Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yadda aka fafata a wasannin Premier mako na 14

Shafi ne da ke kawo maku rahotanni da sharhi kan wasannin Premier League kai-tsaye yayin da suke faruwa.

Rahoto kai-tsaye

Buhari Muhammad Fagge and Umar Mikail

  1. Katin gargadi, Newcastle 1-1 Man City

    An bai wa Fernandinho katin katinb gargadi bayan ya yi laifi.

    Keta ya yi a wuri mai hadari ga Man City.

    Jonjo Shelvey na Newcastle ya buga bugun tazara kuma ya yi kyau sosai.

  2. Satar gida, Newcastle 1-1 Man City

    Gabriel Jesus ya yi satar gida

  3. An dawo daga hutun rabin lokaci, Newcastle 1-1 Man City

  4. Rawar da suka taka, Newcastle 1-1 Man City

  5. An tafi hutun rabin lokaci, Newcastle 1-1 Man City

    Idan Newcastle ta ci wasan nan zai zama karon farko kenan da ta taba cin Man City wasa biyu a jere cikin shekara 17 a gasar Premier, bayan ta cinye City din 2-1 a watan Janairun da ya gabata.

    Babu tabbas ko za ta ci wasan amma dai suna kokari sosai

  6. Willems a kwance, Newcastle 1-1 Man City

    Jetro Willems ya kwanta rike da cikinsa bayan De Bruyne ya riba shi da kwallo a bakin ragarsu.

    Sai da ya fita waje aka ba shi kulawa ta musamman.

  7. Newcastle 1-1 Man City, Newcastle 1-1 Man City

    Allan Saint-Maximin na kawo wa City barazana, yana budewa ya karbi kwallo ya ja Fernandinho a guje sai dai dan kasar Brazil din ya ki yarda da wayon.

    Ya kwace kwallon cikin salon burgewa.

  8. Newcastle 1-1 Man City, Newcastle 1-1 Man City

    City na neman kari, sai dai Newcastle na nuna dagiya da jajircewa a wasan.

  9. Sterling, Newcastle 1-1 Man City

    Raheem Sterling ya sheka wa Dubravka kwallo mai zafi amma mai tsaron ragar ya yi ta maza ya bige tare da rungume kayarsa.

  10. Satar gida, Newcastle 1-1 Man City

    Joelinton ya yi satar gida

  11. Newcastle 1-1 Man City, Newcastle 1-1 Man City

    Yau fa Saint-Maximin kawai kasuwarsa yake ci. Da kwallo ta je kafarsa ake fara ihu da shewa domin ana sa rai zai yi abin da ya kamata.

  12. GOAL '23, GOAL '21 Newcastle 1-1 Man City

    Jetro Willems ya farke wa Newcastle, cikin abin da ya gaza minti biyu Newcastle ta farke kwallon ta. Yanzu wasa ya dawo kunnen doki.

  13. Katin gargadi, Newcastle 0-1 Man City

    Ilkay Gundogan ya karbi katin gargadi.

  14. GOAL '21, Newcastle 0-1 Man City

    Raheem Sterling ya yi abin da ya saba, ya jefa kwallo ta farko a yau cikin ragar Newcastle. kwallo ta takwas a Premier. kwallo ta 15 cikin wasa 20 da ya buga a kasarsa da kuma City.

  15. Newcastle 0-0 Man City, Newcastle 0-0 Man City

    Shelvey ya buga amma ta yi waje.

  16. Bugun tazara, Newcastle 0-0 Man City

    De Bruyne ya yi keta a wuri mai hadari Newcastle za ta yi bugun tazara.

  17. Newcastle 0-0 Man City, Newcastle 0-0 Man City

    Kwana mai kyau City ta samu Fernandinho ya sa mata kai, amma ta yi yawa ta fita waje.

  18. Newcastle 0-0 Man City, Newcastle 0-0 Man City

    Fernandez ya ceci Newcastle domin da Mahrez ya samu kwallon da ya ci.

  19. Rawar da kowacce kungiya ta taka zuwa yanzu, Newcastle 0-0 Man City '16

  20. Newcastle 0-0 Man City, Newcastle 0-0 Man City

    Kora mai kyau City ta dauka, Amma Shelvey ya kwace kwallon ya kuma tura wa mai taron raga Dubravka ya fidda ta.