Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yadda aka fafata a wasannin Premier mako na 14

Shafi ne da ke kawo maku rahotanni da sharhi kan wasannin Premier League kai-tsaye yayin da suke faruwa.

Rahoto kai-tsaye

Buhari Muhammad Fagge and Umar Mikail

  1. Arsenal ta yi canji, Norwich 2-2 Arsenal

    Lucas Torreira ya karbi Joseph Willock, sai kuma Bukayo Saka da ya karbi Matteo Guendouzi

  2. Matt Doherty, Wolves 1-1 Sheff Utd

    Kwallon kai ce Matt Doherty ya ci, ya kuma yi murnar kwallon ne da nuna sama domin nuna ta'aziyya da mutuwar 'yar Benik Afobe mai shekaru 2 da ta mutu ranar juma'a.

  3. Cantwell, Norwich 2-2 Arsenal

    Cantwell ya matsa wa Arsenal, matashin dan wasan nan fa da alama zai kara ta uku indai tsakiyar Arsenal ta ci gaba da barinsa yana warkajami irin wannan.

    Ya kuma kai hari mummuna kuma ba don Mustafi ba da shikenan!

  4. Aubameyang, Norwich 2-2 Arsenal

    Aubameyang ya ci kwallo 10 cikin wasa 11 da ya buga da sabbin kungiyoyin da suka hawo gasar Premier.

  5. GOAL '64, Wolves 1-1 Sheff Utd

  6. Cantwellllll, Norwich 2-2 Arsenal

    Cantwell ya sake sheka wata kwallo mai kyau daga yadi na 19 - saura kiris ya ci ta biyu domin kuwa golan kallonta kawai ya yi.

  7. Aubameyang, Norwich 2-2 Arsenal

    Aubameyang ya zama a-ci-kullum.

  8. Leno ya ceci Arsenal, Norwich 2-1 Arsenal

    Mai tsaron ragar Arsenal Leno ya tare kwallon da aka dada masa mai hadarin gaske.

    An bugo kwana ya sake bige ta. Kokarinsa ya yi wa Arsenal kyau.

  9. GOAL '57, Norwich 2-2Arsenal

    Kwallo ta biyu ga Arsenal a yau.

    kwallo ta biyu ga sabon kocin rikon kwarya FreddieL jungberg.

    Kwallo ta 10 ga Aubameyang.

  10. Mai tsaron raga Krul, Norwich 2-1 Arsenal

    Krul ya buge finareti da yawa a baya-bayan nan - ya buge wa Rashford da Martial - yanzu kuma ya buge wa Aubameyang.

    Sai dai alkalin wasa ya ce ya baro layi kafin a buga, aka sake bugawa kuma aka cinye shi.

  11. Wasa ya ci gaba, Norwich 2-1 Arsenal

    Ko Norwich za ta ririta wannan kwallo biyun?

    Za mu gani dai, amma Arsenal har yanzu labari daya take bayarwa. Tabbas Emery ya tafi amma Arsenal na nan.

  12. Todd Cantwell, Norwich 2-1 Arsenal

    Wannan ne karo na biyu da Todd Cantwell ya ci kwallo a wasa biyu a jere ga Norwich City, kuma kwallo biyu kacal ya ci a wasan Premier 25 vda ya buga wa kungiyar tasa - ya saka Arsenal a tarihinsa kenan.

  13. Norwich ta gano inda Arsenal ke da baraka, Norwich 2-1 Arsenal

    Bangaren lamba biyun Arsenal a bude yake shi yasa Norwich ke amfani da wajen tana jefa kwallo. duka biyun da aka ci tanan aka ci su/.

  14. Yana nan tafe anjima, Man Utd v Aston Villa

  15. An tafi hutun rabin lokaci, Wolves 0-1 Sheff Utd

    Minti 45 na farko ya yiwa Sheffield dadi.

  16. An tafi hutun rabin lokaci, Norwich 2-1 Arsenal

  17. GOAL '45+1, Norwich 2-1 Arsenal

    Wannan wace irin kwallo Cantwell ya ci! Kai jama'a!

    Kwallo ce mai matukar kyau a tsakar yadi na 18 na Arsenal. Sheka kwallon ya yi cikin kwarewa bayan an ba shi ita daga bangaren hagu. Babu abin da Leno ya iya wajen hana ta shiga lokon dama na ragarsa.

  18. Katiun gargadi, Norwich 1-1 Arsenal

    Mc Lean ya karbi katin gargadi bisa ketar da ya yi wa Guendouzi.

  19. Bajintar Aubameyang, Norwich 1-1 Arsenal

    Aubameyang ya ci kwallo 27 a wasannin Premier da ya buga ranar Lahadi, sama da duk wani dan wasa tun da ya fara buga gasar, (Salah ya ci 26 a wasannin ranar Asabar).

    Takwas daga cikin kwallo 11 da Arsenal ta ci a waje Aubameyang ne ya ci su.

  20. Kwanar farko ga Norwich, Norwich 1-1 Arsenal

    Norwich ta buga kwana ta farko a wasan, sai dai ba ta amfana da ita ba.

    Kwallo ta fita kuma Arsenal ta yi bugun gida