Yadda kungiyoyi suka barje gumi a wasannin Asabar

Muna kawo maku sharhi da rahotanni kai-tsaye game da wasannin kwallon kafar Ingila na Premier League.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge

  1. , Tottenham 1-1 Sheffield United

    Tottenham na ta kokarin ganin ta samu kwallo a karshen lokaci, sai dai Sheffield na kara nuna juriya da kokarin tsare bayanta.

  2. Richarlison, Southampton 1-2 Everton

    Ana ta yi wa Richarlison ihu a filin wasa na St Mary, sai dai bai damu ba.

    kwallon da ya ci ce ta baiwa Everton damar jan ragamar wasan.

  3. Karin lokaci, Tottenham 1-1 Sheffield United

    An kara minti 6 bayan cikar lokaci.

  4. Newcastle ta yi canji, Newcastle 2-1 Bournemouth

    Jonjo Shelvey ya fita Andy Carroll ya shigo

  5. West Ham, Burnley 3-0 West Ham

    West Ham ta mamaye wasan tana da kaso 62 cikin dari na rike kwallo, sai dai kuma tana ruwa saboda wasanta biyu da za ta buga a gaba, bayan dawo wa daga hutu, za ta karbi bakuncin Tottenham ne ta kuma je gidan Chelsea.

  6. Lucas Moura ya shigo, Tottenham 1-1 Sheffield United

    Lucas Moura ya karbi Aurier ana saura minti hudu minti 90 ya kare.

    Ba abin mamaki ba ne ya sauya kwallon idan muka tuna rawar da ya taka a gasar Champions League ta bara tsakaninsu da Ajax.

  7. Southampton 1-2 Everton, Southampton 1-2 Everton

    Iwobi ya kara karfafa Everton bayan shigowarsa,

  8. GOAL, Southampton 1-2 Everton

    Richarlison ya farke wa Everton.

    Everton ta samu nata gwarzon.

    kocin Everton Marco Silva na cike da farin ciki.

  9. GOAL '77 Sheffield United, Tottenham 1-1 Sheffield United

    Sheffield United ta farke kwallonta ta kafar George Baldock.

  10. Dalilin da yasa aka soke kwallon Sheffield, Tottenham 1-0 Sheffield United

    Hukumar shirya Premier League ta ce an hana kwallon da Sheffield United ta ci ne bayan na'urar VAR ta gano cewa John Lundstram ya yi satar gida tun a farkon wasan kafin shigra kwallo cikin raga.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  11. Everton ta yi canji, Southampton 1-1 Everton

    Theo Walcott ya fita Alex Iwobi ya shiga.

  12. Southampton 1-1 Everton, Southampton 1-1 Everton

    Meke faruwa da Everton ne?

    Jordan Pickford ya ture bugun tazara da ames Ward-Prowse ya yi, wanda bugun shi ke da matukar hadari.

    Southampton na ci gaba da iza wuta.

  13. Son ya kai kora, Tottenham 1-0 Sheffield United

    Son ya kusa kara ta biyu - ya shiga da kwallo cikin yadi na 18 din Sheffield amma 'yan baya sun hana shi sakat, ya buga kwallon waje amma yana kukan an yiu masa keta ne.lafari ya ce ba a yi masa komai ba.

  14. Burnley 3-0 West Ham, Burnley 3-0 West Ham

    Wasan bai yi wa Manuel Pellegrini kyau ba, amma har yanzu akwai kusan minti 30 sai dai duk da haka Burnley ce ke jan ragamar wasan.

  15. Ayya! VAR ta hana kwallo GOAL '59, Tottenham 1-0 Sheffield United

    Sheffield ta farke kwallo amma sai dai VAR ta ce an yi satar gida.

  16. GOAL, Burnley 3-0 West Ham

    Roberto Jimenez ya ci gida, dama shi ne ke ta kokari a bayan West Ham din.

    To yanzu mai zai faru tun da ya ballo ruwa? watakila hakan ya sa ya rage kokari.

  17. GOAL, Newcastle 2-1 Bournemouth

    Ciaran Clark ya kara zira kwallo ta biyu. yanzu Newcastle ke kan gaba.

  18. Ayya! VAR ta hana kwallo GOAL '59, Tottenham 1-0 Sheffield United

    Sheffield ta farke kwallo amma sai dai VAR ta ce an yi satar gida.

  19. GOAL '58, Tottenham 1-0 Sheffield United

  20. Southampton 1-1 Everton, Southampton 1-1 Everton

    Shot na biyu da Southampton ta buga ke nan a wasan duka kuma ta samu nasarar farkewa, Danny Ings da James Ward-Prowse ne suka zira wa kungiyar kwallo 6 na karshe da ta ci a gasar Premier ko wanne daya ya ci uku.