Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Bayanai da rahotanni kan zaben Najeriya na 2019

Wannan shafi na kawo muku yadda jama'a ke bayyana murna kan lashe zaben Najeria da shugaba Muhammadu Buhari ya yi.

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau and Mohammed Abdu

  1. Gwamna Ganduje ya kada kuri'a

    Lokacin da Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya kada kuri'a.

  2. Osinbajo ya kada kuri'a

    Lokacin da mataimakin shugaban kasar Nigeria, Yemi Osinbajo ya kada kuri'a.

  3. Ahmed Aliyu ya kada kuria'a

    Dantakarar Gwamna a jamiyar APC a jihar Sokoto Ahmad Aliyu Sokoto yayin da yake kada kuriar sa a rumfar zabe mai lamba 19B a makarantar magajin Rafi sokoto.

  4. Lokacin da El Rufa'i ke layin zabe

  5. Ina sa ran za a samu sauyin gwamnati cikin lafiya - Atiku

    Dan takarar shugaban Najeriya na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya ce a matsayinsa na mai fafutikar ganin an wanzar da mulkin dimokradiyya, zai yi biyayya ga sakamakon zaben shugaban kasar.

    Ya bayyana haka ne bayan ya kada kuri'arsa a birnin Yola na jihar Adamawa.

    Tsohon mataimakin shugaban kasar ya je wurin kada kuri'arsa ne tare da mai dakinsa, Hajiya Titi Atiku.

    "Ina sa ran za a samu sauyin gwamnati cikin lafiya", in ji Atiku.

    Da aka tambaye shi ko zai amince idan ya sha kaye, sai ya ce "Ni mai fafutukar kare dimokradiyya ne".

  6. Labarai da dumi-dumi, Atiku ya kada kuri'arsa

    Dan takarar shugaban Najeriya na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya kada kuri'arsa a birnin Yola na jihar Adamawa.

    Tsohon mataimakin shugaban kasar ya je wurin kada kuri'arsa ne tare da mai dakinsa, Hajiya Titi Atiku.

  7. Goodluck Jonathan ya kada kuri'arsa

    Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya kada kuri'arsa a jiharsa ta Bayelsa da ke kudu maso kudancin kasar.

    Bayan zaben, bai fadi mutumin da ya zaba ba, inda ya gaya wa manema labarai cewa idan ya fadi mutumin da ya zaba wasu za su fassara hakan da cewa tamkar ya yi yakin neman zabe ne.

    Mr Jonathan ya tsaya takara a zaben 2015 amma ya ha kashi a hannun Muhammadu Buhari.

    Ana yi masa kallo a matsayin dattijo bayan da ya amince da shan kaye a zaben.

  8. Maudu'in #NigeriaDecides2019 yana tashe a Twitter

    Zaben Najeriya shi ne ya kankane muhawara a shafukan sada zumunta minda a shain Twitter ake muhawara kan maudi'i daban-daban cikin su har da Trendsmap: #NigeriaDecides2019, #VoteNotFight da kuma #ElectionNotWar kamar yadda muka gani a Trendsmap.

  9. Mutane na kan layin zabe a Makurdi

  10. Ra'ayin 'yan kasar waje kan zaben Najeriya

  11. Mata da dama sun fito yin zabe

    Mata sun sa himma wajen yin ruwa da tsaki a zabar wanda zai shugabanci kasar nan

  12. Masu sa idon zabe a Utako Abuja

  13. Wata tsohuwa na jiran kada kuri'a

    Wata tsohuwa na jiran ta kada kuri'a a mazabar Gayam da ke Lafiya, Nasarawa.

  14. Wata matashiya na cinikayya a wajen zabe

    Wata matashiya ce da ta je wajen zabe ba ta da katin da za ta gudanar da zabe sai ta shiga sayer da katin kira na waya a Abuja.

  15. Ana kada kuri'a a wasu mazabu a jihar Bauchi

    Yadda mutane suka yi layin kada kuri'a a makarantar Firamari a Jahun a jihar Bauchi.

  16. Peter Obi ya kada kuri'a

  17. Shirin zabe a Makurdi

  18. Goodluck Jonathan ya kada kuri'a

    Tsohon shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan ya kada kuri'a tare da mai dakinsa.

  19. Yusuf Buhari ya kada kuri' a a Abuja

  20. Matasa na yin karta a kafin yin zabe

    Wasu matasa ne da aka tantance suke yin karta kafin su kada kuri'a a jihar Lehas.