yi har aka cilla masu kwallo a zare minti biyu kacal da take wasa.
An fara wasa da Granit Xhaka, wasansa na farko a Premier tun bayan canjin da aka yi masa a wasan da Arsenal ta buga da Crystal Palace a watan Oktoba.
Duk da dawowar Xhaka, Pierre-Emerick Aubameyang zai ci gaba da rike kambun kungiyar.
Yan wasa: Rui Patricio, Kilman, Coady, Dendoncker, Doherty, Jota, Neves, Joao Moutinho, Jonny, Traore, Jimenez.
Yan benci :Vallejo, Pedro Neto, Cutrone, Ruddy, Ruben Vinagre, Otasowie, Cundle.
Yan wasa :Henderson, Basham, O'Connell, Egan, Baldock, Lundstram, Fleck, Norwood, Stevens, McGoldrick, Mousset.
Yan canji :Luke Freeman, McBurnie, Sharp, Robinson, Jagielka, Moore, Besic.
Yan wasa XI:Krul; Aarons, Godfrey, Zimmermann, Byram; Trybull, Amadou; McLean, Cantwell, Hernandez; Pukki.
Yan canji :Fahrmann, Lewis, Stiepermann, Buendia, Vrancic, Roberts, Srbeny.
Yan wasa :Leno; Chambers, Mustafi, Luiz, Kolasinac; Guendouzi, Xhaka, Willock, Ozil; Lacazette, Aubameyang.
Yan canji :Martinez, Tierney, Sokratis, Torreira, Saka, Pepe, Martinelli.
Kocin rikon kwarya Freddie Ljungberg ya yi canji hudu cikin yan wasan tawagar da suka buga canjaras da Southampton a makon jiya.
Granit Xhaka zai fara buga wasansa na farko a Premier tun bayan canjin da aka yi masa a wasan da Arsenal ta buga da Crystal Palace a watan Oktoba.
Duk da dawowar Xhaka, Pierre-Emerick Aubameyang zai ci gaba da rike kambun kungiyar.
Sakamakon da Southampton suka fi ya samu.