Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yadda aka fafata a wasannin Premier mako na 14

Shafi ne da ke kawo maku rahotanni da sharhi kan wasannin Premier League kai-tsaye yayin da suke faruwa.

Rahoto kai-tsaye

Buhari Muhammad Fagge and Umar Mikail

  1. Leicester City tana jan zarenta a kakar bana, Leicester City 0-0 Everton

    Har yanzu ba a ci Leicester City a gidanta ba (King Power Stadium) a kakar bana.

    Saboda haka yau Everton sai ta yi da gaske za ta kawo karshen wannan bajintar.

  2. GOAL '11, Man Utd 0-1 Aston Villa

    Da wuri haka!

    Jack Grealish ne ya murda kwallon bayan ya yanka Pereira.

    De Gea ya zama tamkar hoto, kawai sai juyawa ya yi ya ga kwallon a raga.

  3. Man Utd 0-0 Aston Villa, Man Utd 0-0 Aston Villa

    Fred ya buga kwallon amma ta yi sama.

    Manchester United na buga wasa kamar dai kullum, amma sakamakon karshe ke tabbatar da jajaurcewa kungiyar.

  4. Manchester United, Man Utd 0-0 Aston Villa

    Manchester United ta ci wasa 34 a baya da ta buga da Aston Villa a Premier/.

    Everton ce kadai ta fi Aston Villa shan kashi a hannun man United a Premier (36) - ita ce nasara mafi girma da wani kulob ya samu a kan wani.

  5. Katiun gargadi, Man Utd 0-0 Aston Villa

    An bai wa Maguire katin gargadi

  6. Man Utd 0-0 Aston Villa, Man Utd 0-0 Aston Villa

    Dama ce ga Ole Gunnar Solskjaer idon ya ci wannan wasa zai koma matsayi na 5 a Premier.

  7. An take wasa, Leicester 0-0 Everton

  8. An take wasa, Man Utd 0-0 Aston Villa

  9. Yau ko Vardy zai iya cin kwallo?

    Vardy ya ci kwallo 12 cikin wasa 12 na Premier da ya buga.

  10. Wolves, Wolves 1-1 Sheff Utd

    Wasa tara Wolves ta yi ba a samu nasara a kanta ba, wanda wannan shi ne tarihi mafi tsayi da ta kafa tun bayan wanda ta yi a watan Afrilun 1973.

  11. Saura wasa biyu

    Yanzu saura Manchester United vs Aston Villa da kuma Leicester City vs Everton.

    Karfe 5:30 za take wasannin biyu.

  12. Wasa ya kare, Norwich 2-2 Arsenal

    An tashi daga wasa. Labarin dai yana nan kamar yadda aka saba a Arsenal.

    Shi ma sabon koci Freddie Ljunberg ya shiga cikin tarihin, kodayake da ma daga nan ya fito.

  13. An tashi daga wasa, Wolves 1-1 Sheff Utd

    Anya wadannan biyun ba za su buga Europa ba a gasa mai zuwa?

  14. Arsenal na ganin azaba a mintin karshe, Norwich 2-2 Arsenal

    Hare-hare uku a jere cikin kasa da minti biyar - Arsenal na ganin azaba a mintin karshe.

  15. Tawagar Leicester City

    Yan wasa: Schmeichel; Pereira, Evans, Soyuncu, Chilwell; Ndidi, Tielemans; Perez, Maddison, Barnes; Vardy.

    Yan canji:Ward, Justin, Morgan, Choudhury, Praet, Albrighton, Iheanacho.

  16. Aarons, Norwich 2-2 Arsenal

    Saura kiris Aarons na Norwich ya ci kwallo a mintunan karshen nan

  17. Ozil ya fita, Norwich 2-2 Arsenal

    Mortinelli ya karbi Mesut Ozil.

  18. Tawagar Everton

    Marco Silva dake cikin matsin rashin kokari ya yi canji uku cikin tawagar Everton da suka yi wasa da Norwich makon jiya.

    Yan wasa :Pickford; Holgate, Keane, Mina; Sidibe, Davies, Sigurdsson, Digne; Iwobi, Richarlison, Calvert-Lewin.

    Yan canji:Lossl, Baines, Gordon, Schneiderlin, Bernard, Kean, Tosun.

  19. Wasa yana wuta, Norwich 2-2 Arsenal

    Wasa ya dauki zafi sosai yayin da ya rage saura kasa da minti biyar a tashi kuma Arsenal ake buga wa kwallo a 'yan tsakjanin nan.

  20. Norwich ta yi canji, Norwich 2-2 Arsenal

    Matashin dan wasa Todd Canbtwell ya fita, inda Emiliano Buendi ya karbe shi.