Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yadda aka fafata a wasannin Premier mako na 14

Shafi ne da ke kawo maku rahotanni da sharhi kan wasannin Premier League kai-tsaye yayin da suke faruwa.

Rahoto kai-tsaye

Buhari Muhammad Fagge and Umar Mikail

  1. Man Utd 1-1 Aston Villa, Man Utd 1-1 Aston Villa

    Aston Villa ta buga kwallo a minti 45 din farko, amma yanzu ta koma baya abin da yasa United ta kara matsa lamba domin samun kwallo ta biyu.

  2. Hari mai kyau, Leicester 0-1 Everton

    Ricardo Pereira ya kutsa kuma ya buga kwallon Jordan Pickford ya kasa rike ta ya watso ta daga kirjinsa sai dai babu kowa da zai kara.

  3. Keane, Leicester 0-1 Everton

    Michael Keane ya samu kwallo a cikin yadi na shida amma mai tsaron raga Schmeichel ya damke ta bayan Kean din ya saka mata kai.

  4. Martial, Man United 1-1 Aston Villa

    Martial ya dada kwallo amma ta daki jikin dan bayan Villa zuwa bugun kwana.

    An bugo kwana amma Maguire ya yi laifi kuma Villa ta buga kwallo.

  5. Leicester 0-1 Everton, Leicester 0-1 Everton

    James Maddison na iya kokarinsa amma kwallon taki bashi hadin kai.

  6. An dawo daga hutun rabin lokaci, Man United 1-1 Aston Villa

  7. Mummunan labari, Man United 1-1 Aston Villa

    Bayan dogon nazari, mahukuntan Premier League sun kwace kwallon da aka bai wa Rashford an bai wa mai tsaron raga Tom Heaton a matsayin wanda ya ci gida.

  8. An tafi hutun rabin lokaci, Man Utd 1-1 Aston Villa

    Grealish ne ya ci wa Villa, sannan kuma Tom Heaton ya ci gida, kamar yadda hukumar Premier League ta bayyana - ba Rashford ne ya ci ba.

  9. An tafi hutun rabin lokaci, Leicester 0-1 Everton

  10. Katin gargadi, Man Utd 1-1 Aston Villa

    Guilbert ya karbi katin gargadi sakamakon keta da ya yi wa Williams na Man United.

  11. Katin gargadi '45+2, Leicester 0-1 Everton

    An bai wa Gylfi Sigurdsson katin gargadi, kuma kati na farko a wasan.

  12. Leicester 0-1 Everton, Leicester 0-1 Everton

    Leicester ta matsa tana neman zare kwallon da aka zira mata.

  13. GOAL '41, Man Utd 1-1 Aston Villa

    Rasahford ya ci gaba da taimaka wa United kamara yadda aka saba.

    Ya goga wa kwallo kai ta shiga raga bayan Pereira ya murzo masa ita daga bangaren dama.

    Kwallo ta takwas kenan ga Rashford a Premier ta bana.

  14. Leicester 0-1 Everton

    Everton ta ci wasa tara da ta buga a Premier wanda ta fara zura kwallo.

  15. Babu Finareti, Leicester 0-1 Everton

    An kwace Finaretin da aka bai wa Leicester.

  16. An bai wa Leicester City finareti, Leicester 0-1 Everton

  17. Rashford, Man Utd 0-1 Aston Villa

    Marcus Rashford ya kai hari amma kwallo ta yi fadi.

  18. katin gargadi, Man Utd 0-1 Aston Villa

    An bai wa Fred katin gargadi.

  19. GOAL '24, Leicester 0-1 Everton

    Alex Iwobi ne ya debo kwallon, inda shi kuma Richarlison ya damfara ta da ka.

    Idan aka tashi a haka, wannan ne karon farko da za a samu nasara a kanta a gidanta a wasan Premier bana.

  20. Canji, Man Utd 0-1 Aston Villa

    Manchester United ta sha mamaki da kwallon da Jack Grealish ya cilla mata a raga mai kyan gaske, sai dai hakan ya jawo wa Aston Villa yin canji da wuri saboda Anwar El Ghazi ya ji wa kansa rauni a ruguntsumin cin kwallon.

    Trezeguet ya karbe shi.