Tawagar Tottenham
Yan wasa :Gazzaniga, Aurier, Sanchez, Dier, Davies, Sissoko, Ndombele, Lo Celso, Alli, Son, Kane.
Yan benci :Vorm, Alderweireld, Winks, Sessegnon, Foyth, Eriksen, Moura.

Asalin hoton, BBC Sport
Muna kawo maku sharhi da rahotanni kai-tsaye game da wasannin kwallon kafar Ingila na Premier League.
Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge
Yan wasa :Gazzaniga, Aurier, Sanchez, Dier, Davies, Sissoko, Ndombele, Lo Celso, Alli, Son, Kane.
Yan benci :Vorm, Alderweireld, Winks, Sessegnon, Foyth, Eriksen, Moura.

Asalin hoton, BBC Sport
Yan wasa :Henderson, Basham, Egan, O’Connell, Baldock, Lundstram, Norwood, Fleck, Stevens, Mousset, McGoldrick.
Yan bencii :Moore, Freeman, McBurnie, Sharp, Robinson, Jagielka, Besic.

Asalin hoton, BBC Sport
Tawagar Frank Lampard ta zama ta biyu a saman teburin Premier bayan ta lallasa Crystal Place da ci 2-0 a filin wasa na Stamford Bridge.
Dawowar dan wasa Ngolo Kante ya taimaka wa tsakiyar Chelsea sosai, ganin yadda da ma aka dakatar da Jorginho daga taka-leda.
Wannan shi ne wasa na shida da Chelsea ta ci a jere, abin da ya ba ta damar darewa mataki na biyu a teburi da maki 26 cikin wasa 12.
Tammy Abraham dan kasar Ingila ne ya bude wasan da kwallonsa ta farko, wadda ya ci bayan Willian ya ba shi ita a cikin yadi na 18 din Crystal Palace.
Kazalika, Abraham ya zama dan wasa mafi karancin shekaru da ya ci wa Chelsea kwallo sama da 10 a Premier- shekarunsa 22.
Sai a minti na 79 ne Christian Pulisic dan kasar Amurka ya jefa ta biyu - Zouma ne ya hango shi a cikin yadi na 18 din Palace, inda shi kuma ya goga mata kai kuma ta gangare zuwa cikin raga ba tare da mai tsaron Guita ya iya yin komai ba.

Asalin hoton, Getty Images
Yan wasa :McCarthy, Soares, Bednarek, Stephens, Vestergaard, Djenepo, Ward-Prowse, Romeu, Armstrong, Ings, Redmond.
Yan benci: Yoshida, Adams, Boufal, Obafemi, Gunn, Danso, Valery.

Asalin hoton, BBC Sport
Yan wasa: Pickford, Sidibe, Mina, Holgate, Digne, Schneiderlin, Davies, Walcott, Sigurdsson, Richarlison, Tosun.
Yan benci: Baines, Keane, Calvert-Lewin, Iwobi, Coleman, Lossl, Gordon.

Asalin hoton, BBC Sport
Yan wasa :Dubravka, Yedlin, Fernandez, Lascelles, Clark, Willems, Almiron, Hayden, Shelvey, Saint-Maximin, Joelinton.
Yan canji : Dummett, Carroll, Gayle, Krafth, Darlow, Atsu, Matthew Longstaff.

Asalin hoton, BBC Sport
Yan wasa :Ramsdale, Smith, Steve Cook, Ake, Rico, Harry Wilson, Lewis Cook, Billing, Fraser, Callum Wilson, King.
Yan benci: Boruc, Francis, Gosling, Solanke, Danjuma, Stacey, Mepham.

Asalin hoton, BBC Sport
Muna da wasanni 4 na gasar Premier da za mu kawo maku kai-tsaye. Dukkansu za a take da 4:00:
Burnley vs West Ham United
Newcastle United vs AFC Bournemouth
Southampton vs Everton
Tottenham Hotspur vs Sheffield United
Wasan ya yi kama da na Newcastle da Brighton. Chelsea ta nuna hakuri da juriya kuma ta matsa lamba yadda ya kamata a karshe kuma nasara ta zo.

Asalin hoton, Getty Images
Ta faru ta kare an yi wa mai dami daya sata. Chelsea ta ci wasanta na shida a jere a Premier.
Yanzu haka tawagar Lampard din ce ta biyu a teburi kafin Man City ta farje gumi da Liverpool a gobe Lahadi.
An bai wa McCarthy katin gargadi bisa keta da ya yi wa Kovacic.
An kara minti hudu kan minti 90 da aka shafe ana fafatawa.
kiris ya hana Michy Batshuayi ya kara kwallo ta uku.
Matashin dan wasa Billy Gilmour ya karbi Mason Mount.
Shekarunsa 18, kuma wannan ne wasansa na farko a Premier. Sai dai ya buga wa kungiyar wasa a watan Agusta, inda ya buga minti 7 kacal.
Ga abin da shafin Chelsea na 'yan Amurkar ke cewa:
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Chelsea ta buga wasa biyu a Premier ta bana ba a jefa mata kwallo ba, ga ta a kan hanayar wasa na uku, amma fa sai idan an tashi Palace ba ta zare kwallonta ba.
Christian Pulisic ya fita yayin da Callum Hudson Odoi ya karbe shi.
Pulisic ya jefa kwallo ta biyu.
Wannan ce kwallonsa ta biyar a cikin wasa uku da ya buga wa Chelsea. Dan kasar Amurkan yana wuta kwana biyu.
Yanayin matasan 'yan kwallon da ke Chelsea da yadda suke taka leda na kara burge magoya bayan kungiyar.
Michy Batshuayi ya karbi Tammy Abraham wanda ya jefa kwallo.