Muna kawo maku sharhi da rahotanni kai-tsaye game da wasannin kwallon kafar Ingila na Premier League.
Rahoto kai-tsaye
Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge
Leicester City 0-0 Arsenal, Leicester City 0-0 Arsenal
An buda wasan sosai da yuyuwar zira kwallaye da yawa a yau, Jamie Vardy ne ke yawan kai hari ta bangaren dama,
A very watchable opening 25 minutes, but still level.
Minti 25 din farko da ake bugawa babu tsoro sai dai har yanzu babu kwallo.
Leicester City 0-0 Arsenal, Leicester City 0-0 Arsenal
Dama guda biyu a jere Leicester city ta samu sai dai babu wadda ta iya ci a ciki.
GOAL La Liga '20, Eibar 0 - 2 Real Madrid
Sergio Ramos ya kara ta biyu a raga.
GOAL '17 La Liga, Eibar 0 - 1 Real Madrid
K. Benzema ya jefa kwallo
Leicester City 0-0 Arsenal, Leicester City 0-0 Arsenal
Lacazette ya barar da dama mai kyau a tsakiyar yadi na 16.
Leicester City 0-0 Arsenal, Leicester City 0-0 Arsenal
Tsakanin Pierre-Emerick Aubameyang da Jamie Vardy waye zai fara zira kwallo?
Leicester 0-0 Arsenal, Leicester 0-0 Arsenal
Minti 11 kuma har ya zuwa yanzu kwallon ba ta gama warwarewa ba.
Leicester City 0-0 Arsenal, Leicester City 0-0 Arsenal
Asalin hoton, BBC Sport
Bayanan hoto, Arsenal
Asalin hoton, BBC Sport
Bayanan hoto, Leicester
Wasa na gaba, Leicester City 0-0 Arsenal
Leicester City ce take karbar bakuncin Arsenal a filin wasa na King Power.
Tottenham ta gaza cin wasa a gidanta, Tottenham 1-1 Sheffield United
Tottenham ta ci gaba da shiga tasku yayin da ta gaza cin wasan mako na 12 bayan wasa ya tashi 1-1 tsakaninta da Sheffield United a filin wasa na Tottenham Hotspur.
Ba don na'urar VAR ba ma da tuni an cinye masu masaukin bakin, domin kuwa David McGoldrick ya ci kwallo a minti na 59 amma sai aka ce ya yi satar gida.
Kazalika, wannan ne karon farko da Tottenham ta gaza kai hari na-ci a wasan Premier da take bugawa a gidanta a minti 45 na farkon wasa.
Mai masaukin bakin ba ta iya kai wani harin kirki ba har sai a minti na 58 lokacin da Son Heung-Min ya ci kwallon farko.
Sheffield United ba ta yi kasa a gwiwa ba har sai da ta rama minti biyu kacal a tsakani, abin da ya nuna irin jajircewarsu a wasan.
Wannan sakamakon ya sa Tottenham ta koma matsayi na 12 da maki 14, maki 9 kenan tskaninta da 'yan hudun farko da ke saman teburin gasar.
Asalin hoton, Getty Images
Tom Davies, Southampton 1-2 Everton.
Dan wasan tsakiyar everton Tom Davies "Ba karamar nasara ba ce - wannan ita ce nasarar farko da muka samu a wasan waje a wannan kakar wasannin, kuma munyi amfani da damar."
"Matasan yan wasanmu sun taimaka wajen samun nasarar, dukan mu muna cike da murna."
"Dukan mu muna cike da rashin jin dadin abin da ya faru ga Andre Gomes, muna da fatan taimaka masa ta hanyar sa shi farin ciki, nasarar ba karamin abu bane, saboda akwai damuwa raunin da Gomes din ya ji."
Sakamakon wasannin yau, Premier
Chelsea 2-0 Crystal Palace.
Burnley 3-0 West Ham United.
Newcastle United 2-1 AFC Bournemouth.
Southampton 1-2 Everton.
Tottenham Hotspur 1-1 Sheffield United.
Wasannin Premier, Leicester City vs Arsenal
Wasan na nan tafe nan da karfe 6:30..... ku kasance tare da mu.